← Book details Fahimah Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 35

Sashe 2

Fahimah Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kunna motar da ya yi, da reverse hadi da cin taya ya bar harabar bankin shi ya tada Faheemah daga wahalallen barcinta.

Barcin yunwa da gajiya.

Ta dube shi ta gefen ido, ya nutsu yana tukinsa cikin gwanancewa.

"Fuskar ta salihai, kyakkyawa a ido, amma kamar ta Firauna a zuciya.

Fahima ta fada a zuciyarta.A shekaru goma shaf takwas na rayuwarta da ta yi tare da shi gida daya, bai taba kyautata mata ko sau daya ba, sannan ba za ta taba iya fadar wani alkhairi guda daya da ya yi mata ba a matsayinsa na Yayanta a kan dalilin da ba ta sani ba.

Duk da kasancewar su biyu ne kacal a wajen mahaifiyarsu Hajiya Safiyya, ta sa a ranta Uwais makiyinta ne na babu gaira babu dalili, don bata san laifin da take masa ba, Ammi ma bata sani ba, don har a cikin kwayar idanunsa tana iya hango tsantsar kiyayyar da yake mata, a gaban kowa kuma ba ya iya boyewa including mahaifiyarsu Ammi Safiyyah.

Ita kuma nan duniya babu mai burge ta irin UWAIS ABDULKARIM SHAGARI!!!

Wani kwayan mutum guda daya da ya yi mata babakere a zuciya.Daga baya ta fahimci shi Ammi ta haifa ba ita ba daga lokacin da ta soma hankali, amma in za a yanka ta ba ta san alakar da ke tsakaninta da su ba.

Ita dai ta taso ta ganta a gaban Hajiya Safiyyah Basudaniyyah, cikin wata irin kulawa irin ta UWA da duk wata kyautatawa da uwa ke wa danta.

Ammi Safiyya is more than a mother a gare ta, she is an ANGEL wadda Allah ya halicce ta a hannunta domin ta zame mata kafadar da za ta kwanta a kai ta yi kuka, ko dariya.

Yawan kyautatawar Ammi, jin kai da kulawarta gare ta ke hana ta yi mata titsiyen da Ammin ba ta so na ita wace ce uwarta, wane ne ubanta???

In tana son ganin bacin ran Ammi, to ta yi mata wadannan tambayoyin.

Don haka ta dade da daina yi mata tun kafin ta kawo munzalin adolscence.

Ta yarda da abin da Ammin ke gaya mata kullum, ITA CE UWARTA, ITA CE UBANTA amma ta sani watarana na zuwa da dole Ammin za ta yi mata confessing daga inda ta samar da ita tunda ko makaho ya shafa a halitta ya san Ammi balarabiyar usuli haka ba ita ta tsugunna ta haife ta ba.

Kodayake ba'a judging haihuwa da kamanni ko kalar fata, amma ita kam ko daga kalar fata, gashin kai da yanayin kirar jiki za ka san Ammi balarabiya ce, yayin da ita kallo daya za ka yi mata ka tabbatar cikakkiyar bahaushiya ce, jikar Barbushe da Tsimbirbira.

To amma me ta ke nema a iyaye wanda Ammi ba ta yi mata ba?

Ta yi mata komai a rayuwa wanda a kullum yake mantar da ita cewa, ba ita ta haife ta ba, sai dai kulafuci irin na dan adam.

Musamman akan son tabbatar da legitimacy din ta.

A duk lokacin da wani tunani makamancin haka ya sarke ta, fuskar Ammi da murmushinta na UWA a gare ta take daukowa ta dora a kan idanunta, sai kowanne tunani, da kowacce damuwa da kowanne bacin rai su bace su kama gabansu.

A duk lokacin da Uwais ya yi mata kallon nan nasa na tsana da kyama, murmushin Ammi kadai ke gusar da shi komai girmansa.

