Sashe 10
Fahimah Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mumini an sanshi da karbar kaddarar Ubangiji da kasancewa cikin godiyarsa ala kulli halin.
Wannan damuwar da ki ka sanya kanki babu abin da za ta janyo sai nakasu ga lafiyar zuciya da kwakwalwar ki.
Insha Allah wata mai kamawa za mu je Umrah mu yi ibada mu nemi kusanci da Ubangiji, za ki samu sukunin zuciyarki insha Allahu.
Haka Ammi ta yi ta lallashin Fahimah, da kalamai masu dadi da nuna kauna har sai da ta sanya murmushi a kan fatar bakinta.
******
9/23/21, 8:15 PM - Buhainat: Kafin muryarsan nan mai tada tsigogin jikinta ta biyo baya.
A yau har wani kauri ta kara mai nuna ya zama cikakken mutum.
Wanda ya gama mallakar duk abinda da Da namiji ke bukata a rayuwar sa.
Ta juya a hankali ta dube su da fararen idanunta suna shigowa, hannun su cikin na juna sun yi balain dacewa da juna, kyau na bugun kyau.
Ko hasidin iza hassada ya kalle su sai ya yaba su a ransa.
Wani abu wai perfect match.
Da gaske KISHI gaskiya ne a tare da kowacce diya mace, kuma Fahimah ta ji shi a kirjinta har fiye da misali, yau ga ta ga matar Uwais!
Wadda ta dade tana kimanta zuwan ranar haduwar su da juna, amma murmushin da Amrah ta yi mata da innocence looks dinta sun sanya Fahimah mayar mata da martanin murmushinta.
Ta kuma amsa sallamarta.
Sannan ta maida kai ga abinda take yi bata kara kallon su ba.
Uwais kamar ya fashe don bakin ciki don bai so Amrah ta ganta ba shiyasa ya kawo ta da safe, lokacin da ya tabbata tana barci.
Bayan sun wuce falon zuwa falo na gaba Amrah ta juya tana kallonsa da sigar da ta ke kallonsa, wadda ta bambanta da yadda ta ke kallon kowa, ta ce,
Ina ku ka samo kyakkyawar budurwa haka?
Ba ka taba gaya min kana da sister ba.
Cikin harshen Turanci ta yi maganar.
Fahimah daga inda ta ke tsaye tana jiyo shi yana bai wa matarshi amsa da cewa, Mai aikin Ammi ce.
Suka wuce turakar Ammi, Amrah na waiwayonta tana ta mata murmushi, sai ta samu kanta da kasa maida mata martani sakamakon zuciyarta ta yi bakikkirin da jin amsar da Uwais ya bayar a kanta.
Daga bisani ta yi murmushi mai ciwo, cikin ranta ta ce, ban da abun ki Fahimah, don Uwais ya ce ke yar aikin gidansu ce ai ya kara miki matsayi, tunda bai ce da matarsa tsinto ki suka yi a gidan marayu ba.
Maganar a ce ita matarsa ce ma ba ta taso ba.
Ta ci gaba da daukar aure a tsakaninsu a matsayin shifcin gizo, zai fi mata sauki; wato irin almarar nan mai zuwa ta wuce wa dan adam yadda kowacce almara ke zuwa ta wuce, haka aurenta da Uwais zai zo ya wuce ba tare da ya zama actual reality ba.
A hankali ta zame jiki daga wurin zuwa dakinta tana cewa cikin ranta, ina ma ita ce Amrah?
Watakila da ita ce ke da kyan da Amrah ke da shi da Uwais ya so ta.
Ta yi maza ta kwabi zuciyarta a kan hakan.
Shes proud of her own beauty no matter what, watakila ko da ta fi duk matan duniya kyau asalinta ma kadai ya isa ya sa Uwais ya kyamace ta.
Don haka Fahimah ta soma kallon aurenta da Uwais a matsayin dabaibayi rather than defensive kamar yadda Ammi Safeeyah ke kallonsa.
Anya kuwa tunani da tsinkayen Ammi a kansu daidai ne?
Ta yi ta zama da igiyar auren Uwais a kanta kenan don kawai a kira ta matarsa?
Anya auren bai zame mata dabaibayi ba ya hana ta yancinta na yammatanci?
Ko da ta ke yar gidan marayu in da Ammi ta yi hakuri ba za ta rasa me sonta a duniya ba, ko ta auri orphan dan uwanta a gidan marayun, soyayyar da zuciyarta ke yi wa Uwais da ma mai zaman kanta ce.
Da Ammi ta yi hakuri ba ta yi amfani da karfin ikonta na uwa ba wajen ganin Uwais ya aure ta ba, da sannu za ta iya overcoming dinta (rinjayarta).
Haka ta yi ta saka da warwara ita kadai a daki tanajuyejuye akan gado, idan ta ce ta yi watsi da alamarin Uwais, idan tsautsayi ya gifta suka hadu ko yaya ne, tofa dole sai zuciyarta ta motsa.
Daga nan ta gane cewa soyayyar gaskiya abu ce da zuciya ba za ta iya kaucewa ba.
Saidai ayi mata pretending.
Amma daga yau da Uwais ya gaya wa matarsa ita yar aikin gidansu ce, daga yau za ta soma yaki da duk wata soyayyar UWAIS daga zuciyarta, ko da kuwa da karfin addu'ah ne.
******
Amrah ba ta samu wata special reception daga Ammi ba, daga gaisuwa shi ke nan, ta ce,
In ce ko ba matsala?
Amrah ta ce, Babu Ammi.
To Allah ya yi muku albarka.
Daga haka ta shiga wata hidimar a daki.
