Sashe 15
Fahimah Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta gaishe su, muryarta ba ta fita sosai sabida kukan da ta ci.
Baffa Haruna ya hau yi mata nasihar da ba ta san dalilinta ba, yana fadin ta zauna lafiya da abokiyar zamanta su ba wa mijinsu hadin kan da zai iya adalci a tsakaninsu.
Ta dauki kishiyarta 'yar uwa ba kishiya ba, ta rike girmanta da Allah ya ba ta.
Fahimah dai ba ta dago ba har zuwa lokacin da Kawu Shuraim ya ce, "Ki yi hakuri da dan uwanki Uwais, kin san ba da son ransa aka yi aurenku ba.
Wannan burin na mahaifiyarsa ne, don haka tabbas sai kin yi hakuri Fahimah a zamanki tare da Uwais.
Don Uwais wani baudadden mutum ne wanda idan aka yi gabas shi sai ya yi yamma, in aka yi kudu shi sai ya yi arewa.
Hakurin shi ne kadai maslaha har zuwa sanda Allah zai daidaita ku, don haka ba za mu gaji da cewa ki yi hakuri ba kin ji ko Fahimah?"
A hankali Fahimah ta dago rinannun idanunta ta sauke a kan Ammi Safeeyyah.
So ta ke ta tantance ma'anar kalaman da ke fita daga bakunan kawunnan Uwais, shin ko idanun Ammi za su ba ta assurance na abin da dattijan nan ke cewa?
A zahiri cikinsu babu sa'anta, babu abokin wasanta balle ta yi zaton wasa ne irin na kaka da jika suke yi mata.
Ammi ta gyada mata kai a hankali tana murmushi da ba ta tabbaci daga fararen kwayan idanunta.
"Uwargidan Uwais!".
In ji Ammi tana mai sanya tattausan hannunta cikin na Fahimah.
"Allah ya ba ku zaman lafiya.
Da zuri'a mai albarka.
Allah ya kade fitina da dukkan abun ki".
Fahima sai ta samu kanta cikin wani hali na 'fita hayyaci' na wucin gadi.
Ta nemi jinta da ganinta na 'yan dakikai ta rasa.
Don haka har su Baffa suka yi sallama da Ammi suka fita Fahimah ba ta koma cikin hayyacinta ba.
Watakila dai mafarki ta ke yi...
Irin mafarkin da dan Adam ke yi idan ya cika sanya tunanin abu a ransa.
Mafarkin kasancewa matar Uwais ai ba yau ta fara ba.
Don haka na yau din ma in ta yi hakuri za ta farka ne kada ta yaudari kanta.
Har sai da Ammi ta raka su Baffa ta dawo Fahimah na nan kafe a inda Ammi ta barta, rokon Allah ta ke yi a zuci ya yi gaggawar farkar da ita daga wannan rudadden mafarki.
Ammi na shigowa ta kama hannunta ta cira ta tsaye suka nufi dakin barcinta.
A gefen gadonta ta zaunar da Fahima wadda zuwa yanzu ta fara ji a jikinta yau ba mafarki ta ke ba, wani babban alamari ke shirin faruwa da ita, wanda ba za ta ce alkhairi ba ne.
Idan kalamansu gaskiya ne sun aura mata Uwais shin hakan zai haifar da Da mai ido a gare ta?
Wanda ba ya sonka fa bai sonka har abada, kuma ba zai taba sonka ba balle an hada auren da na matar da yake so, ai kawai in hakan ya tabbata ta amince kawai karshen Fahimah ya zo (the end of FAHIMAH).
Don dai ta san Uwais ba zai barta da rai da numfashi ba, ba zai barta ta shaki numfashi a matsayin matarsa ba, balle su hada inuwa daya, inuwar ma wadda ta fi kowacce alfarma wato inuwar aure.
Maimakon farin ciki duk da mayataccen son da zuciyar Fahimah ke yi wa Uwais, ji ta yi wani irin tsoro da firgici ya mamaye ta, kada Allah ya nuna mata ranar da za ta kara haduwa da Yaya Uwais ko da a hanya ne.
Kamar yadda suka ce burin na Ammi ne, ta yadda Ammi za ta yi mata kauna fin haka.
Ji ta yi hawaye sun jika fuskarta sharkaf ba tare da ta ankara ba, Ammi gorar ruwa ta dauko a firji mai sanyi ta zubo a tambulan ta mika wa Fahimah, ganin yadda ta ke yanka gumi daga zaune kamar wadda ke dakin nakuda duk da rabar iyakwandishan da ta lullube dakin Ammin.
Kusa da ita Ammi ta zauna, ta ce, kuka Fahimah?
Ki yi hakuri in na miki ba daidai ba, ban iya rabuwa da ke Fahimah zuwa gidan wani, bansan irin kalubalen da zaki fuskanta ba, haka ba zan iya jurar ki wulakanta a gidan aure ba, a dalilin haka ne na yanke shawarar aura wa Uwais ke ba tare da neman shawara ko amincewar kowannenku ba don na san ba za ku taba amincewa ba bisa karan-kanku.
Amma Allah shi ne shaidata kan cewa ALHERI nake nufinku da shi, ba za ku gane hakan ba ku duka sai ranar da bana raye.
A yanzu dai ba hadin kanku nake nema ba don abin da nake nema na same shi, burina ya cika.
Fahimah kin dauwama cikin zuriata.
Dukkanku kuna bukatar lokaci kafin ku tantance aya da tsakuwa, ki kwantar da hankalinki in dai a kan Uwais ne ba zan kai ki gidansa ba sai bisa amincewar zukatanku ku duka.
