← Book details Fahimah Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 35

Sashe 31

Fahimah Complete Hausa Novel · about 8 min read

Maganganun da Uwais ke wa Fahimah a waya na sanya ta a wani hali na tsananin kewarsa, ta ji ba abin da ta ke so irin ta bude ido ta ganshi tare da ita.

Amrah ta shiga edd dinta ana saura sati biyu Uwais ya dawo daga Switzerland, kuma an yi sa
lokacin suna gab da zana jarrabawa, don haka iyayenta cike da bacin rai suka ce ta taho Abuja, wata shekarar sai ta zana din.

Ko kadan ba sa murna da wannan haihuwa ta Amrah ba ta cimma komai a rayuwa ba (a cewar Aunty Wasila).
e dabbar ina ce ki ka yarda ki ka dau ciki a wannan lokacin kamar wadda ba ta je makaranta ba?

Ba ki san dan contraception na zamani ba?

Ai shi ke nan sai ki yi deferring karatun ki zauna kula da jaririn Uwais, ba ki ganki ba duk kin bi kin tsofe daga aure shekara daya
In ji Aunty Wasila ranar da Amrah ta sauka a gidansu da ke Apo.
asbunallahu wa ni
mal wakil
?.

In ji Jabeer da ke shigowa,
asila, kina tsoron Allah kuwa?

Kina son gamawa da duniya lafiya?

Sunnar Annabin ki ke wa wadannan munanan maganganun haka?

Ni dai wallahi Daddy ya cuce ku, kwata-kwata hanyar da ya nuna muku ta saba wa addini, da ba a yi auren ba a haife ku?

Ko da an haifeku ba aure zaku so hakan?

Zina ta yi ta samu cikin ko kuwa da kike mata wannan titsiyen?

To ahir dinki a kan dan Uwais, don wallahi a kan wannan cikin daga ke har Amran zai iya daure
ku har sai igiya ta yi rara!".

Wasila ta zumbura baki daidai lokacin da Mamansu ta shigo.

Ta ce,
mrah me ki ke so a dafa miki?

Amrah wadda idonta ya cika da hawaye ta ce,
ama ki yi min tsakani da Aunty Wasila, cewa nake ita
a uku gare ta?

Ina ruwanta da cikina da za ta ce min dabba a kansa?

Aure fa nake yi ba zina ba, ban ga dalilin da za a ce za'a bani query don an ganni da ciki ba
Mama ta kyabe baki, ta ce,
asu aure manya, ke ki ka ga za ki iya, da ma Daddy ya ce yaron nan ya gama da ke, in ba a yi wasa ba karatun likita sai dai a ga kannenki da shi ban da ke
Amrah ta fashe da kuka, ta ce, ta fasa haihuwa a gidan kada ta haihu su bi dare su kashe mata da, ta fuskanci duk ba sa son Uwais ita kuma tana son kayanta.

Mama ta ce,
i fi ruwa tafiya, muna nan za ki dawo mana in dai namiji ne.

Namijin ma irin wannan kallelen mai idanu a tsakar ka, daga ganinshi womaniser ne
?...

Amrah hannu ta sa ta toshe kunnuwanta, ta rasa me Uwais ya yi musu haka, daga Yaya Jabeer sai Aunty Murjanatu ke kaunar aurenta, amma a ce har uwar da ta haife ka?!

Womaniser!

Kalmar tayi tsauri da yawa a alaqantata da mutum mai daraja da mutumci irin Uwaiss.

Wannan bakin cikin ya sa washegari ta tattara kayanta sai Kano.

Ga shi tana cikin EDD bai kamata ta yi doguwar tafiya ba, amma da ta haihu a gidansu ta gwammace ta haihu a hanya, babu mai taba mata Uwais ta kyale.

Ko da Daddy ya dawo Mama ta gaya masa Amrah ta yi fushi ta tafi, ta fasa haihuwa a gabansu don kawai Wasila ta gaya mata gaskiya, ta kwashe duk yadda aka yi ta gaya masa.

Daddy a take ya dau waya ya kira Amrah, lokacin suna gab da shiga Kano ita da direban gidan su.

Ya ce,
mrah?

Ta ce,
m Daddy
Ya ce,
ada ki sake in kara ganin kafarki a gidana, in kin haihu kuma babu wanda zai zo ki je ga ki dangin miji su yi miki komai da uwarki zata yi miki, ga da namiji nan don soyayya ku wuce India
Amrah ta bude baki za ta yi bayani, Daddy ya ce,
ana son jin komai, tunda duk abin da muke hango miki ba kya hangowa, we
e talking of your future which is ruined now
Kuka Amrah ta fara tana ba shi hakuri da kyar ya hakura, amma ya ce ba za ta haihu masa a gida ba.

Amrah ta ce,
a ji na yarda, amma don Allah ka yi hakuri
Ya kashe wayar ya rabu da ita.

Jiki a sanyaye ta isa Kano, sai ta rasa ina za ta dosa, ba ta iya zama gidan ba Uwais, don haka ta ce da direba ya wuce da ita
ankaba.

Ammi da Fahimah na zaune suna karatu a falo, assignment na Fahimah suke solving.

Ammi na nuna mata.

Sai sallamar Amrah suka ji ta shigo tinkis-tinkis da tirtsetsen cikinta.

Gaba daya suka hada baki wajen cewa,
araba da mutanen Malaysia
Talatu ta shigo da jakar kayanta, wadda Maigadi ya shigo da ita.

Fahimah ta karba sai ta wuce da ita nata dakin.

Ammi babu sakewa sosai tsakaninta da Amrah don haka gaisawa kawai suka yi, da tambayar bayan rabo.

