← Book details Fahimah Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 35

Sashe 34

Fahimah Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna zuwa gida ta zuro kafar ta daya waje tana kokarin fitowa daga motar, sai ta juyo ta ce da shi,
o amma fa Habib Qalby, ba za mu hada daki ba, wallahi ko kadan yanzu bana son turaren ka
Cikin mamaki yake dubanta baki a sake.
mrah lafiyarki kalau kuwa?
umul kalau nake
o kam, ai sai dai in canza kayan, amma abin da ki ke fadi ke ma kin san ba mai yiyuwa ba ne
Amrah kamar ta saka kuka, ta ce,
allahi ko ka cire ba ka daina kamshin (Maison Francis)
Ya ce,
i kuwa sai dai a yi wacce za a yi, amma ban da wannan yaren
Sun yi shirin kwanciya, zullumi da damuwa duk sun ishi Amrah, ba da wasa ta ke ba turarensa hawa kanta yake, a baya babu kamshin da ta ke so irin na Uwais amma banda yanzu.

Uwais na sanya tafukansa a bayan wuyanta ya hada goshinsu zai lallashe ta don ya ji actual abin da ke damunta ta ke ta wannan yamutse-yamutsen fuskar.

Ai kuwa ta kelayo masa wani uban amai, mai karni.

Ya yi maza ya ja baya ita kuma ta ci gaba da amayar da spicy chicken din da ta ci tas!

Sai da ta amayar da ita.

A daren ya ce su tafi asibiti, ita kuma ta dage ba ta zuwa ko
na.

Ai ta gaya masa turarensa ne ba ta so ya ki jin magana.

Ya ki ya bar mata dakin.

Washegari sai da ya yi mata jan ido sannan ta yarda suka tafi asibitin standard.

Awo na fitsari a tashin farko ya nuna ciki na watanni uku.

Tunda suka dauko hanyar dawowa Amrah ke kuka, kuka kashirban.

Kamar ba ita bace a baya ta ce ta yi surrender ba.

Bata taba tsammatarwa kanta ciki a wannan lokacin ba.

Ta rantse ba ta shirya wa haihuwa yanzu ba, karatunta zai salwanta.

Uwais sabida tsananin bacin rai ga kalaman Amrah a kan kyautar da Allah ya yi masa cewa ya yi,
allahi in ki ka zubda cikin nan da gangan, to a bakin aurenki
Amrah ta zaro ido tana kallon Uwais, kallon mamaki da tsoro, ina soyayyar da yake ikirarin yana yi mata?

Yanzu har ya fi son dan da zai haifa a kanta?

Da ma Daddy ya ce soyayya karya ce, ka yi aure kawai don bukatarka ta dan Adam da cika sunnar Annabi, amma ba don soyayya ba, sabida it never exist in nowadays men, even if it exists da zarar sun gano wata za ta yi fading.

Shin Daddy da gaske yake?

Ko dai Uwais ya gano watan ne shi ya sa komai nata ke fading a idanunsa???

Ba za ta yi mamakin kowacce barazana daga gare shi ba, don ya nuna yana son cikinsa.

Amma barazana da igiyar aurenta abin ya ba ta mamaki da tsoro sosai, ya kuma kara sagar mata da gwiwa akan canje-canjen data ta gani daga gare shi.

Tunda suka dawo kuwa ta raba daki da shi, shi ma bai kara takura mata ba.

Yanzu lallabawa zai yi ta haife masa dansa ko
arsa lafiya ya daina neman komai a wurinta.

All thanks to AMMI yana da precious gem dinsa a gefe, a virtous wife who her pri
e is far above rubies wadda sai yadda ya ga damar sarrafa ta (na
ve and innocent FAH-HIMAH SHAGARI).

Yau da bai san ina zai sa kansa ba da wannan takunkumin na Amrah.

Wuni guda Amrah ba ta kulla komai a gidan ba, ga shi duk ya yi kura, kasancewar an kwana biyu ba'a ciki, tunda suka zo sai abincin sayarwa yake ta faman sayo musu.

Har ya fara gajiya da daukan mota yana fita yana dawowa.

Ita da kanta dattin gidan ya ishe ta, ta fito ta same shi a falo yana kallon ball da kungiyar da yake so Arsenal, yana shan wankakken inabi da ke kan tebirin gabansa.

Daga can nesa da shi ta tsaya tana toshe hanci.
abiby, ina wannan yarinyar ta gidanku?

Ya kalle ta cikin takaicin yadda ta ke toshe masa hanci kamar wani mushe, ya ce,
"Wace yarinya?

Mu gidanmu da yarinya ne?

Ta ce,
annan budurwar nake nufi, baka, mai kyau haka, mai jan class din nan
Gaban Uwais ne ya bada wani irin damm!

Ya bude ido kawai yana kallon ta.

Ta ce,
on Allah don Annabi ka je ka dauko min ita ta taimaka min in kintsa gidan nan, ta yi min miya ko ta sati daya ce in sa a firji don wallahi ba ni son warin albasa
Uwais ji ya yi tamkar Amrah ta yi masa gafara, zaman nan da ya yi yana shan inab tunaninta yake yi, ba ya son Amrah ta samu wani clue ne kasancewar Fahimah matar sa a yanzu, musamman cikin halin nan da ta ke ciki komai zai iya faruwa.

Ya yi niyyar gaya mata gaskiya tun kafin ya baro gidan Ammi, amma sai ga bayyanar maganar cikin, don haka ya fasa sai cikinta ya yi kwari.

Ta yadda ko me ye zai biyo baya ba zai shafi lafiyar babynsa ba.

