← Book details Fahimah Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 35

Sashe 4

Fahimah Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har aka yi kiran assalatu ba ta yi barci ba, tana kai wa Sarki Allah kukanta a kan Uwais.

Amma ko da ta kwanta barci bayan ta sallaci asubahi, mafarkin da ta yi ya firgitata...
9/23/21, 8:15 PM - Buhainat: *****
Washegari da ta gama shirinta tsaf na tafiya makaranta ta cimma Ammi a dakinta tana karatun littafin Bulugul Maram da ta ke yi duk safiya.

Ta tsugunna a gabanta ta gaishe ta sannan ta yi shiru tana wasa da yatsun hannunta.

Ammin ta lura akwai magana a bakinta, ta rufe littafin ta ce,
Ya aka yi autar Ammi?

Kina son wani abu ne?

A hankali Fahimah ta motsa dan bakinta kamar mai tsoron abin da za ta fada.

A karshe ta daure ta ce,
Ammi don Allah kada ki ce Yaya Uwais ya dauko ni a makaranta, don yau ma muna da practical na food and nutrition.

Ammi zan dawo da kaina tunda gobe Surajo (direbanta) zai dawo.

Ammi yar ki ta girma, ki bar ta ta dinga yin komai da kanta.

Ta karasa da murmushi.

Murmushi mai sauti Hajiya Safiyyah ta yi, alkunyar yarinyar na sa wa ta kara shiga ranta.

Ta tabbata Uwais rashin kirkinsa ya yi mata jiya, sannan ya hora ta da ynwa, amma ba za ta fada mata kai tsaye ba sabida kawaici irin nata.

Ta kai hannu ta shafa kan Fahimah affectionately..

I will not send him to pick you again, na lura da yadda ya azabtar da ke da yunwa jiya, amma kansa ya yi wa.

Ungo kudin mota ki hawo adaidaita ki dawo gida.

Ta karbi kudin da hannu biyu ta yiwa Ammi godiya ta wuce.

Ammi, sai na dawo!.

Ammi ta ce, Rehlah Saeedah (wato a dawo lafiya).

Bayan wucewar yarinyar Hajiya Safiyyah ta lumshe ido ta jingina bayanta da bango tana tunani.

Anya mafarkin ta zai zama gaskiya?

Anya Uwais zai cika mata burinta?

Idan kuma ta tursasa shi anya tirsasawar za ta haifar da Da mai ido?

A kafiya da miskilanci gami da izza irin nasa da ta dade da sani?

To in ba shi din ba wa zai auri Fahimah ya rike mata ita da amana?

"Babu!"
Amsar ta kutso da karfi cikin kwanyar ta.

Ko ta samu masoyi ya ji ko wace ce ita guduwa zai yi, in kuma ya karbe ta a haka tofa babu daraja da martaba.

Uwaisun dai da ta haifa shi kadai ne guarantee dinta a kan Fahima, amma baro-baro ya nuna gara kowa da shi in dai a kan ya so Fahimah ne. son ma irin wanda ita ta ke mafarkin ya yi mata, wanda ya kasa karbarta a kanwa ta jini, ta ya ya zai yarda ya karbe ta a matsayin MATARSA?

Shekaru goma sha biyar a baya suka soma gilma mata tamkar a majigi.
*****
TUSHEN LABARIN!

Bayan haihuwarta ta biyu ne jini ya tsinke mata, washegarin haihuwar yar ta koma ga mahaliccinta.

Ita kuma ta samu matsalar da dole aka cire mata mahaifa bakidaya.

Shi kadai gare ta, shi kadai Allah ya bar mata, UWAIS kenan.

Mahaifinsa Justice Abdulkarim Shagari tsohon alkali ne dan asalin jihar Sokoto, wanda ya taka har matsayin Grand Khadi a lokacin rayuwarsa.

Dan asalin Sokoto ne amma a Kano ya rayu sanadin aikin sa da ya samu a Kano, ya yi kuma aure da Safeeyah tun yana dalibin digiri na biyu a kasar ta Sudan inda ya yi dukkan karatunsa.