Ki je ki hada kayanki na sati biyu, gobe insha Allah in an kai masa amaryarsa ni da ke za mu tashi zuwa umrah, ba za mu dawo ba sai bayan sati biyu.
Jiki a mace Fahimah ta mike amma ta kasa ce da Ammi komai.
Idan na yi miki ba daidai ba, idan hukunci na bai miki daidai ba ki yi hakuri ki yafe min Fahimah.
Da sauri Fahimah ta juyo, tausayin Ammi wadda tsufa ya soma bayyana a gare ta duk sai ya kamata.
Cikin rishin kuka ta ce,
Ammi, ba ki yi min komai ba.
Sannan ta sa kai zuwa dakinta.
Burinta a rayuwa komai ya girmansa a yau ya cika.
Mafarkanta sun zamo gaskiya, ta zamo wani bangare na Uwais Shagari, amma abin mamaki ta kasa farin ciki da hakan, watakila don girman kalubalen da ta ke hangowa ne, watakila kuma don ta san auren ba zabin Uwais ba ne, in ma ya sani ke nan.
Jin kanta ta ke tamkar wadda ta rako dukkan mata duniya sabida rashin saarta a rayuwa.
Gabadaya maganar auren da auren kansa ba ta san a ajin da ya dace ta sanya su ba.
Da me za ta ji ne a rayuwarta?
Maraici, rashin asali and finally BORANCI?
Kodayake Ammi ta ce ba kai ta gidan Uwais za ta yi ba, sai ranar da dukkansu suka amincewa hakan.
Ranar da ta tabbata ba mai zuwa ba ce, sai dai ta dauwama da sunan matar Uwais, amma auren ba zai taba zama reality ba.
Yadda Fahimah ta ga rana haka ta ga dare a wannan ranar, kitsawa ta ke tana tufkewa sannan ta warware.
Ta rasa makomar rayuwarta.
A karshe ta sa a ranta cewa, ya kamata ta yarda cewa, duk bakinta da Uwais ke fadi yana gorantawa ita ma mace ce kamar sauran mata, wadda wani namijin bayan Uwais zai iya gani ya ce yana so ya biya sadaki ya dauka ya kai gidansa.
In haka ne kenan ya kamata ta martaba kanta....Ta daina kallon kanta wulakantacciya.
Ba kuma ta kowacce hanya ba face ta yin gefe da UWAIS daga zuciyarta, shi da duk abin da ya shafe shi.
Ta maida komai nasa a bakomai ba, ta maida hankali kadai ga karatun da Ammi ke so ta yi, ta gina wa kanta future yadda duk ranar da babu Ammi za ta tsaya da kafafunta.
Ta dauki aurenta da Uwais a matsayin shifcin gizo in ba haka ba ita ce a wahale.
Ta tsaya ta nema wa kanta madafa ga rayuwarta ta gaba, wanda ba komai ba ne san yin ilmi da zai ba ta martabar da kyawun halitta ba ya badawa.
Kyawun halittar da ta fi tunanin a kansa ne Uwais bai sonta.
"Goddam Black" kamar yadda yake cewa tana alfahari da bakin fatarta.
Ammi ta sha gaya mata Black is beauty a duk lokacin da Yaya Uwais ya ce mata Black, kuma babu mummuna sam a yaya mata sai wadda ba ta martaba kanta ba.
Da kyar barci ya sace fahimah a wannan daren cike da tunanin da ta kwanta da shi.
******
Washegari Ammi da Fahimah suka tashi Umrah zuwa kasa mai tsarki.
Ammi ta yi haka ne don ta nesanta Fahimah da Uwais na dan lokaci, ya kuma samu lokaci da matar sonsa yadda ya kamata.
Duk adduar Ammi a Harami da Masjid Nabawy a kan Uwais da Fahimah ne, ita kadai ta san adadin abubuwan alkhairin da ta ke roka musu.
A can Kano, ango da amarya sun
a ta barzar amarci babu kama hannun yaro.
Uwais ya matukar jin dadin tafiyar Ammi da Fahimah, don ba ya so ko da kuskure a samu wanda zai gaya wa Amrah yana da wata matar bayan ita.
Alhaji Umar Dikko ya zuba dukiya a gidan Amrah kamar bai san zafin nema ba.
Gidansu komai ya yi acan-acan, soyayya ruwan zuma gangariya tsakanin Uwais da Amrah ba su taba gundura da juna.
Kafin Ammi da Fahimah su dawo Saudiyyah ango da amarya har wata yar kiba suka hada a kumatunansu sabida kwanciyar hankali da samun contentment in life.
Ranar asabar da daddare suka sauka a filin jirgin saman Malam Aminu Kano.
Fahimah ta yi wa kanta sayayya sosai, haka ta yi wa Talatu tsaraba.
Ba yadda Ammi ba ta yi da ita ba a kan ta yi wa Uwais tsaraba ko ta carbi ne, Fahimah ta ki.
Yadda ta yi fatali da Uwais daga zuciyarta haka ta ke fatan ta manta da ko sunansa.
Dan halak din shi ya zo daukarsu zuwa gida, ya sha excelcior fara kal, sai walainiya ya ke.
Da ganin shi ka ga angon daje kan ganiyar sa.
Motarshi kamar a nan ne kamfanin Maison Francis yake.
Ga wani farin gilashin PRADA da ya manna ma dogon karan hancinsa.
Kallo daya da Fahimah ta yi masa ba ta kara maimaitawa ba, duk da kuwa cewa zuciyarta ta yi mugun raurawa.
Sakamakon wata irin ilhama da kamala da aure ya kara wa Uwais, gara ita ta kalle shi sau daya, shi ko sau dayan bai kalle ta ba.
Sai da ya mallaki Amrah ya kara gane babu wata sauran diya mace da za ta kara burge shi a duniya.