← Book details Fahimah Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 35

Sashe 1

Fahimah Complete Hausa Novel · about 8 min read

Root Entry
WordDocument
0Table
Data
: SHIMFIDA
Misalin karfe ukku na yammacin ranar, wadda ta kasance Talata, cikin wata Unguwa a jihar Kano da ake kira ''Yankaba, Hajiya SAFIYYAH-BASUDANIYYAH (kamar yadda kowa da ya santa yake kuma alaqa da ita ke kiranta), na zaune bisa Kilishin tsakiyar falon ta, carbi ne dan madina a hannun ta tana ja, lokaci zuwa lokaci tana mai daga kanta zuwa ga tankareren agogon bango dake manne a fuskar gabas maso kudu na falon nata.

Ga dukkan alamu akwai abinda take dakon jira, shiyasa tun da ta yi sallahr azuhur bata tashi a gurin ba take yawan kai idanun ta ga agogon bangon.

Kayataccen falo ne ne da ya ji kayan alatu na zamani wanda kallo daya zaka yi masa ka tabbatar masu gidan suna cikin wadatar rayuwa, daular duniya ta gama zaunawa dai-dai misali da burin kowanne dan adam.

Komai dake falon kalarsa ruwan madara ne da ratsin ruwan goro (orange) wanda hakan ya maida falon kalar unique don kala ce da ba'a faya amfani da ita ba wajen tsara falukan zamani.

Tun Haj.

Safeeyah bata damuwa, amma da ta ga yadda lokaci ya ja sai damuwa ta fara nunawa akan kyakkyawar Basudaniyar fuskar ta.

Me ya tsayar da FAHIMAH a makaranta har yanzu da ake neman karfe uku na rana???

Sallamar mai aikin ta Talatu ya katse mata tunani, ta shigo dauke da butar Shayi irin ta larabawan SUDAN da 'yan kananan kofunan tangaran na shan shayin Sudanai, kai tsaye ta nufo inda uwargijiyar ta ke zaune ta russuna daga gefe ta ajiye, ga dukkan alamu abu ne da ya zamewa Hajiyar al'ada wato shan shayin akai-akai.

Talatu tace, tana duban Hajiyar.

"Hajiya mutuniyata ko lafiya?

Tun dazu nake duban hanyar ta har yanzu shiru, ko ta ce miki zata biya wani waje ne yau?"
Hajiya Safeeyah ta kai karshe a carbin da ta ke ja, tayi addua suka shafa tare da Talatu, sannan ta ce.

"Tunanin da nake ta yi tun dazu kenan, karfe daya da rabi yau tace min zata dawo, bari in kira wayar ta mu ji ko lafiya, don Fahimah bata zuwa wani waje ba tare da ta gaya min na mata izni ba".

Ta dauki wayar dake gefenta ta lalubo lambar Fahimah ta kira ta kara a kunnen ta, amma har tayi ta katse mai wayar bata amsa ba.

Which was very unusual of her (kin daga waya).

Wanda hakan ya kara dugunzuma zukatan Hajiya da Talatu.

Daidai lokacin da ya shigo falon yana balle 'links' din hannun farar rigar shi, gabadaya falon ya dauki kamshin sassanyan turarensa "Maison Francis (Kurkdjian, Paris)".

Farar shaddah ce kal a jikin shi mai santsi da ake kira (London King) da farar hular Zanna mahadin shaddar jikin shi.

Dogo ne, mai fadin kirji (physique chest) amma hakan bai hana ka kira shi siriri, don tsayi har ya rankwafa, kallo daya zaka yi mishi ka tabbatar ba cikakken bahaushe bane; ko dai ruwa-biyu (half-caste) ko kuma cikakken Ba-sudane.

Sudanan ma irin fararen Sudanai ba bakaken cikin su ba, hancinsa don tsayi har lankwasawa yayi kadan, hular kansa ta nitse tsaf a cikin tarin sumar kansa wadda ta kara fallasa jinsin da ya fito daga cikin sa.