Ta dai fahimci Amrah za a zauna lafiya da ita daga dukkan alamu, bata da kwaramniya kuma bata da girman kai ba kamar sauran yayan masu kudi irinta ba, shes very simple a cikin muamalarta da kowa.
Tunda suka dauko hanyar komawa gida, Amrah ke zubo wa Uwais tambayoyi duk kuma a kan Fahimah, shi kuwa komai ta tambaya cewa yake bai sani ba.
Yadda ta ga yarinyar shi ma haka ya ganta a gidan.
Amma wallahi Habib-Qalby ba ta yi kama da yan aiki ba.
Zubinta irin na matan kasar Sirreleone irin kalar fatarta nake burin ina ma in samu.
I hate so much brightness.
Ga dasashin cikin bakin ta irin wanda nake shaawa, da a ce ni mazauniya ce da na roki Ammi ta bar min ita, I just like the girl.
Uwais dai sai "umh" yake cewa, yana ci gaba da tukin motarsa cikin nutsuwa har suka isa gida.
Sun yi shirin kwanciya ya shigo dakin Amrah da zummar yin wani abu, sai ya ganta tana kora magani a bakinta.
Da sauri ya idasa shigowa dakin zuwa gabanta.
Lafiya Amrah?
Ba ki da lafiya ne?
Ta ce, No, lafiyata kalau.
Contraceptive pills ne nake hadiya sabida su aka min recommending kan cewa sun fi rashin illah ga wanda bai taba haihuwa ba.
Tunda Uwais ya hadu da Amrah daga dating (soyayya) zuwa aurensu ba su taba samun sabani ba, bai taba jin haushinta a ransa ko miskala zarratin ba.
Amma yau ya ce,
Amrah!
Cikin kakkausar murya.
Zan amince da komai, karatu a Malaysia, amma ban da a dinga zubar min da kwayayen haihuwata.
Ban sani ba ko iya su Allah ya yi nufin ba ni a duniya.
Amrah ta dube shi tana kankance idanu, Habib-Qalby, me ka ke nufi ne?
Ina MBBS student in haihu yanzu?
Kwata-kwata nawa nake?
Ko shekaru ashirin ban rufa ba, ni karatuna ya fi min komai muhimmanci, wallahi...
Uwais ya yi mata wani irin kallo, ya ce, Har da ni Amrah?
Ai da abuna ka gan ni ka aure ni, ban ga dalilin da zai kai ni haihuwa yanzu ba.
Uwais ya yi sake da baki yana kallonta.
Rana ta farko da ya soma tunanin anya nan gaba zai iya tankwara Amrah?
Yayi sake tun farko.
Anya bai yi kuskure ba da ya nuna wa Amrah matsananciyar soyayya a fili?
Juyawa ya yi ba tare da ya ce komai ba, zuciyarsa na tafarfasa.
Ba abin da yake so a duniya irin haihuwa, kasancewar shi daya tal!
Allah ya bai wa mahaifiyarsa.
Yayan da yake burin haifa su yake fatan su zamo masa yan uwa.
Ashe Amrah rariya ta ke kora su.
Don haka kwanaki biyu da suka biyo baya ya dauke wa Amrah wuta, amarci da soyayya sun tsaya, wanda hakan ya jefa Amrah a damuwa.
Amma abinda yake so da ita ba mai yiwuwa ba ne.
Ya za ta yi da Da alhalin tana karatu a wata uwa duniya?
Sai yanzu ya fahimci cewa, ashe dai duk son da yake wa Amrah har gobe yana nan a Uwaisunsa.
Murmushinsa duk ya tsaya, haka yawan sakewar da yake wa Amrah.
Damuwar da Amrah ta shiga ba ta misaltuwa, musamman da yake Uwais ya koyar da ita wata irin soyayya mai wuyar bari, yanzu ya dawo ya koma tamkar ba shi ba, ita kuma ba za ta iya bin raayinsa ba.
Aunty Murjanatu ta kira domin neman shawara tana kuka, Uwais have changed completely, haihuwa yake so Aunty Murja, ni kuma ban shirya ba.
Ya kasa fahimtata, akalla ina bukatar shekaru biyar nan gaba kafin na amince na fara haihuwa.
Murja ta ce, Amrah in kina son kwanciyar hankali a gidan aurenki ki bi abin da mijinki ke so, tun ba ki yi sanadin da dimbin soyayyar da yake miki za ta ragu ba.
Komai na Allah ne, ke ba ki isa ki tsarawa kanki rayuwa ba sai abin da Ubangiji ya tsara miki, haihuwa ba ta hana komai sai ki dauki Nanny.
Da haka Murjanatu ta samu ta rarrashi Amrah ta kuma tabbatar mata a daren yau za ta je ta bai wa Uwais hakuri.
Shiri na musamman Amrah ta yi zuwa dakin Uwais cikin wasu tausasan nighties.
Uwais na loosing tie din wuyansa bayan ya dawo aiki bai ji motsin shigowar Amrah ba, sai ji ya yi ta rungume shi ta baya, kamshin sassanyan turarenta Yves Saint Laurent da sulbin hannunta su suka gaya masa ita ce.
Ya lumshe ido yana tuno wahalar da ya sha a kwanakin nan da ya hora kansa da rashin Amrah.
Zai iya cewa shi ne horo mafi muni da ya taba karba a rayuwar sa bayan horon auren Fahimah wanda sanadin auren Amrah ya ja masa, amma ya fiye masa a kan ya biye wa abin da Amrah ke so.
Ko Ammi ta ji za ta kara tsanarta ne a kara lika masa wannan abun aman (Fahima).
Shi kuwa da wani abu makamancin auratayya ya shiga tsakaninsa da Fahimah gara ya koma mace (ya yi losing manhood dinsa).
Im sorry Habeeb-Qalby, something like this will not happen again I surrender.