A yayin da ka ke da uwa irin Ammi a gefe, babu wani bacin rai a rayuwa da ya isa ka yi masa kuka.

Fahimah ta kan yawaita fadar hakan a zuciyarta.

Tana wannan tunanin cikinta kuma na ci gaba da kartawa ta ji Uwais ya kashe motar a parking lot na gidan su, sai a lokacin ta ankara sun zo gida.

Ya fice ya barta a motar ba tare da ya ce da ita ko uffan ba.

Tana fitowa jiri ya kwashe ta, sai da dafa bango sannan ta iya karasawa zuwa cikin gida.

Shi tuni ya jima da shigewa part dinsa.

Wanda dole sai ka ratsa ta main parlour zaka isa part din nasa.

Ammi bata yarda ta ware shi daga can waje ba, sabida tsantseni na tarbiyyah irin nata.

Ammi da Talatu har suna hada baki wajen tambayarta lokacin da ta shigo wujiga-wujiga da ita.

Fahimah, me ya zaunar da ke a makaranta haka?

A gurguje ta yi musu bayani Mr.

Edward ya tsare su kan shirye-shiryen su na fara SSCE, da sassanyar muryar ta wadda ta kara sirancewa sabida yunwa da gajiya, sannan ta durfafi dining-table tana zuba abincin jikinta har rawa yake, kuma da ma tana da ulcer.
9/23/21, 8:15 PM - Buhainat: A bakin get ya tadda Jabir yana jiransa, a motar Uwais za su tafi, in sun dawo ya ajiye shi a gidansa ya juya.

Tunda suka hau kan titin da zai kai su Bompai wuta ta dauke wa Uwais saboda fargabar irin tarbar da kuma amsar da zai samu daga Alhaji Umar Dikko.

Jabir shi kadai yake zuba hirarsa ga dukkan alamu shi kam bai da sauran matsala a rayuwa, da ya fahimci halin da Uwais ke ciki, sai ya yi dariya ya dafa kafadarsa.
addy is very friendly, kawai za ka sha tambayoyi, in ya ga dama kuma ya ce ka jira auta for 6 years ta gama MBBS dinta.

This is for sure na tabbata zai fadi hakan.

Ashe da na tattaro kayana na koma gidansa a Abuja idan yana ganina kullum zai gane ba zan iya jiran ba".

Dariya Jabir ya sake yi, ya ce, Kada ka tsorata da dukkan tambayoyinsa, be brave, be yourself, sannan kada ka boye masa komai ya tambaye ka.

Alhaji Umar Dikko na zaune a luntsumemiyar kujerar sitting room dinsa, da ganinsa ka ga bafillacen usli, furfura ta cika a gashin kansa amma fatar jikinsa sumul ta ke, babu tsufan, sabida samun hutu.

Jabir ya yi musu iso suka shiga already ya san da zuwan nasu.

Dukkansu a kasa suka zube suka kwashi gaisuwa, irin ta neman iri, fuska sake yake amsawa har yana tsokanar Uwais ya aka yi ya bari abokinsa ya shiga daga ciki shi yana daga waje har yanzu?

This is kafin ya ji gundarin abin da ke tafe da su.

Daddy, kamar yadda ka sani Uwais abokina ne, tun a A.B.U, Daddy abin da ya kawo mu shi ne, ya zo neman amincewarka ya fara neman auren Amrah.

Cikin mamaki Alhaji Umar Dikko ya ce, Amrah?

Amrah wacce?

Jabir ya ce, Autar Mama dai Daddy.

Ya tsura wa Uwais ido na 'yan dakikai inda ya hango cikar kamalarsa ko ta ina bai ga makusa ba kamar yadda komai da ke jikinshi ya nuna ba karamin mutum ba ne, ilmi da hatimin nasara sun wadace shi.

Sannan ga wani irin sassanyan kyau da ya rasa gane daga kabilar da ya dauko shi.

