← Book details Fahimah Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 35

Sashe 6

Fahimah Complete Hausa Novel · about 8 min read

Farar doguwar shimi ce a jikinta mai santsi (armless) kanta ko kallabi babu, ta matse gashin kanta mai tsayi da santsi a tsakiyar kanta.

Kai ka ce jarumar nan ta fina-finan Hindi ce wato Sushmita Sen.

Ga tsayi ga zati.

Wuta ta daukewa Uwais na dan lokaci, ya nemi zuqar numfashi ya kasa, bai taba ganin kyakkyawan abu da ya keta zuciyar sa irin wannan halitta da ke tsaye gabansa ba.

Sannan a lokaci guda idanuwansu suka sarke cikin na juna, chemistry din ya afku a lokaci guda.

Amrah go and cover yourself.

Ta ji muryar yayanta a tsakar kanta, a lokacin ne ta ankara da yanayin sutturar jikinta, da bakon fuskar da ke falon wanda ta zama lost a cikin kallonsa.

Da sauri ta juya ta shige daki, Uwais ya bi ta da ragaitattun idanunsa.

Tunda yake a rayuwarsa bai taba jin yana son mace da dukkan zuciyarsa da ruhi irin yau ba.

Yes, ya yi dating iri-iri a makaranta amma bai taba jin abin har zuciyarsa ba.

Yawanci ma matan ke fara kawo kansu.

Yau kuwa ji ya ke ba shi da sauran buri a rayuwa irin na mallakar kyakkyawan abin da ya gani yanzun nan.

Jabir na ta yi masa hira, sai ya lura Uwais absent - mindedly yake sauraronsa.

Ya dan doki kafadarsa,
Kai tunanin me ka ke haka ina ta magana ba ka jina?

Suka ci gaba da cin abincin su, amma Uwais bai kara nutsuwa ba.

Sannan dandanon abincin bai kara hawa kansa ba duk da kwarewar da Murjanatu ta nuna wajen sarrafa shi.

Sai da Jabir ya rako shi zai tafi ne ya tambaye shi game da yarinyar da ya gani dazu, Jabir ya ce,
Wai Amrah?

Kanwata ce uwa daya uba daya, ta zo mana hutu ne, a Malaysia ta ke karatu.

Duk miskilancin Uwais yau ya kasa sarrafa kansa.

Ya ce, To Jabir, ko in shigo daga ciki ne?

Dariya Jabir ya yi sosai ya ce, Ta yi kankanta da aure a gidan mu.

Yanzu ne ta ke shekarar farko a karatunta na medicine, Daddy ya fi so ta kammala MBBS ma kafin ya yi mata aure.

Uwais ya marairaice wa Jabir, Ni dai don Allah ka shige min gaba, ka gabatar da ni ga Daddy, sai da izininsa zan fara nemanta.

Wallahi na yi alkawarin barinta ta yi karatu har sai ta ce ya ishe ta.

Ka ji tausayi na Jabir na kai 30 fa, kullum da jikakkiyar kanwa ta a kofi a gefen gado nake kwana.

Dariya sosai Jabir ke yi, dama gwanin dariya ne, ya ce, Ina su Salma?

Firdaus?

Jennifer and co?

Ka fi karfin autar mu Uwais, you never take any dating serious, ina tsoron in shigar maka ka gano wata ka bar min kanwa emotionally touched.

Uwais ya shafi lallausar sumar kansa, ya ce, Joke apart Jabir, ni fa na ga mata a gidanka.

So ko ka ki supporting dina zan kai kaina ga Daddy, amanar kanwarka idan na ci ta Allah ya ci tawa.

Ko daga cikin amon muryarsa Jabir ya san he is now talking serious, amma gani yake Uwais ya fi karfin Amrah domin shekarunsa sun kusa ninka nata.

Ga shi da matukar wayewa tun suna jamia da farin jinin mata fiye da dukkan abokansu.