Sun zauna a can shekaru biyar, sannan ya taho da ita kasarsa ta haihuwa, Nigeria, ya samu aiki da (Shariah Court of Appeal), ya sanya ta a jamiar Bayero, inda ta yi nata karatun a fannin tsimi da tanadi.

Allah ya azurta su da Da guda daya, ko ace daya tamkar da goma, shi ne Uwais, wajen haihuwarta ta biyu ne waccan matsalar ta faru.

Uwais na girma, sha'awarta da shaukinta ga son haihuwar diya mace na karuwa, bayan already an cire mata mahaifa.

Duk inda ta ga baby mace kamar ta zauce, ita ba yan uwa a Nigeria ba balle ta karbo yar riko, cikin yan uwanta kuma da ke Sudan ta tabbata babu mai ba ta, alhalin tana kasar Nigeria.

Don auren dan Nigeria da ta yi ma ba da son ransu ta yi shi ba.

Larabawa akwai kabilanci.

Maigidanta kullum cikin kwantar mata da hankali ya ke, don ta kara kwantar da hankalinta a kan haihuwar diya mace ya samo mata aikin koyarwa a Bayero University, ta zama cikakkiyar assistant lakcara.

Ba ta dade da fara aikin ba Allah ya yi wa Grand Khadi Abdulkarim Shagari rasuwa.

Mutuwar da ta gigita Safiyyah da tilon danta Uwais.

An dauki lokaci kafin su dawo hayyacinsu.

Kadaici ya kara yi wa Safiyya wadda danta Uwais ke kira Ammi yawa, daga ita sai danta ta ke rayuwa sai mai aikinta Talatu, wadda ta ke tare da ita tun Uwais na karami.

Shaawarta ga son diya mace bai canza ba bayan rasuwar mijinta, sai ma karuwa da ya yi a dalilin rashin miji mai tattali, soyayya, kulawa da nuna kauna wato Grand Khadi Shagari.

A wani dare da kadaici ya yi mata yawa, kuma ta yanke shawarar ci gaba da rayuwa a Nigeria madadin ta koma Sudan saboda aikinta, wani tunani ya fado mata.....

Ita dai ba za ta iya kara yin aure ba, don Uwais baya so, ya fada ya kara, muddin ta kara aure tayiwa Babansa kishiya a bayan ran sa shi Sudan zai koma wajen Kawunsa Shuraim wato Yayanta, wanda ke da da sa'ansa mai suna Mahdi, kuma ko ta yi aure ta san ba haihuwa za ta kara yi ba, don haka ta yanke shawarar dauko ya daga GIDAN MARAYU (Orphanage).

Ta hada da Uwais ta rike sun isheta rayuwar duniya, tayi musu
raino da tarbiyyah irin wanda take so sannan a karshe ta yi wa kowannen su aure da wuri, su haifa mata jikokin da zasu gina mata extended family mai albarka a kasar mijin ta, Nigeria.
******
"Tsintarta aka yi, a kofar makarantar firamare ta gidan Galadima, tana jaririya sabuwar haihuwa ko wanka ba a yi mata ba, a cikin kwalin taliyar indomie, ko suttura babu a jikinta, babu wata shaida da muka samu a kanta bayan wannan".

Shugabar gidan marayu na Kano wanda ke unguwar Nasarawa ta gaya wa Haj.

Safiyya.

Ta kara rike yar bakar yarinyar mai kyawun fuska sosai a jikinta, wadda ba ta fi shekaru uku ba.

Ta cike duk wasu formalities na daukar Da a gidan marayu ta karbe ta cike da so da kauna.

Tunda suka taho a cikin motar ta babban dan yatsan yarinyar nan yana cikin bakinta tana tsotso, alamu ne na cewa, yarinya ce mai tsananin hakuri.

A nan kantinan da ke kallon asibitin Nassarawa ta tsaya ta saya mata sutturun yara masu yawa, sannan suka karaso gida.

Ammi!

