← Book details Fahimah Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 35

Sashe 7

Fahimah Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta tabbata She must be beautiful like him in one way or the other.....ba kamar ita ba, and the LUCKIEST woman on earth...... watakila ranar ce ranar karewar numfashinta a duniyar Subhana......(ranar da zata ga matar Uwais).
******
9/23/21, 8:15 PM - Buhainat: Kwana uku bayan nan suka wayi gari da bako na ba-zata, kawu Shuraim daga Khartoum.

Ko kusa Ammi ba ta kawo a ranta abin da ya kawo Shuraim har Nigeria a kan maganar auren Uwais ne ba.

Rabon shi da kasar Nigeria an fi shekaru ashirin, tun rasuwar Baban Uwais, bayan nan kuma sau daya ya taba zuwa tun Uwais na yaro don kawai ya gan shi, sai kuma yau da ta ganshi a falonta bisa jagorancin Uwais ba zato ba tsammani.

Ammi ta rasa ina taka saka ina taka aje da Yayanta.

Ta cika shi da cima ta alfarma.

Ta sa Talatu ta gyare masa dakin baki, amma tun a wajen cin abinci ya gaya wa Ammi kwana uku kawai zai yi ya koma Sudan.

Sai dare suka samu zama officially ita da Kawu Shuraim.

Ta tambayi duka yan uwanta da yayansu, ya tabbatar mata kowa lafiya, sannan ya ba ta jakar himilin tsaraba da yan uwanta suka aiko ya kawo mata, wadda duk ta danganci cimar kasar Sudan da kayayyakin amfaninsu na yau da kullum.

Kawu Shuraim ya yi amfani da hikima irin ta manya bai nuna Uwais kararta ya kai ba, ya ce, Safeeyyah abin da ya kawo ni takanas kasarku ba komai ba ne face maganar auren Uwais.

Sai yaushe ki ka shirya yi masa aure, ko ko shi ke nan don ba mahaifinsa sai ki yi ta zama da shi a cikin gida har sai ya zama tuzuru?

In matar ce bai samu ba a duba masa a can Sudan cikin yayan dangi.

Da sauri Ammi ta ce, Ko kusa, ba mace ce bai samu ba, hasalima ni na dade da tanadar masa mata, ina jira ne ta kare karatun sakandire a daura musu aure.

Sai kuma ya kawo min wani zancen banza wai kanwar abokinsa yake so zai aura, ni kuma na soke zancen tuntuni.

Ba zan gaji da cewa mace ko da zubarjadu da yaqutu aka kerata ba za ta auri Uwais ba face Fahima ta.

Kawu Shuraim ya yi murmushi, ya ce, Wace ce ita Fahimar?

Ta ce, Fahima tawa dai da ka sani, wadda na dauka tun tana yarinya.

Ta gidan marayu?

In ji kawu Shuraim cikin shagube.

Ammi ta yi shiru, ya ce, To su waye madaura aurenta, kuma su waye suka kawo ta duniya?

Idan yar zina ce fa?

Sai ki hada da tsarkakakken Dan ki?

Wannan halaka kai don farantawa wani da me ya yi kama?

To ba da mu za a yi wannan danyen kazamin aikin ba.

Idan mafarki ki ke ki farka.

Gobe insha Allahu zan sa shi a gaba ya kai ni har Shagari wajen dangin mahaifinsa.

Mu hadu mu je mu nemo masa aure na mutunci da martaba.

Tun wuri ki san yadda za ki yi da bakar yar ki, Uwais ba zai karba bayafi karfin ta
Kawu Shuraim bai ankara ba sai jin shesshekar kukan Ammi ya yi a hankali ta ke kuka mai motsa zuciya.

Kafin ta share hawaye ta dago ido ta dubi Yayanta.

Alummar Annabi ina za ku kai rashin adalci?

Su wadannan yaran me ye laifinsu?

Zabin su ne zuwan su duniya a haka?

Ko kuwa laifin iyayen su?

Har ce mata ka ke BAKA don kawai kuna farare larabawa, shin zabinku ne fitowa da farar fata?

Ko kuwa tsarinku ne irin halittar da ku ke so Ubangiji ya baku?

Ni a wajena HALIN MUTUM shi ne yake sa wa a so shi, amma ba nasaba ko zubin halitta ba.

Don haka in har ni na haifi Uwais na kuma raine shi ba tare da taimakon kowa ba, Fahimah na yarje masa ya aura.

Duk da jikin Kawu Shuraim ya yi sanyi, amma bai ji dadin kalamanta na karshe ba, Safeeyyah ni ki ke gaya wa ke kadai ki ka raini dan ki ba tare da taimakonmu ba?

Ta girgiza kai da sauri, Ka yi hakuri dan uwana, ban fada da wannan manufar ba, amma idan har kun amince, Uwais zai auri Fahimah, ni ma na yi masa adalci ya hada su ita da zabin ran nasa ya aura.

Amma ita Fahima zan ci gaba da rikonta a wurina sai ranar da ya zo min da bakin sa ya ce ya karbi auren ta, burina kawai ya kasance da auren Uwais a kan ta, kuma da aurenta za ta yi karatun jamia.

Duk ranar da ya ankara cewa zabi na gari na yi masa, kuma ya shirya karbar matarsa sai ya yi min magana in kai ta dakinta.

Kawu ya ji dadin adalcin da Ammi ta yi wa Uwais a dalilin sa.

Ya sa mata albarka, ya ce kuma insha Allahu zai yi convincing Uwais ya amince da tsarinta.