Sai dai ta fannin tarbiyya ya yarda Uwais ya same ta cikakkiya.

Maman shi is over-protective.

Don haka ya yi masa alkawarin zai kai shi wajen mahaifinsu in ya zo gari kasancewar a Abuja iyayensu ke zaune.

Yana da wata matar a nan Kano bayan mahaifiyarsu duk karshen wata yake zuwa Kano ya yi kwana uku kacal.

Ko shi zai so Amrah ta samu gwarzon miji irin Uwais Shagari.

Tun daga ranar Uwais ya maida gidan Jabir wajen cin abincin darensa, don kawai ya ga Amrah.

Ya yi alkawarin ba zai tunkare ta ba sai da yardar mahaifinta kamar yadda shariah ta umarta.

Ya kuma roki Jabir ko Murja kada ya bari ta ji don Amrah yake zuwa, shi kuma Jabir da gayya yake kiranta ya sa ta aiki in Uwais ya zo don ya samu ya ganta hankalinsa ya kwanta.

Girkin ma cewa yake Murjanatu ta sakar mata don Uwais ya ce ba abin da yake so irin ya ci abin da ta sarrafa da hannunta.

A fannin ita Amrah ba ta san manufarsu ba, don haka da zuciyarta daya ta ke yin komai da Jabir ya sa ta yi musu.

Murja dai duk da Jabir bai gaya mata don Amrah abokin nasa yake zuwa ba ta fara ramfo su, ko tsakiyar idanun Uwais ka kalla sai ka ga kwantacciyar soyayyah.

Cikin kallon da yake yi wa Amrah.

A ranta dari bisa dari tana supporting abun don har zuciyarta ta san in Amrah ta yi nasarar samun Uwais a matsayin miji ta yi matukar dacen miji daya da daya a cikin maza.

Yawan fitar da ya tsira kullum bayan ya dawo ofis wanda a baya ba ya yi kuma ba halin sa bane ya soma damun Ammi.

Ta tsare shi da tambayar ina yake zuwa ko abincin dare ba ya ci a gida?

Ya ce mata babu inda yake zuwa sai gidan Jabir dole ta kyale shi.

Ranar jumaa Alhaji Umar Dikko ya sauka garin Kano daga birnin tarayya.

Gidansa na Kano yana unguwar Bompai.

Tsohon dan boko ne da aka dade ana damawa da shi a gwamnatin tarayyah, a halin yanzu shine shugaban hukumar Haraji ta kasa.

Yayansa takwas biyar ciki daya, uku ciki daya, Jabir ne babba, sai Hassan da Hussaini, Wasila sannan autarsu Amrah.

Amaryarsa da ke Kano tana da yaya uku kanana.

Sun yi shi da Jabir cewa in daddy ya sauka jumaa, washegari asabar za su je su same shi da kokon barar su.

Duk da Jabir ya san mawuyaci ne Baban nasu ya amince ya aurar da Amrah a wannan lokacin.

Sai dai an ce a rashin tayi akan bar arha kuma a rashin kira karen bebe ya bata.

Tun karfe bakwai yake shiri, kayan da ya tanada musamman don ranar babban riga da yar ciki da wando na wani rantsattsen yadin filtex milk colour ya sanya ya feshe su da 'Maison Francis' dinsa.

Agogon rolex mai fata ruwan kasa-kasa ya daura a damtsen hannunsa, haka hular kansa da budadden takalminsa ALDO duk ruwan kasa-kasa ne. kowa ya kalle shi sai ya kara, ya hadu iyakar haduwar da kowacce rantsatstsiyar mace ke buri a mijin aurenta.

Uwais Abdulkarim Shagari kenan.

A falo ya tadda Ammi da Fahimah suna shan shayin da ba ya rabo da gaban Ammi.

Fahima sanye cikin wani lallausan cotton lace ruwan makuba mai ratsin orange, ta kalmasa daurin kai mai tsari a kanta kamar mai shirin zuwa dinner.

