← Book details Fahimah Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 35

Sashe 13

Fahimah Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya fi karfin mintuna ashirin a wurin yana tunanin abinda zai yiwa Amrah ya rama bacin ran data sanyashi, kin amsa kiranta is not enough.

Amma ga mamakin sa ya kasa daukar wani matakin bayan wannan.

Amrah ta riga ta yiwa zuciyar sa illah bai da wani katabus a kanta.

Da kyar ya jawo motar ya dawo gida, bai tadda kowa a falon ba duk sun shige daka, ya wuce dakin sa kansa tsaye.

Wani irin gyara da dakin ya samu da sanyin air fresh da Fahimah ta fesa su suka yi masa sallama, wadanda suka cakude da rabar iyakwandishan.

Sai lokacin ya tuna ya ji sanda Ammi ke fadin Fahimah ta zo ta gyara masa daki.

Tsaki yayi yana fadin "da abinda tafi dacewa kenan ai (aikatau) ba matar masu gida ba".
9/23/21, 8:15 PM - Buhainat: Washegari da safe Fahimah ta shirya masa breakfast, sabida Talatu ta yi sammako zuwa kauyen su Jahun 'yar ta ta haihu.

Kunun gyada tayi masa fari kal mai gardi sai kosan dankalin turawa da ruwan shayin da ya zamewa al'ummar gidan duka farillah.

Ya fito cikin casual - dress din sa na suit din ma'aikatan bankin GT misalin karfe bakwai dai-dai na safe.

One thing shine baya wasa da cikin sa sabida fadin kirjin sa (physique) da motsa jiki da yake yi da Asubah yasa baya iya fita ba tare da ya karya ba.

A jikin dining din ya sameta tana jera abincin, rigar barci ce a jikin ta da 'yar hula a kanta ta dora zanin atampa a saman rigar.

Yana zuwa ya ja kujera ya zauna, ba tareda ya dubeta ba.

Juyawa tayi ta bar wurin jin zata sake yin barin tangaranm ita kuma tayi alkawarin ta daina bada kanta gaban Uwais.

Yayi tsammanin zata gaishe shi ne ya baiwa banza ajiyar ta.

Ga madaukakin mamakin sa sai ta juya zuwa dakin ta ba tareda ta ko kalle shi ba.

"Kin rufawa kan ki asiri".

Ya fada yana tsiyaya kunun a kofi.

Ko daga kyan kunun a ido ya tabbatar zai yi gardi a baki.

"Kin taimaki mijin ki na gaba (idan Uwais ya sake ki) da kika tsaya kika iya girki.

Don zaman Ammi kike yi ba nawa ba.

Banda abun Ammi wannan Blakin ai sai ta dinga firgita mutum cikin dare.

Gara da ta rike abar ta a gefen ta bata yi gigin kawo masa ita gida ba.

La-shakkah da Amrah ta samu Kuku.

Don bazai taba bude baki ya iya cewa Amrah yana da wata macen a duniya bayan ita ba.

Bai yaudari Amrah ba, don da gaske har cikin zuciyar sa bai da wata mace bayan ita.

Sama-sama ya ci abincin ya wuce dakin Ammi, tana zaune bisa darduma tana azkar din ta na safiya.

"Na fito Ammi, sai na dawo.

Sabahul khair".

Daga masa kai ta yi ya juya ya fita.
****
Yau Fahimah zata fara registration, don haka tare suka tafi da Ammi, kuma fannin da Ammi ke koyarwa shi ta zabar mata, don tace a fannin ne kawai zata iya dinga taimaka mata a gida wato tsimi da tanadi (economics).

Kasancewar yanzu abu ake na sanayya, Fahimah bata sha wahalar samun gurbi fannin na tsimi da tanadi ba kamar sauran dalibai, duk da wahalar da yakeyi, tunda tana da uwa a gindin murhu.

Da taimakon Ammi ta fara registration, kullum da safe tare suke tafiya, yau da suka fito akan titin su na komawa gida Ammi ta ce "Fahimah, is high time ki fara koyon tukin mota don ki dinga taimaka min kina taimakon kanki, tunda Surajo ya tsufa baya iya gani sosai, yanzu kuma ke matar aure ce, bai kamata ga mijin ki zaune a gida in dauko wani kato ya dinga kai ki makaranta ba, nikuma ba kullum nake shiga Campus ba, tafiyar mu zata saba in kika fara daukar lacca".

Fahimah ta ce "Ammi to waye zai koya mini?" "Ni dai kin san bani da lokaci, tunda an shiga sabon semester, amma zan wa Uwais magana ya dinga koya miki a karshen mako".

Ammi ta kirkiro zancen koyon mota ne don ta samar da kusanci ko yaya tsakanin Uwais da Fahimah don ta ga abin nasu ba mai alamar karewa bane.

Kada kuma auren ya lalace a haka.

Lokacin da Ammi ta furta masa wannan umarnin, fuskar Uwais komawa ta yi kamar hadarin da ya nausa yayi gabas.

"In koya mata mota fa kika ce Ammi?" "Eh, abinda nace kenan" bai san sanda ya ce "Ammi muharramata ce?" Don shi shaf!

Ya mance da wata Fahimah balle auren ta dake kansa.

Ammi dunkule yatsunta tayi ta mika masa "ungo nan (dakuwa).

A'ah ba muharramar ka bace, kanwar tsohon ka dake kabari ce".

"Yau sabida Fahimah har Baban shi an zaga".

Tashi yayi fuuuu!

Ya wuce dakin sa.

Abincin ma ya fasa ci.

Ammi tana kai shi bango da yawa akan Fahimah yana hakuri ne kawai don UWA ta fi gaban wasa ammma da tuni Fahimah ta dade da komawa orphanage.