Uwais da ke wajen kwallon kwando a kofar gida tare da abokansa ya fada cikin mamaki a lokacin da ya ga ta fito daga mota dauke da yarinya.

Wace ce wannan?

Ina kika samo ta
Ya sake tambaya.

Murmushi ta yi masa tare da kamo hannunsa, amma sai ya janye daga gare ta cikin tsoro.

Ammi ina ki ka samo ya?

Ta mika hannu za ta sake kamo hannunsa, ya kara ja da baya.

Haba Uwais!

Kanwa ce na samo maka, were living a lonely life, ka ga ka samu abokiyar hira da wasa idan bana nan.

Kai ya shiga girgizawa da sauri da karfi.

Bana so Ammi, bana son ki da wani Da ba ni ba!.

Haushi ya sa ta shige cikin gida ta barshi a wajen.

Talatu ta fito daga kitchen tana wa Ammi barka da zuwa, tare da karbar yarinyar da ke hannunta.

Ina muka samo ya?

Tubarkallah haka?

Ammi ta ajiye handbag dinta a kan kujera, Kanwa ce na samo wa dan gidanki Talatu, ita ma ya ta ce daga yau.

Bayan wannan har inda yau ke motsi, Talatu ba ta san ina Hajiya Safiyyah ta samo yar ta Fahimah ba.

Ta san dai ba sato ta ta yi ba, amma tunda ba ta taba bude baki ta gaya mata ba sai ba ta takura mata da tambaya ba.

Farat daya yarinyar ta shiga ranta, in Ammi na wajen aiki to Fahimah tana hannunta.

Suka zage wajen kula da ita su biyu.

Suna karba-karba in Ammi ta tafi aiki.

Albashin Ammi da shi suke rayuwa cikin rufin asiri, rayuwarsu very simple, ta wadanda ilmi ya wadata.

A wancan lokacin cikin gidajen malamai na sabuwar jami'ar Bayero suke zaune gidan dajami'ar Bayero ta baiwa Ammi.

Sabida ya fi wa Ammi saukin zirga-zirga.

Acan ta sanya Fahimah a (staff school).

Lokacin Uwais ya gama ya shiga sakandire a Musa Iliyasu wadda itama nan kusa dasu take.

Grand Khadi Shagari ya bar musu gadon tankareren gidan da suke ciki a halin yanzu wanda suka dawo cikin sa bayan Fahimah ta fara karatun sakandire a 'Yan Dutse College, ya bar musu gidan wanda ke unguwar 'Yankaba da tsabar kudi a banki, wanda Ammi ta sayi hanun jari da su a bankuna duk wata suna karbar kamasho.

A haka ta dauki nauyin karatun yayanta guda biyu, Uwais da Fahimah!

Cin zalin na duniya da mugunta iri-iri babu irin wanda Uwais bai yi wa Fahimah ba, wadda har gobe bai san a ina Ammi ta samo ta ba.

Sai da ya shekara ashirin ne ya gane Ammi a gidan marayu ta dauko Fahimah, don lokaci zuwa lokaci yana kai su gidan marayu ta gaida wata mata wadda ya fahimci shugabar gidan ce.

Ita kanta Fahimah ba ta san hadinta da Hajiya Asabe ba, da Ammi ke yawan kai ta ta gaishe ta in ta samu lokaci, kuma hankalinta da dan guntun tunanin ta na lokacin bai taba ba ta cewa gidan marayu gidansu ne ba.

Ta fi daukar Hajiya Asabe a matsayin kawar Ammi, don in suka hadu suka tsinke da hira har ba sa son rabuwa.

Daga baya Hajiya Asabe har gidansu tana zuwa, Ammi na yi mata alheri sosai.

Musanman lokacin da ta zo aurar da diyarta ta fari Ammi ce ta dauki nauyin gado da kujeru.

Tun daga lokacin da Uwais ya gane daga inda Ammi ta dauko Fahimah tsanarshi da ita ya karu, ya nunku.
Chapter 4 · 0% Book details