← Book details Fahimah Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 35

Sashe 14

Fahimah Complete Hausa Novel · about 8 min read

A yau da daddare Ammi zata tashi, tun jiya Fahimah ta hada mata kayan da zata bukata a babbar jakar matafiya, bata san me ke faruwa tsakanin Ammi da Uwais akan ta ba.

Karfe shidda na yamma Ammi ta shigo dakin ta, ta zauna dab da ita, sannan tace.

"Fahimah, ban miki bayani ba tun jiya, na bari sai yau da zan tafi, ki hada kayan ki kamar kala shidda, idan na tafi yau, ku kuma gobe da safe zaku tashi zuwa Ikko".

"Ni da wa Ammi.. wa muka sani a Lagos?"
"Ke da mijin ki zaku tafi, ko akwai damuwa ne a cikin hakan?"
Ta yi mata tambayar tana mai tsatstsareta da ido, don kada ta bata damar cewa komai.

Fahimah ta ji miyan bakin ta ya kafe, ta fiddo idanuwa kawai zuruuu!

Tana kallon Ammi.

Wani abu ya shiga kan Ammi da alama.

Ammi ta fahimci kallon da take mata sarai don haka tayi murmushi ta ce.

"Kalle ni da kyau ki kara, lafiya ta sumul-kalau, a kullum ina addu'ar Allah ya kawo sanadin da shakuwa ko yaya zata shiga tsakanin ki da Uwais.

Wannan nesa-nesan da kuke da juna shi yake bada babbar gudunmuwa wajen nesanta zukatanku da juna.

Na baku lokaci, ban zaci abin naku zai kai haka ba, amma na fahimci in za'a shekara a haka zaku zauna har auren ya lalace.

Ban ce lallai sai kun zauna gida daya ba, ni in dai zaku amsa sunan miji da mata ko a gidannan ne kiyi ta zama Fahimah, ki haifa min jikoki masu irin tarbiyyar ki, masu kama da ku, wadanda ni Allah bai bani da yawa ba.

Uwais in dai irin halittar marigayi mahaifin sa gare shi, wallahi bai iya tsallake wannan tarkon dana dana masa.

Ina nufin (bai iya yin kwanaki masu yawa babu mace).

Don haka wuyar ta ku fahimci juna shike nan ina tabbatar miki komai zai wuce kamar ba'a yi shi ba.

Sai tattali da soyayya da zasu biyo baya.

Soyayya zata yi kanta a zukatanku duk da yanzun ma bani da tabbacin kiyayya ce kuke wa juna.

In ma kiyayyar ce sai dai daga Uwais amma banda ke Fahimah.

Na ga soyayya mai yawa cikin kwarar idanun ki....shiyasa ma na jajirce na hada wannan auren, don idan mace na son namiji, to kuwa tabbas zata yi hakuri da shi duk rintsi, ta rike shi matsayin uban 'ya'yan ta albarkacin wannan so da ta ke masa.

Don haka bisa umarni na Fahimah, tashi ki hada kayan ki ki bi mijin ki zuwa inda duk yasa kafa wajen neman abincin sa.

Allah yayi muku albarka".

Fahimah bata ce komai ba, abinda bata son yi agaban Ammi shi ya zo (tears).

Ammi da kanta ta shiga zabo mata kayan da ya kamata ta dauka daga cikin na lefen ta da aka dinko.

Hatta kayan shafa dana kwalliya duk a acikin na lefen ta ta diba mata, ta hada mata su a matsakaiciyar trolley.

Fahimah sai bin ta take da jikakkun ido har ta gama.

Ta dube ta tana daga zaune a bakin gado duk jikin ta ya mutu.

Ta yi kamar bata gane halin data ke ciki ba na zullumi da anxiousness.

"In da abinda kike bukata na amfanin ki sai ki kara, na gaya miki kwana uku zaku yi, kuma in kun dawo da kwana biyu zaku biyo ni Sudan.