Washegari Ammi ta samu waya daga babban dan Kawu Shuraim wato Mahdi, cikin kuka mai tsanani Mahdi yace.

"Allah ya yi wa Abbu rasuwa yau din nan".

"Innalilllahi wainna ilaihi rajioun".

Ammi Safeeyah ta fada tana karawa.

Ashe shiyasa ya dage ya zo ya yi wa Uwais aure?

Ashe sallama ce ya yi musu, ashe rabuwar kenan, ashe daga wannan lokacin Uwais yayi rashin Kawun sa mai son sa da kaunar sa...

Allahu akbar!

Muryar Ammi kadai ya ji ya tabbatar kuka take yi.

Uwais a zaune yake akan kujerar sa amma bai san sanda ya mike tsaye ba makale da wayar a kunnuwan sa, kansa ya kama ya dafe da hannayensa biyu a lokacin da Ammi ta fada masa rasuwar Kawu Shuraim.

Babu irin kokarin da bai yi ba don ya samu excuse daga Banki ya bi Ammi Sudan amma bai samu ba, domin already yana daga cikin manyan ma'aikatan GT da zasu halarci seminar ta organization din nasu gabadaya, wadda suke yi duk karshen shekara a babban reshen su da ke jihar Lagos, zasu tafi cikin satinnan kuma an riga an mika sunan sa.

Ammi ta so tafiya da Fahimah, amma ga nata karatun da bai gama nuna ba, kuma tana so ta jima a Khartoum wannan karon kasancewar ta dade bata je ba.

Don haka dole ta bar ta a gida.

Da daddare bayan Uwais ya dawo take tambayar sa "yaya ka samu excuse din ne zamu tafi tare ko yaya?" Ya kalli Ammi da tausayin ganin yadda mutuwar dan uwan ta ta buge ta, ta fyadar da ita a wuni guda, Ammi har ramewa ta yi.

Idanun ta sun yi jazur sabida kuka.

Ya ce a hankali "ban samu ba Ammi, don an tura ni cikin masu tafi seminar a Lagos nan da kwana uku, zan yi kwanaki ukku, sai dai idan na dawo, zan yi matukar kokari na samu adduar bakwai".

Ammi ta ce yaushene tafiya Lagos din?

Yace jibi Juma'ah, zamu dawo Lahadi don mu samu ofis litinin, sai in yi kokari a bar ni in zo Sudan ko na kwana biyune kacal".

Ammi ta ce "to Yaya za'a yi da Fahimah?

Don ni zan yi akalla sati biyu kuma tana zuwa makaranta, ga Talatu bata dawo ba har yau, don haka tunda Juma'ah, Asabar da Lahadi ne ka tafi tare da ita Lagos din, bazan barta ita kadai a gidannan ba.

In kuka dawo ka samu izni daga ofis din sai ku taho Sudan tare ku samu addu'ar bakwai ku dawo tare, tunda dukkan ku kuna da passport na kasar Sudan".

Wani gumi ne ya shiga barkowa Uwais daga kowacce kafa mai tsatstsafar da gumi ta jikin sa.

Bai san san da ya kira sunan Ammi da hanzari ba.

"AMMI!"
Tune din muryar kamar na wanda zai fashe da kuka.

"Muharrama ta ce da zan tafi da ita wani gari har kwanaki?" Ammi bata san sanda ta kai masa bugu da filon hannun ta ba, ta ce "idan ka sake yi min wannan tambayar ta rainin hankali wai ko Fahimah muharramarka ce sai na sassaba maka kamanni.

A'a ba muharramarka bace, karuwa ce nace ka dauka ka tafi da ita.

Kuma ka kula da marainiyar Allah Uwais, cin ta, shan ta da walwalarta.

In ka ci amanata kai da Allah".

Uwais ya mike yana rangaji ya bar falon, bakin ciki kamar ya hadiye zuciyar sa.

Wai me ke damun Ammi ne?

Idan da yana tunanin Dimentia ne yanzu kam ya tabbatar lafiya kalau take, tana matukar son hada rayuwar sa da yarinyar nan, yarinyar data riga tasan ita kadai take son abarta.

Ya dauketa ya shiga da ita cikin abokan aikin sa ma ya ce matar sa ce ai ya sayowa kansa raini a wurin ta da wurin su.

Wannan matar leburori ce da marassa gata ba irin tashi bace.

Shi fa ba abunda bai so ma a duniya irin ganin black fuskarta, balle yasa ta a gefensa yana yawo da ita cikin Nigeria wai har ma da wajen ta (Sudan).

Idan Amrah ta samu labari fa cewa he is with another woman me zata dauke shi?

Hakan bai zama yaudara da cin amanar soyayyah ba?

Zuciyar sa ta tambaya.

Sannan ba tare da bata lokaci ba daya zuciyar ta halarto da amsa...

Bai zama cin amana ba, tunda itama ka biya sadakin ta, matsalar tun farko bai kamata ka boyewa Amrah ba.

In har tana son ka zata baka goyon ne baya kayi biyayya ga mahaifiyar ka.

Yadda zuciyar sa zata iya jure hada muhalli da Fahimah a bakon wuri inda basu san kowa ba har na tsayin wasu kwanaki shine babbar damuwa a gare shi.
****
Ya cigaba da yiwa Ammi shirin tafiya Sudan a yinin ranar duk da cewa he's frustrated amma bazaka taba ganin hakan akan fuskarsa ba, yana da charisma na boye fushi, ya saya mata tikiti, a lokaci guda yana nashi shirin na tafiya Lagos.

Yayi waya da duka 'ya'yan Kawu Shuraim yayi musu ta'aziyyah musamman Mahdi, ya gaya musu uzurin sa na rashin biyo Ammi.
Chapter 13 · 0% Book details