Above all Allah ya yi ma Uwais wani irin kwarjini, ilhama da cikar zati da ya wuce ya nemi alfarma wurin mutum a kasa yi mass.

Amsar da ya so bayarwa sai ta canza kanta ba tare da ya ankara ba, domin da farko so ya yi ya ce su tashi su tafi, ba yanzu zai yi wa yarsa aure ba.

Wane ne Babanka?

Kai dan wace kabila ne?

Gama na ga ba Bahaushe bane
Uwais ya muskuta sannan ya kara dukar da kansa in ka ganshi a wannan lokacin kamar bawan da ke neman taimako.

Ji yake zai jure komai, zai iya komai in dai Alhaji Dikko zai ba shi auren Amrah a karshe.

"Sunanan Babana Grand Khadi Abdulkarim Shagari, ya jima da rasuwa, na girma a hannun mahaifiya ta, Babana basakkwace ne, mahaifiyata basudaniya ce.

Alhaji Dikko ya gyada kai, sannan ya kara jifansa da tambaya.

Mene ne matakin karatunka?

Kuma mece ce sanaarka?

Uwais ya zuki numfashi, a ransa ya ce, wannan wane irin mutum ne?

Ina da kwalin digiri na biyu, sannan ni banker ne da Guaranteed Trust.

Alhaji Umar Dikko ya gyada kai cikin gamsuwa, sannan ya ce, Kana da masaniyar cewar Amrah karatun likita ta ke yi a matakin farko?

Za ka iya jiranta ta kammala tsawon shekaru shidda?

Uwais ya hadiyi yawu da kyar shi fa jiran ne ba zai iya ba, burinsa ya bude ido ya ga ya mallaki Amrah, don haka bai yi kasa a gwiwa ba.

Daddy, ku yi min alfarma, na yi alkawarin barin Amrah ta yi ta karatunta a dakina har sai ta ce ya ishe ta.

Ya kara dukar da kansa cike da zullumi da fargabar amsar da zai samu daga Alhaji Umsr Dikko.

Bai san dalilin da ya sa farad daya yaron ya shiga ransa ba.

Kamalarsa ce ko kamewarsa?

Ba zai iya cewa ba, ga wasu exceptional qualities da ya gani a tare da shi.

Shi kansa Jabir a yadda ya san mahaifin su bai zaci tambayoyin Daddyn nasu za su tsaya a nan ba.

Sosai Alh.

Umar ya dubi Uwais kafin ya ce,
Na ba ka izni ka nemi auren yata.

Idan ta amince da kai dari bisa dari zan iya ba ka aurenta a bisa alkawarin da ka yi min na cewa za ka barta ta ci gaba da karatu a gidanka.

Besides ni kuma zan yi nawa kyakkyawan binciken a kanka da iyayenka, idan na samu wani mummunan hali a tare da kai zan dakatar da kai.

My daughter is innocent ka yi taka tsaftacciyar muamala da ita a cikin neman aurenta.

Farin ciki ya sa bakin Uwais ya kasa rufuwa, kansa a kasa ya yi godiya tare da alkawarta wa Daddyn insha Allahu zai kiyaye abin da ya fada masa, kuma da yardar Allah ba zai samu wata mummunar shaida a kansa ko iyayensa ba.

Suka fito shi da Jabir, inda Jabir din ya ja shi suka shiga cikin gidan wajen amaryar Babansu Aunty Nana.

Suka gaisa tana da kirki sosai.

Jabir ya gabatar mata da Uwais matsayin abokinsa, kuma manemin auren Amrah, wanda Daddy ya san da zamansa a yanzu.

Aunty Nana ta yi mamaki sosai, don ta san Daddyn ya ce ba zai aurar da Amrah ba sai ta kammala MBBS.

Ta karbi Uwais hannu bibbiyu, ta yaba da komai nasa cikin ranta.
Chapter 2 · 0% Book details