Amma anya Fahimah za ta yarda ta zo gidansa?

Kuma in ya yi hakan ya yi wa Ammi da ita kanta Fahimar daidai duk da Amrah taimako ta nema?

Amma Amrah ta kafa naci, ta kasa ta tsare ita lallai ya je ya zo mata da mai aikin Ammi.

Da ya rasa yadda zai mata bayani, sai ya fiddo wayarsa ya binciko lambar Ammi ta kasar Sudan ya kira.

Wayar na shiga ya mika mata,
ngo nemi iznin Ammi da kanki
Tana karba ta yi sallama,
alamu alaikum, Ammi ni ce Amrah
Ammi ta ce,
araba da mutanen Malaysia, ya ya karatun?
mmi na samu mid-term break na sati biyu shi ne kawai na taho Kano.

Amma Ammi ba ni da lafiya, ba na iya aikin gida da girki, shi ne na roke shi ya dauko min aron yarinyar wajenki kafin ki dawo, lokacin ne nima zan koma makaranta, tunda ita ma cikin kadaici ta ke, sai mu zauna tare ta taimaka mun har ki dawo, sai ya ce wai sai dai in tambaye ki da kaina.

Don Allah Ammi a yi min alfarma
Ammi ta yi jimmmm!

Kafin ta ce,
abu laifi, zan masa magana ya dauko ta ya kawo miki, amma ku bari in fara magana da ita tukunna in nemi amincewar ta.

Don Fahimah ba wai ta saba da shiga mutane ba ne
Amrah ta ce,
i roka min ita Ammi, ki gaya mata I
not boring, ba zan dinga damunta ba sam, hira in ba tana so ba ba za mu yi ba, ni ma ba dadi nake ji ba kullum ina daki, sabida warin komai sai in ji shi ba daidai ba
Ammi ta yi murmushi, ta ce,
hankali komai zai dawo daidai, zan lallashi Fahimah ta zauna da ku din har in dawo
A zuciyarta kuma addu
ta yi, Allah ya bai wa Fahimah nata rabon itama cikin gaggawa.

Ta rasa dalilinsa na kin gaya wa Amrah gaskiya cewa Fahimah kishiyar ta ce, amma ta san Uwais sarai ta san halayensa, ko me yake yi yana sane, kuma sai ya tabbata yana da hujja.

Kafin ta kira Fahimah sai da ta fara kiran Uwais a lokacin da ta tabbatar yana office.

Ta ce,
wais me zai hana ka gaya mata gaskiya in ya so Fahimah ta tare gabadaya su yi zaman mai dalili?

Ni bana son abu na rashin gaskiya ko kankani, kada nan gaba ta gane ta ce mun yaudare ta".

Uwais ya ce,
mmi ki rabu da Amrah kawai, zan gaya mata amma ba yanzu ba, don ba son cikin jikinta ta ke ba.

Idan na gaya mata yanzu komai zai iya faruwa.

Za ta iya yin komai don ta huce wanda zai kare ne a kan cikin nan, don hakan sai nan da watanni hudu a gaba zan gaya mata.

Lokacin na gama yi wa Fahimah gininta.

Ita kuma cikin ya kusa isa haihuwa.

Don yanzu na aza harsashin ginin
Ammi ta fahimce shi, as she has no option, ta ce,
o Allah ya kade fitina ya hada hankulansu in ka tashi sai ka biya ka tafi mata da Fahimar zan kira ta yanzu in mata bayani".

Fahimah ta fito wanka kenan tana shafa a gaban mudubi kiran Ammi ya shigo mata.

Ta mika hannu ta daga da sallama, Ammi ta ce,
a ya na ji muryarki so pale?

Are you alright?

Fahimah ta ce,
afiya nake Ammi, barci ne bai ishe ni ba
Ammi ta ce,
o ki kwanta zuwa lokacin tashin Uwais zai zo ku tafi gidansa.

Amrah ta roke ni kan ba ta da lafiya ki je ku zauna tare kafin na dawo.

Ki sa a ranki Amrah ba kishiya ba ce a gare ki, kanwa ce.

Ko babu aure tsakaninki da Uwais in tana cikin lalura hakkinmu ne mu taimaka mata tunda iyayenta ba a gari suke ba
Fahimah ta ji kanta ya yi wani irin gingiringim.

Idan kuma Uwais ya bada wata kafa da Amrah za ta fahimci something in between a tsakaninsu fa?

Tunda daga shi har Ammi ba su shirya bayyana matsayinta ga Amrah ba?

A kan dalilinsu da ba za ta ce mene ne shi ba?

Amma matsayin Ammi ya wuce ta yi umarni ta saba, ko da bai yi daidai da son ranta ba.

Ammi ba ta yi haka don ta kaskantata ba, sai don ta zamo uwa mai adalci ga kowa (zuciyarta ta tunasar).

Sai kawai ta mike ta hau shiri, tana addu
a cikin ranta, Allah ya ba ta juriya a zama da Amrah da zata je ta yi, ya rage mata kishinta da ke damun ranta.

Sanda Uwais ya shigo gidan a falo ya tadda ita jingine jikin jakar kayanta da ta hada.

Ya tafi gaba-gadi da sassarfa ya yi mata wata kyakkyawar runguma tamkar ya tsaga kirjinsa ya sanya ta.

Ya yi kewarta yadda harshensa ba zai iya bayyanawa ba.

Sai ya shiga nuna mata practically yadda ya yi kewan nata har abin ya bai wa Fahimah mamaki da tsoro.
Chapter 34 · 0% Book details