Fahimah kuwa tuni ta tafi kitchen don hado mata abinci da abin sha.

Har dare Amrah na zuba idon ganin ta inda Uwais zai bullo su wuce gida, amma shiru ka ke ji har karfe goma.

Fahimah sai hidima ta ke da ita, dauko wannan miko wannan, da ta ga ta fara hamma daga zaune ta ce,
unty Amrah ko za ki shiga daga ciki ki kwanta?

Ganin idon Ammi ya sa Amrah ba ta furta damuwarta ta rashin ganin Uwais ba, ta bi shawarar Fahimah, domin sosai take son kwanciyar, suka yi sai da safe da Ammi, sannan ta bi bayan Fahimah zuwa dakinta.

Fahimah tuni ta gyara mata gadonta, ta ce ta kwanta a gadon don ta fi jin dadi ita a kan lallausar bargo da ta shimfida a kasa za ta kwana.

A lokacin ne Amrah ta tambaye ta ko Uwais sai karfe nawa yake shigowa?

Fahimah ta juyo tana kallonta da mamaki, ta kasa cewa komai.

Ita ce za ta gaya mata mijinta bai kasar?

Abu wajen watanni biyu?

To ba sa waya ne?

A karshe ta ce,
a ji Ammi ta ce, yana Switzerland
Amrah ta zaro ido cikin kidima, Fahimah ba ta bi ta kanta ba ta ci gaba da shirin kwanciyarta.

Wajen sha biyun dare Amrah tana barci wayar Uwais ta shigo wayar Fahima, kuma wayar tana kan bedside daidai inda kan Amrah ke kwance.

Hasken wayar ne ya dame ta ta dauka don ta mika wa Fahimah don da alama ta yi barci, amma hoton da ya fito kan fuskar wayar ya sa ta mamaki hadi da bayyanar lambobin da daga gani ka san na kasar Switzerland ne.

Abu biyu ya sa Amrah jin gara kawai ta amsa wayar nan.

Don hankalinta ya kasa tsayawa waje guda.

Dalilin Fahimah na dora hoton Uwais a kan lambarsa, da irin tune din da kiran ke bayarwa, sannan uwa-uba wane Yaya ne zai kira
ar uwarsa late at night haka?

Lokaci ne na masoya da ma'aurata bana
an uwa ba.

Kawai sai ta amsa wayar ba tare da ta ce komai ba.

She just want to confirm it's Uwais ko ta samu nutsuwa.

Muryar Uwais tar-tar cikin yanayin da ke nuna akwai marital intimacy (sexual bond) ya ce,
ahhima na kasa barci, wallahi hakuri na ya kare.

Jiya saura kadan in maimaita irin laifina na Sudan, na ji tsoron Allah na ji tsoron fushin ki, musamman da na tuna tsiwar da ki ka yi min a ranar da tsanar dana gani cikin kwayar idon ki, na ce gara in rufawa kaina asiri in kashe ko nawa ne in miki ticket da visa ki zo min ko na kwana uku ne don Allah Fah-himah kada ki ce min a'ah, I
missing everything, the luscious and succulent lips, your sweet...
? kalmar karshe da ya fadi ya sa Amrah gigicewa don ko ni ban iya rubutata, wani karfin gwiwa ya zo mata.

A nitse ta ce,
a FAHHIMAH ba ce, AMRAH ce
?.

Sannan ta kashe wayar silently.

Ta koma ta jingina bayanta a jikin gadon.

Abin da ta kasa tantancewa shi ne, da ma tuntuni zaman miji da mata suke yi, ko kuwa farkarsa ce tuntuni suke blackmailing dinta?

Ko kuwa Uwais extra-marital affair yake having da
ar rikon gidansu???

Ko da ta ce Fahimah ta auri Uwais, wallahi duk cikin lalurar yaron ciki ne, saboda a lokacin burinta kawai Uwais ya daina kusantarta, don ta daina jin qamshin (Maison Francis).

Amma daga baya bayan ta samu ingantacciyar lafiya komawa ta yi tana cewa,
llah ya sa ban fada da bakin mala
ku ba
i Amrah....Amrah Umar Dikko, ni Uwais ya yi wa haka???

Hawaye suka soma sintiri a kan fuskarta kafin wani azababben ciwon mara ya zo ya turnike ta.

Salati ta shiga yi tana juyi don ba ta san nakuda ba, amma wannan ciwon da ta ke ji yau ta tabbata nakuda ce, amma da ta haihu a hannun farkar mijinta gara ta koma Abuja ko da da rarrafe ne.........
9/23/21, 8:19 PM - Buhainat: Washegari Amrah ta wuce Malaysia, da ma sati biyu za ta yi.

Satin biyu ma cikin lokacin karatunta ne, ta yanke komai ne don ta samu ta gyara tsakaninta da Uwais, kuma ta samu ta gyara dan kadan ko ba duka ba duk da bai samu wata kulawa a tare da ita ba saboda lalura iri-iri na cikinta.

A daren ranar bayan tashin Amrah daga airport gidan Ammi ya taho.

Ammi da Fahimah suna zaune a falo suna kallon shirin Arewa24 Uwais ya yi sallama, hannayensa duka biyun zube cikin aljihu.

Idanunsa straight a saitin Fahimah wadda daga amsa sallamarshi ta mike.

Ta ba su wuri shi da Amminsa.

Ba ta yarda ta kalli Uwais cikin ido ba sabida Ammi, kuma dai ba ta hango komai a tare da shi sai tsagwaron rigima yau, tunda ya koma gwauronsa kamar da.

Ammi ta amsa mishi, ya zauna suna kara gaisawa, ta ce,
an Malaysia an tashi kenan?
Chapter 31 · 0% Book details