Ga dukkan alamu cikin sauri ya ke, sauri mai yawa, ya dubi mahaifiyar sa dake zaune nannade cikin laffaya shudiya da carbi a hannun ta, bai taba ganin ta da wata suttura ba ta Sudanese ba, Talatu na duke gabanta tana firfita mata shayi, yayi dan russunawa daga tsaye cikin tarin ladabi ga mahaifiyar sa...

"Ammi zan fita, zan koma office, don bamu tashi ba na dawo, amma bazan wuce karfe biyar na yamma ba yau zan dawo, insha Allah.

Na baro wasu ayyuka da ban karasa ba nake so inje in karasa, don gobe da safe managern Gyadi-gyadi Branch zai karbe su daga ofis dina".

Bai kuma jira cewar mahaifiyar tasa ba ya doshi kofa, ko abincin ranar da aka shirya masa bisa makeken tebir din falon bai kalla ba.

"Uwais!"
Muryar mahaifiyar tasa ta dakatar da shi.

Ba tare da ya juyo ba ya dakata a kagare.

Ta ce, Fahima ba ta dawo ba tun fitarta makaranta.

Annurin da ke fuskarsa nan da nan ya gushe.

Gabadaya ya juyo fuskarsa a gintse, For Allah sake.

Ammi ni ina ruwana?

Is she a kid?

Ko kuwa ba ta san hanya ba?

Hajiya Safiyya ta girgiza kai tana iya karantar tsanar maganar yarinyar da ta yi masa baro-baro a kan kykkyawar fuskarsa.

To amma dole ta gaya masa sabida yadda kasar tamu ta koma daukan dan mutum ya zama kamar na kiyashi.

Babu kuma wani namiji a gidan bayan shi, shi ne ubansu har ita da ta ke mahaifiyarsa.

Duk uzurin da ka ke da shi ka ajiye ka bi bayanta, ko in tashi ni da kaina in bi ta.

A matukar fusace ya sa kai ya fita daga falon ba tare da ya ce komai ba.

Daga yadda yake tukin motar kadai za ka fahimci ransa a bace yake, don dai fuskar sa ta kasance mai boye bacin rai ne, ko kadan ba abin da ya tsana a duniya irin Ammi ta hada sha'anin sa da na Fahimah.

Ta ki yarda ta gane har yau shi zuciyarsa ba ta son Faheemah, kuma har abada ba za ta so ta ba!

Ba don komai ba sai don ASALINTA....

Da wasu specific dalilan da suka dade da samun muhalli a ransa tun suna yara shi da Fahimar, muhimmi shi ne son da Ammin sa ke mata, wanda yake ittikafin da kyar in bai zarce wanda take masa shi da ta haifa ba.

Shi kuma tun asali mutum ne mai kishi akan abinda yake so, musamman Amminsa, wanda kishin nasa akan ta ne ya hanata sake aure har yau.

A daidai lokacin ya karya kan motarsa ya shiga makarantar YAN DUTSE COLLEGE, bayan maigadi ya bude masa kofar makarantar, abin haushi yana shigowa ita ya fara hangowa tun daga nesa suna tafe ita da kawarta Majida suna hira, sai dariya ta ke ba abinda ya dameta.

Ta baro masa uwa cikin taraddadi don bata san zafinta ba.

Her elegant black skin sai sheki ta ke cikin hasken ranar, babu wani abu mai haske a jikinta kamar fararen idanunta da jerarrun hakoranta.

She's dark-skinned yet beautiful.

Wasu irin idanuwa masu sparkling cikin idanun duk mai dubanta.

Cikakken gashin girar da ya kusa hadewa da dan uwansa yana daga cikin abin da ya bambanta ta da sauran mata yan uwanta.

Uwais dauke kai ya yi yana sakin tsaki, tare da danna musu gigitaccen horn mai karfi don kamar ba su lura da tsayuwar shi ba.