Nan kuwa daga ita sai Allah Ubangijinta suka san don wa ta yi kwalliyar nan, a daidai lokacin da ta tabbatar zai fito ya tafi yawon magribarsa da ya tsira kwanan nan.

Bayan ya yi mugun daukar wanka.

Ita a kan karan-kanta ba maabociyar kwalliya ba ce, kuma ba ta yinta sam a fuskarta, amma tana zama ta bata lokaci wajen kalmasa daurin kai mai tsari wanda zai fiddo cute fuskarta, da lace ko atamfa (her fovourite attire).

Ta shafa wet-lips mai kamshi da tausasa lebe.

Burin zuciyarta in zai shige ta ganshi, ko da ba zai kalle ta ba, ita za ta saci kallonsa zuciyarta ta rage zugi da radadin da ta ke mata a kansa.

Sai ina kuma?

Wannan babbar riga haka?

Ammi ta fada trying hard ta tuna lokaci na karshe da ta ganshi cikin babbar riga.

Baki sake ta ke kallonsa don alamuransa a dan tsukin nan ta kasa gane musu.

Kamar wanda yayi gamo sai aukin wanka kamar kwado.

Wani sassanyan murmushi ya yi, a miskile ya ce,
Ammi, neman aure za ni, ki yi min addua. sai na dawo.

Bai jira cewarta ba ya sa kai ya fice.

Ammi ta bi shi da sakakken baki kafin ta ce da Fahima, wadda ta daskare a wurin,
Anya Uwais lafiyarsa?

Aure?

A ina?

Ba don bai kai munzalin ya yi auren ba ne ya sa Ammi ta yi wa kanta wannan tambayar ba, sai don kallon da ta ke masa na miskilancinsa ba zai taba bari ya taba cewa yana son mace ba.

Sai fargawa ta yi babu Fahimah a wajen, ta shige dakinta ta bame kofa.

Tana rufe kofar ta jingina jikinta ta lumshe idanunta tana amsar sababbin feelings din da maganar Uwais ta haifar.

Masu kama da fitar bullet zuwa tsakiyar kirjinta.

AMMI NEMAN AURE ZA NI!

She dont actually know the meaning of the feelings, amma ta san it deeply hurts, some hidden parts da ke karkashin zuciyarta.

Neman aure za ni, Ammi ki yi min addua.

Maganar Uwais ta yi amsa-kuwwa a cikin kanta a karo na biyu, ta kuma rasa dalilin da ya sa ta haifar mata da wannan bitterness din a kasan ranta.

Me hakan ke nufi?

Zuciyarta na nufin Uwais ba zai yi aure ba?

Ko kuwa bai kai munzalin yin aure ba?

Amma da ta yi tsam da ranta da hankalinta waje guda a yau, sai ta fahimci cewa Uwais zuciyarta da gangar jikinta ke son aure, wanda hakan na nufin zuciyarta LOVES UWAIS DEARLY..... shine dalilin da yasa taji wannan bitterness din a karkashin ranta don ya ce ya tafi neman aure.

Da ta ki da ta so gaskiyar magana kenan, shi ne kuma fassarar duka unexpressable feelings din da ke dankare cike da zuciyarta shekara da shekaru akan Yaya Uwais, shi ne kuma silar jin abin da ta ke ji yanzu da ya ce ya tafi neman aure, something unbelievably like KISHI.

A hankali Fahima ta sauke ajiyar zuciya tana jin tamkar zuciyarta na gutsittsirewa into pieces tana narkewa kamar dalma, kawai saboda Uwais ya ce ya tafi neman aure!

To ina ga ranar da aka daura auren sa da wata akan idon ta!?

Da kyar ta ja kafa zuwa gadonta ta kwanta rigingine, abubuwa da yawa na gilmawa a idanunta.... zuciyarta na hasko mata ranar da za ta ga matar Uwais a gabanta, ko how does she look?
Chapter 6 · 0% Book details