Bakin Fahimah sai motsi yake tana so ta tambayi Ammi.

"Shin Yaya Uwais ya amince da wannan tsarin nata?" Amma ta kasa furtawa har Ammi ta bar dakin.

Ba abinda ta kara kan kayan da Ammi ta hada mata sai inner wears, sannan ta dauki pad, kasancewar tasan ta kusa yin period.

Ita da Uwais din ne suka raka Ammi airport, karfe takwas na dare, kasancewar boarding flight zata bi.

Suna can har karfe goma Uwais na shige da fice da kayan da Ammi zata tafi dasu gun (screening) kafin lokacin tashin su yayi.

Gab da zasu tashi ya iso inda suke zaune itada Fahimah akan kujerun silver, yace.

"Everything is set Ammi, Allah ya kiyaye hanya, safe journey".

Ammi ta daga ido ta dube shi da murmushi, daidai lokacin da aka soma kiran pasinjan Sudan da su shiga jirgi.

"Ina fatan kafin in dawo, komai zai zama tarihi Uwais.

I mean tsakanin ka da Fahimah.

Za ka rungumi auren ka da hannu bubbiyu, ka yarda Fahimah amanar Allah ce a hannun mu Uwais.

Idan kana ganin takurawa ce na yi maka kayi hakuri ka bani dama, just give it a try, ni na haifeka Uwais don haka ka yarda bazan cutar da kai ba, komai na yi maka sai dai ya zamo taimako da soyayya.

Kai da kanka watarana zaka zo kana gaya mini WACECE FAHIMAH?

Wadanne irin baiwarwaki Allah yayi mata nayi maka wannan alkawarin.

Kyal-kyal banza ya daina diban ka.

Halin mutum shine abinda yake sawa a so shi ba nasaba ko zubin halitta ba...

Above all this black da kake cewa is but expensive beauty, but only ta BRAVE MEN Uwais......".

Ta karasa da murmushi, sannan ta mike tsaye don kowa ya shige ya barta,
"I'm hoping that my son to be among them".

Sannan ta kama hannun Fahimah wadda kanta ke sunkuye tana hawaye, ta sanya cikin tattausan hannun Uwais.

Ta dunkule su ta cure wuri guda, sannan ta dauki hand bag dinta ta wuce zuwa terminal.

Ya dade yana kalon bayan Ammi, sannan ya sauke ido akan hannun Fahimah dake dunkule cikin nasa, wadda tunda ta sunkuyar da kai hawaye take zubarwa bata dago ba.

Ji take kamar ta bi Ammi, kamar Ammi sallama take musu, kamar in ta tafi ta bar su su kenan bazata dawo ba!

Ta barta da miskilallen dan ta a inda bata da kowa.

Kalaman Ammi Safeeyah sun luguiguita zuciyarta; wai namiji akewa wannan rokon akan ya so ta ita wace irin mara sa'a ce a rayuwar ta?

Ta shiga ittikafin adadin soyayyar da Ammi ke mata....wadda duk itace silar hakan.

Ko don wannan kauna da soyayya na Ammi Safeeyah, ta ci alwashin zama karkashin igiyoyin auren Uwais no matter what, sannan against all odds, ko da zai dinga zaftarar naman jikin ta ne kullum yana sawa a miya saboda kiyayya.

Mu karasa a littafi na 2.
9/23/21, 8:15 PM - Buhainat: A daidai wannan lokacin Amrah na can cikin Aunties dinta ana yi mata kwalliya.

Kasa daga kiran ta yi da ta ga sunansa ke yawo a screen din, domin Amrah yarinya ce mai alkunya.

Aunty Murjanatu ta ce, Amrah ba kiranki ake bane?"
Aunty Wasila ta ce,
"Maybe angon ne ake jin kunyarmu".

Ita dai ba ta tanka su ba har wayar ta katse.

Yau ji ta ke ba wanda ta ke jin nauyi duk duniya irin Uwais.

