Sashe 12
Fahimah Complete Hausa Novel · about 8 min read
Don tsananin bacin rai da ya koma gida sai ya samu kansa da janyo trollies yana hada kayan sa, gara masa ya koma gidan Ammi da ya zauna gwauro har tsayin wata hudu.
Ko ba komai zai dinga samun abinci.
Amma yau da wata ce ta yi masa haka ba Amrah ba, zai hakura da auren ta ne kawai.
Amma Amrah zata ci alfarmomi har guda biyu; alfarmar son da yake mata da kuma mutuncin dake tsakanin sa da Jabeer.
Ammi na falo tana karatun 'Bulugul Maram' din ta.
Sanye da shudiyar laffaya, da butar shayin ta da tambulan a gefe, sai ganin maigadi tayi yayai sallama yana shigowa da akwatunan Uwais, yana wucewa da su part din sa.
Ta saki baki tana kallon sa a lokacin da yake shigowa.
Fuskar nan tayi jawur, ta nan take gane fushin Uwais ko bacin ransa tun yana yaro.
Bata ce komai ba har ya zo ya samu wuri ya zauna daga gefen kaf
afun ta.
"Ammi masa'ul khair"
Tana cigaba da kallon sa ta amsa fuskar ta ba yabo ba fallasa, sannan tace "wadannan akwatunan fa?
Ko balaguro zaka yi?" Ya girgiza kai cikin shanye bacin rai, don ya san Ammi ba wai tana farin ciki da auren sa da Amrah bane kawai ba yadda zata yi ne kuma tana so ta bashi hakkin sa, shi yasa ta yarda ya aure ta.
Don haka dole ya rufawa Amrah asiri don dorar da dangantakar su.
Yace.
"Babu komai Ammi.
Amrah ta koma makaranta ne, sai bayan watannni hudu zata samu hutu, shiyasa na dawo gida kawai don kadaici zai dame ni, babbar matsala ta abinci".
Ammi cikin mamaki tace "makaranta a ina?" "Limkokwing, Malaysia" Ammi ta rasa abinda zata ce, daga bisani ta ce "dama ka san tana karatu a wata kasar ka aure ta?
Ko kuwa sabon zance ne?" Uwais ya sunkuyar da kai, sai yanzu yake ganin wautar kansa, sannan yace "eh Ammi" sai kawai ta gyada kai ta ce "Allah ya bada nasara".
Har wata ajiyar zuciya Uwais ya saki don bai zaci Ammi zata gajarta zancen a haka ba.
Shi kuma baya son zancen yayi tsaho har ya kai ga fada mata cewa Amrah ta tafi ne ba tare da iznin sa ba.
Haj.
Safeeyah tace "bari in sa Fahimah ta gyara maka dakin, don tun bayan tafiyar ka babu wanda yayi amfani da sassan, na san yayi kura sosai, Talatu bata nan na aiketa kasuwa".
Ba tareda ta saurari me zai ce ba tasa murya tana kiran FAHIMAH.
Uwais sai ya sunkuyar da kai, sannan ya ji gaban sa ya fadi, da ya tuna wai itama zaman matar sa take.
Zaman shi ta ke yi.
Don shi sam ya manta da ita da existence din ta.
Fahimah ta fito daga kicin dauke da madaidaicin tray data shiryowa kanta abinci zata ci, ta shigo falon tana amsa kiran Ammi ba tareda ta san Uwais yana nan ba.
Dai-dai lokacin da Uwais ya dago kai.
Sexy eyes din sa suka sauka akan Fahimah.
Ita kuma bata tsammaci ganin sa a falon ba, don haka farantin dake hannnun ta da duk abinda ke kai ta saki a kasa ba tareda ta sani ba.
Idanun Uwais na da matukar tasiri ga mental well-being din ta, ta yadda a duk lokacin da ya dubeta da su take neman hankalin ta da nutsuwarta ta rasa.