A ransa cewa ya ke, ko uban me suka zauna yi a makarantar har yanzu oho!

Kwata-kwata su da suka rage cikin makarantar ba su fi a kirga da yatsun hannu ba.

Ta dago kai da sauri ta dubi inda horn din motar ya fito.

Mutum na karshe da ba ta taba tsammanin gani a makarantarsu ba, da sunan dai ya zo daukanta.

A gurguje ta yi sallama da kawar tata ta nufo inda yake kafafunta har hardewa suke don sauri da fargaba.

Ba yau ta fara ganin wannan moody expression din a kan kyakkyawar fuskarsa ba in dai a kanta ne, don haka inda sabo Fahimah ta saba.

Ta bude kofar gefensa ta shiga, ya tada motar a guje ya bar makarantar ba tare da ya dube ta ba.

Maimakon ya dau hanyar gidansu kamar yadda ta yi tsammani, sai gani ta yi sun dau hanyar Bank Road, ita dai ba ta ce komai ba, amma ganin sun yi parking a wani branch bankin GT ta fahimci inda suka zo din, wajen aikinsa ne.

Ya bude kofarsa tare da daukar jakar loptop dinsa da wayoyinsa ya yi shigewarsa.

Duk inda ya gifta sai maaikata yan uwansa sun kula shi sun gaishe shi, amma hannu kawai Uwais yake daga musu ya wuce, kowa ya saba da rashin walwalarsa shi ya sa shan kamshinsa ba ya damun kowa don farin jini gare shi ba na wasa ba, wanda kyawun surarsa ke sayo masa.

Yana kokarin zama a kujerar ofishinsa wanda ke zagaye cikin raw gilashi, kowa da ke wajen yana iya hango shi daga waje, wayar Ammi ta shigo, yana jan kujerarshi zai zauna ya amsa mata.

Muna tare.

Kawai ya ce tare da ajiye wayar bisa makeken tebirinsa baki wuluk mai sheki.

Ammi hankalinta ya kwanta tunda ya ce yana tare da Fahimar.

Kai ba za ka ce ya ajiye mutum cikin mota ba, ya kunna kwamfutar kan tebirinsa ya durfafi ayyukan da ke gabansa cikin kwarewa da sanin makamar aikin sa, wadanda da ma su ya dawo don yayi.

Ya manta da wata da wata mutum dan adam da ya ajiye a cikin mota, ba tare da ko ya sauke mata gilashi don ta sha iska ba.

A can kuma Faheema tun tana duba siririn agogon da ke daure a hannunta har ta kwantar da kanta a kan dash board din motar, ta sauke gilassan da ya rufe iska ta soma ratsa ta, wata irin yunwa na sakadarta.

Rabonta da abinci tun karin kumallon safe da Ammi ta takura mata ta yi, ta san halin Uwais sarai, duk yadda aka yi Ammi ce ta takura masa ya bi sawunta shi ya sa ya zo ya shanya ta a harabar ofishinsu.

Ba kowa ya ja mata ba sai Mr.

Edward malaminsu na Biology, shi ne ya zaunar da su yin practical na darasin da yake daukarsu bayan normal school hours kasancewar nan da watanni uku za su zana jarrabawar barin makarantar sakandire gabadaya.

Ammi ta san Uwais ba ya son hada hanya da ita don me za ta sa shi ya biyo bayanta?!

Allah sarki Fahimah!

Tun tana sauraron kidan da akuyar cikinta ke yi, har ta koma ta kwantar da kanta jikin kujerar motar, wani wahalallen barci ya yi awon gaba da ita.

Sai karfe biyar na yamma ya kammala duk abin da yake yi a bankin, ya tattaro wayoyinsa da kwamfutarsa ya fito.

Sai da ya tunkaro motar sannan ya tuna da ita, ya bude gidan baya ya zuba shirginsa sannan ya shiga mazauninsa ya zauna.
Chapter 1 · 0% Book details