Aunty Wasila ta ce, "Amrah a haka za ki kama mijin?

Yo yanzu wa yake kunyar amsa wayar mijinsa a ko ina?

Zauna nan kina fulako, matan waje su kwace, wannan mijin naki wanke hannu ka taba".

Duk aka yi dariya har make up artist din dake yi mata kwalliya.

Still Amrah ta kasa daga wayar Uwais duk da sai kira yake har sau uku.

Daga karshe ya turo text.

Shi ma sai da ta saci idon su Aunty Murja sannan ta karanta.

"Finally Mrs.

Shagari.

May this moment mark the beginning of the series of our blessings...

May Allah's rahma cover us forever.

I promised you eternal love Amrah and all the happiness that love can bring...

I love you Amrah!"
Uwais Shagari.

Amrah ta yi catching numfashinta a hankali tana satar kallon yayyanta ko da wanda ya gane yadda sakon Uwais ya tafiyar da numfashinta na wucin gadi?

Dukkansu hankalinsu ba ya kanta yana kan hirar dinner da za a yi yau da daddare.

Ta yi ajiyar zuciya tana tunanin da idanun da za ta iya kara duban Uwais a sabon matsayinsa na miji a gare ta.

Amrah na son Uwais, amma soyayyar Uwais ta fi ta Amrah yawa.

Probably za ta iya ci gaba da rayuwarta normally ko babu Uwais ko da akwai shi.

Yayin da Uwais zazzafar soyayya yake yi wa Amrah ta yadda rayuwarsa ba za ta taba cika babu Amrah ba.

A can gidan Ammi yau ne wuni, don haka duk abokan arzikin Ammi sun zo, ciki har da Hajiya Asabe shugabar gidan marayu.

Hajiya Asabe ta kwance jakarta ta soma fiddo 'yan kulle-kullen da ta zo da su tana yi wa Ammi bayani, kasancewar 'yar Sokoto ce ita, ta ce ita ga gudunmawarta kenan kayan gyaran amarya.

Ammi ta karba ne kawai ta yi godiya, amma ta saka a ranta ba za ta bai wa Fahima komai ta ci ba.

Matar da hankalin mijin ba ya kanta sam-sam za'a bai wa maganin mata ya sa ta ciwon mara a banza.

Fahimah ba ta san ta zama matar Uwais ba, da halin da ta samu kanta a ciki yau, da jin cewa bikin Uwais ake yi da ba ta shige shi ba.

Daga ita sai ubangijinta suka san cewa tana gab da zarewa.

Wani dan karamin zaucewa ne ya same ta a daki sai safa da marwa ta ke a cikin dakinta tana magana ita kadai.

"Yaya Uwais ya yi aure, zai tafi ya barmu...

Matarsa mai sa'a ce...

Ni ba ni da sa'a...

Sai koshin wahala.

In ya tafi gidansa shi ke nan na daina ganinsa...

Ganinsa kawai is a blessing because it heals...

Allah ka ba ni juriya, Allah ka ba ni dangana.

Allah ka fahimtar da zuciyata ta daina son abin da ba za ta taba samu ba...".

Sai ji ta yi ana bubbuga mata kofa da karfi.

Muryar Ammi ce ke kiran sunanta, "Fahimah!

Fahimah!

Fito ku yi sallama da su Kawu Shuraim za su tashi yanzu zuwa Sudan".

Ta soma kokarin regaining consciousness dinta don tabbas Ammi ta ganta a wannan halin ba abin da zai hana ta gano ta...

Ta zama zararriya a kan dan ta Uwais, kishinsa na neman hallaka ta.

Toilet ta fada da gudu ta wanke fuskarta da sabulu ta sanya hijab sannan ta fito, ta bi bayan Ammi zuwa falo.

Duka kawunnin Uwais suka bi ta da kallo har ta samu gefen Ammi ta zauna.
Chapter 14 · 0% Book details