Komai dake kan farantin ya kife, tangaran sun fashe sannan jikin ta ya hau bari.
Ammi takaici ya ishe ta na yadda Fahimah bata iya mallakar kanta a duk lokacin da ta ga Uwais kamar wadda ta ga mala'ikan daukar rai, tace.
"Yau nake ganin sakarci, sai ki dauko tsintsiya da mopper ki share, ke ba makauniya ba balle ace tuntube kika yi, kiyi maza ki kwashe kije ki gyara masa sassansa".
Ta juya a sanyaye ta koma kicin don ta dauko tsintsiyar.
Uwais mikewa yayi yana sakin dan karamin tsakin da Ammi bata ji ba.
"Zan je wajen Jabeer na dawo Ammi, kafin a gyara dakin".
Ammi tace "Rehlah Sa'eedah" wato a dawo lafiya.
Bayan fitar sa Ammi ta bishi da kallo sannan ta yi murmushi ta maida duban ta ga Fahimah wadda ke durkushe tana tsaftace wurin data yi messing, ta kasa dagowa har Uwais ya zo ya wuce ta gaban ta.
Ammi a ranta tace "muje zuwa dai, ai sannu - sannu bata hana zuwa ai, sai dai a dade ba'a je ba".
*****
FAHIMAH A DAKIN UWAIS
Wannan ne karo na farko data taba shigowa dakin Uwais a rayuwar ta, da farko kasa tabuka komai tayi, domin ji tayi gabadaya kuzarin jikin ta ya kare, koda yayi watanni baya dakin kamshin tsadadden turaren sa 'Maison Francis' bai bar sanyaya dakin ba.
Babban hoton sa window size cikin kayan aikin sa na GT shi yafi daukar hankalin ta domin yayi kyau ba na wasa ba a cikin hoton.
A jikin bed-side wani dan karamin hoton ne cikin frame da ya sha adon zuciya, fuskar sa ce data Amrah a ciki kamar zasu sumbaci juna.
A hankali ta kai hannu ta dauki hoton a tafin hannun ta tana share kurar jikin sa da gefen gyalenta, tana kallon su da wani irin mixed feelings da ya fi kama da "kishi mai nukurkusa zuciya".
Kishin da bata taba ji akan Amrah ba sai yau, ganin yadda ta maida Uwais jazur, ga 'yar kiba yayi, tabbacin yana samun gamsashshiyar soyayyar mace.
Mai mace kamar Amrah yaushe zai taba waiwayar ta?
Amma me?
Mayaudariyar zuciyar ta sai ta ci gaba da bata hope da courage na cewa wata rana irin haka na zuwa....ranar da zata ga fuskarta haka gab da ta Uwais, watakila closeness din har ya fi haka.
Duk da haka bata jin kin Amrah a ranta domin ta yaba da yadda ta karbeta a ganin ta na farko da ita.
Ba abunda ke bukatar gyara a dakin sai kura da ko'ina yayi, don haka ta hau karkade komai tana gogewa tayi shara ta gyara abinda duk ya kamata ta tsaftace, sannan ta wanke masa toilet wanda yake fari kal shi ko kurar ma bai yi ba fari kal yake tabbacin a baya yana samun kulawa sosai.
Da ta kammala ta feshe dakin da 'air freshner' din 'raspberry' ta shimfida masa sabon bedsheet mai kauri da Ammi ta bata ta shigo da shi sannan ta juya zata fita.
Kamar wadda aka yiwa umarni sai ta sake juyowa, ta kalli hoton sa dake kafe, sannan ta runtse idon ta ta juya ta fita.
"Na gama Ammi!"
Ta fadawa Haj.
Safeeyah dake zaune tana lazumi, mace ce mai yawan ibadah da bata bari lokacinta ya wuce a banza.
Kai ta gyada mata.
Sai Fahimah ta wuce kitchen ta tadda Baba Talatu don ta taya ta shirya abincin Uwais.