Amma ko da Kawun ya yi wa Uwais bayanin da Ammi ta yi a washegari da safe, Kawu Shuraim na ganin yadda gumi/zufa ke barkowa daga kowacce kafa ta jikin Uwais kamar bai taba jin abin da ya girgiza shi irin wannan ba.

Don haka Uwais ka amince kawai, ban ga laifi cikin hukuncinta ba.

Mahaifiyarka ce da ta fi kowa hakki a kanka.

Hakkinka ne ka faranta mata don samun aljannah.

Na yarda va karamin so take yiwa yarinyar nan ba, domin kuwa har hawaye ta zubar a gabana.

Ta ce ba za ka dau yarinyar zuwa gidanka ba sai sanda ka shirya karbar auren ta, zuwa lokacin Uwais kana tare da matar da ka ke so kun hayayyafa, wannan auren garkuwa ne kawai ga yarinyar kamar yadda na fahimci yar uwata.

Uwais kowa ya rufa wa wani asiri, Allah zai rufa nasa.

Uwais Da na kowa ne, kuma samun uwa irin taka sai an tona.

A kan wannan marainiyar sai ka ga ta shiga aljanna kamar kiftawar ido mu muna gefe muna jan gindi a kan siradi, saboda girman kan mu da rashin tausayi.

Haka Kawu Shuraim ya ci gaba da yi masa nasiha da nusar da shi muhimmancin biyayya ga iyaye, musamman UWA, musamman ga su maza.

A fatar bakinsa bai ce ya amince zai auri Fahimah ba, amma shirun da ya yi da sunkuyar da kansa da ya yi na lokaci mai tsawo ba tare da ya ce komai ba, ya tabbatar wa Kawu Shuraim ba shi da ta cewa wai barawo a hannun mata.

Don haka Kawu ya yi ta sa masa albarka ya ce ya yi musu shirin tafiya Shagari washegari, ba zai bar kasar ba sai an karba masa auren Amrah tare da shi, sannan shi zai zama waliyyin Fahimah idan lokaci ya yi ba don komai ba sai don shima yana kwadayin irin ladan da yar uwarsa ke kwadayi.

Washegari ta jirgi suka tafi Sokoto shi da Kawu Shuraim, inda suka hadu da Baffaninsa na can Malam Haruna da Malam Sufyan wadanda kanne suke ga marigayi mahaifinsa Grand Khadi Shagari suka wuce Abuja gidan su Amrah.

Alhaji Omar Dikko ya yi musu tarba ta mutunci, aka tattauna a kan siyasa kafin su gangaro ga abin da ya kawo su, wato nema wa dan su Uwais auren diyarsa Amrah, Kawu Shuraimn bai fadi zancen Fahimah ba kada su rusa neman auren ta hanyar bata rawar su da tsalle.

Alhaji Omar Dikko ya ce, A da ban yi niyyar aurar da Amrah nan kusa ba, amma sabida yadda na ga Uwais da gaske yake sonta, sannan ya amince ta ci gaba da karatunta a Malaysia in ta yi hutu sannan ta zo masa, ko shi ya je, to ni ma na amince.

Amma in za a saba wannan yarjejeniyar tun wuri a yi hakuri kawai sai ta kammala".

Kawu Shuraim ya ce, an riga da an wuce wurin, domin Uwais ya amince, kuma su da komai nasu suke tafe, lokaci kawai suke so a sanya musu.

A takaice ba su bar Abuja ba sai da aka tsayar da ranar daurin aure watanni uku masu zuwa, lokacin ita Amrah ta samu hutu tana gida.

Hatta sadaki da kudin aure sun biya.

Farin cikin da Uwais ya samu kansa a ciki ya mantar da shi zancen wata Fahimah.

Bai kara tunawa da zancenta ba musamman da ya daina ganinta ma kwata-kwata.

Ta daina zaman falo don karatu ya yi mata zafi.

Nan da sati biyu za su fara WAEC kullum tana dakinta tana bitar littattafanta.

Zuwa yanzu Fahimah ta san zuciyarta ta samu sukuni daga duk wani kalubale dake addabar ta a baya, sabida karatu ya dauke mata hankali, amma na awa daya ba ta taba manta Uwais ba.

Kullum yana nan like a zuciyarta sai dai tunanin nasa ba ya hana ta sukuni kamar da, kuma ba ya hana ta fahimtar karatu, sannan ba ta da masaniya a kan batun aurensu, wanda ko a mafarkinta ba ta kawowa.

A haka ta fara zana WAEC cikin dimbin nasara, ta gama ta yi NECO sannan suka zauna suna hutawa kafin su zana jamb.

A can gidan Alhaji Umar Dikko gagarumin shiri suke na bikin Amrah, don ana ji da Amrah a familyn.

Tuni Aunty Murjanatu da Yayarta Aunty Wasila suka karbi kudi wajen Daddyn suka tafi Dubai don hado mata kayan daki.

Shi ma Uwais a nasa bangaren yana ta nasa shirin, ya kammala ginin gidansa da ke unguwar Sultan Road a Kano, gida madaidaici daidai babban maaikacin banki.

Amma fa komai na mace daya ne a gidan, kuma na mace daya ake ci gaba da yi.

Ba ya son tuna zancen wata Fahimah domin amai ne yake taso masa a duk lokacin da ya tuna wai tare zai aure su ita da Amrah....

Ban da uwa-uwa ce wa ya isa ya yi masa wannan kutsen cikin rayuwarsa?

A nasu bangaren, Ammi da yarta Fahimah babu wani shiri da suke yi, sun ci gaba da rayuwarsu as normal as before.

Ita Fahimah da ma ba ta san me ake yi ba, ko da wasa Ammi ba ta gaya mata ba.
Chapter 7 · 0% Book details