Ko dama can tare suke girkin su muddin Fahimah tana gida.
Suna cikin aikin Baba Talatu ta dube ta sosai ta ga kullum kara ramewa take yi.
Ta san dole Fahimah ta kasance cikin damuwa sai dai ta boye hakan a ranta, don bata taba ji ko ganin Aure irin nata ba.
Har yau ta kasa gane manufar Ammi ta hada wannan baudadden aure, ita Fahimahn tana nan a gefe kusa da uwar sa, shi yana can tare da matar da yake so suna more kuruciyar su.
Anya ko Fahimah bata son Uwais hakan bazai ke damun ta a karkashin zuciya ba?
Koda yake Ammi tace jami'a zata fara, ta san Fahimar su da son karatu, watakil in ta fara zuwa makarantar zata samu abin debe kewa.
Baba Talatu ta nisa ta ce.
"Uwar daki na, daga yau ke kadai zaki dinga dafa abincin ubandaki na, sannan ke zaki dinga kai masa, gyaran dakin sa da kula da komai nasa a gidannan ya dawo wuyanki domin da ke yafi dacewa har zuwa lokacin da zai bar gidannan".
Fahimah tayi mata kallon "sannu sarkin kankanba".
Sannnan ta ce "shin Baba Talatu meye gami na da shi din?" Dariya Talatu tayi tace "wai ai naga aikin neman lada ne da neman aljannah, kiyi don neman dacewa da aljannah ba don komai ba" da sauri Fahimah ta girgiza kai "ban iya shishshigi ba, kuma bazan fara yanzu ba.
Ayyukan neman lada yawa gare su.
In ya ga dama ya bi matar sa.
Ni ki daina alaqanta ni da Ya Uwais, don babu komai tsakanin mu bayan 'yan uwantakar musulinci da Ammi ta hada, kuma ita nake fatan ta cigaba da wanzuwa a tsakanin mu har karshen rayuwa ta.
Baba Talatu ta yi murmushi ta ce "Fahimah har yanzu ke yarinya ce, amma yaya zaki nade hannu a kirji ki koma gefe ki barwa kishiya miji?
Miji fa aka ce Fahimah ba saurayi ba!
Ai kowanne li'irabi kike dashi ki ajiye shi a gefe ki yi hobbasar kwatarwa kanki 'YANCI don tabbatar da martabarki ta diya mace.
Ni ban yarda wai wannan farar tsadar ta fi ki komai ba, mace sunan ta mace, kowacce irin kala ce ita, bahaushiya, balarabiya, ba'abziniya, bafullatana ke har bayerabiya duk daya muke.
Balle ma Fahimah ke kike ganin kan ki a baya don baki da hasken fata irin ta ubandaki na, amma bakar mace ai ita ce mace ta alfarma, shi kansa ya san hakan sai don dai wani dalili nasa na daban amma.....".
Zancen duk ya gundiri Fahimah, tace "Baba Talatu chapter closed, inda aka san darajar ka acan ne zaka yi rawa a baka kudi, a inda ba'a san darajarka ba kuwa maimakon ka samu kudi, kana iya karewa da dan banzan duka!".
Uwais da ya je bai samu Jabeer a gida ba sai Murjanatu, ta gaya masa Jabeer yana Abuja, zurfin ciki irin na Uwais yasa bai tattauna komai akan matsalar sa da Amrah da Aunty Murjanatu ba duk da ya san kusancin dake tsakanin su.
Maimakon ya koma gida sai ya samu gefen hanya ya gangara ya tsaya, ya kashe motar gabadaya yana kallon wayar sa da kiran Amrah ke ta shigowa akai-akai ba kakkautawa.
Zuciyar soyayyah na azalzalarsa da ya dauka.....zuciyar maza na hambarewa.
Duk son da yake yi wa Amrah dole ta yi abinda zai nuna mata shi ba irin mazan da mace ke juyawa bane don kawai yana son ta.