← Book details Exile Princess Love And Power Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 44

Sashe 7

Exile Princess Love And Power Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya na ganin ta dago kan ta ya kai hannayan shi biyu ya rike kunnuwan shi ya dan sunkuyar da kai allamun ya na bata hakuri

Wata yar karamar dariya ta yi cikin kukan nata sai da dan dimple din ta na geffen dama ya banyana karan farko kenan da na gan shi kuma gashi ba karamin kyau ya na kara mata ba

A hankali ya dago kan shi ya na kallon ta ta cikin glass din shi, abun har dariya ya so ya bashi yadda ta ke dariya ta na kuka lokaci guda

" Shikenan auta ya wuce ko ? " malam ya fada ya na kai hannun shi ya goge mata hawayen ta

Jinjina mishi kai ta kafin ta kai hannun ta bayan kanta ta ce " Abba wajen zafi ya ke min " ta kai karshen cikin shagwaba

Dan murmushi malam ya yi kafin ya ce " babu komai auta na zai wuce tashi ki je daki, ki konta "

Da to ta amsa mishi sannan ta fara kokarin mike wa da ga jikin shi

Da sauri Nesrine da ke tsaye waje guda tun dazu ta na kallon su , ta karaso wajen ta kamosu hannun ta guda ta taimaka mata ta mike tsaye su ka nufi cikin daki

Su na shiga cikin dakin Inaya ta Haye saman gadon ta yi rub da ciki ta na sauke nunfashi a hankali ta lumshe idanun ta

Ita kuma Nesrine ta juya ta baro dakin ta tafi kitchen

Ta na shiga malam ya kali Zayd ya ce " Zayd me ya sa ba ka taro ta ba, yanzu da ta ji ciwo fa, dama ta na da tabo a kan ta na dauke shi ne ya motsa yadda na ga ta na kukan nan "

Kallon shi Zayd ya yi cikin sanyi murya ya ce " sorry uncle , amma wane tabo ne wannan ? " ya tambaya ya na son ya ji karin bayani

Ya na shirin magana Abdoul ya fito da ga dakin shi ya na sanye da jallabiya brown mai dogayen hannu ya zo geffen su ya zauna ya na musu sallama

A tare su ka amsa sallamar amma ta Abba kadai a ka ji , dan Zayd in ba kallon bakin shi ka yi ba baza ka gane ya amsa ba

Sai da ya zauna sannan ya ce "malam, na ji wani ya yi kara, cikin gidan nan ne ? "

Dan murmushi malam ya yi kafin ya ce " ba komai, auta ce ta dan fadi amma ba ta ji ciwo ba "

Jinjina kan shi kawai Abdoul ya yi ba tare da ya ce komai

Su na a haka Nesrine ta fito da ga kitchen ta na rike da plate ta shiga dakin su

Ta na shiga mama ta fito da ga kitchen din ta na rike da tray madaidaici ta karaso wajen su malam ta yi musu sallama ta ajiye tray din gaban su , sannan ta koma kitchen ta dauko musu jug na ruwa da glass biyu ta ka ta ajiye musu sannan ta wuce dakin ta

Ta na shiga dakin Abdoul ya bude musu tray din ya mika ma kowane spoon guda sannan ya ce musu bismillah

Kamar yadda su ka saba haka wannan karan ma haka su ka ci
Sai da su ka Kamala ba wanda ya ce ma wani ufan

Ya na tsaka da shan ruwa Inaya ta fito da ga dakin su ta na dafe kai da hannu guda ta na dan lumshe idanu kamar mai jin barci

A tare duka su ka dago kai su na kallon ta ba wanda ya ce da ita komai

Ta na tsaka da tafiyar ta ta ji wani jiri ya debe ta yi fuuuuu baya ta tafi za ta fadi

Da sauri Abdoul ya yi kokarin tashi dan ya taro ta amma sai dai mi ?

Tun kafin ya mike ya ga Zayd ya mike a dubu dari ya nufe ta , taku biyu kawai ya yi ya riko hannun ta ya janyo ta, ta fado saman fafadar kirjin shi

Baki sake Abdoul da malam ke kallon shi sannan su juyo su kali juna su na son su yi magana amma baki ya ki buduwa

Basu Ankara ba sai kawai ganin su ka ya dauke ta cak ya komo inda ya tashi ya kontar da ita, sannan ya kai hannu ya dauki glass din ruwa ya zuba kadan ya yarfa mata a fuska

A hankali ta ware idanun ta ta na karanto kalmar shahada

Ajiyar zuciya malam ya sauke ya na lumshe idanun shi a hankali sannan ya bude ya kali Abdoul ya ce " Abdoul meda ta dakin su "

Da to ya amsa mishi sannan ya mike tsaye ya kai hannu ya dauke ta cak kamar baby ya nufi bedroom din su da ita

Ya na barin wajen malam ya kali Zayd ya ce " Zayd na san kai ba kurma ba ne amma yau abun da na gani makaho bazai iya yin haka "

Shiru Zayd ya yi ya na sauraron shi amma ya kassa bude baki ya yi magana

Dafa kafadar shi malam ya yi kafin ya ce " Zayd ni fa na yarda da kai, dalilin da ya sa na aura maka Inaya nassan ka na da kyakyawar zuciya amma ban San assalin ka ba kuma bazan ce ka fada min har sai randa ka yi ninya amma zan so in sani meyassa ka ke karyar wadanan nakassa al'halin ka na cikin koshin lafya ? "

Malam na gama fadar haka Abdoul ya fito da ga cikin dakin su Inaya ya dawo inda ya tashi ya zauna

Ya na zama Zayd ya ce " Ni ban taba ce muku ni kurma ne ko kuma makaho ku ne ku ka yi hassashen ku a haka "

Dan zaro idanu malam ya yi dan fa maganar Zayd ba karya ba ce dan tun lokacin da su ka shigo garin kano su ka hadu da Zayd kullum shiru da shi ko an mishi magana sai dai ya girgiza kai ko ya jingina da haka har su ka yi tunanin ko shi kurma ne , gashi kullum ya na sanye da bakin glass wani lokaci ya na rike da sanda kamar makaho dalilin da ya sa su ke tunanin shi kurma ne kuma makaho

Kallon shi da kyau Abdoul ya yi kafin ya ce " Zayd ka na nufin yanzu ka na iya gani na "

Sai da ya dauki lokaci kafin ya ce " of cours ina iya ganin ka, ka na sanye da jallabiya brown mai dogayen hannu , ni fa ba ni son yawwan magana dan Allah ku daina saka ni dole sai na bude baki na yi magana zan iya fadar abun da zai bata muku baki daya " ya fada kai a sunkuye

Jinjina kan shi Abdoul ya yi kafin ya ce " don Allah Zayd zan so na ga idanun ka ko da so guda ne ka ga yanzu four years kullum ina ganin ka da glass wannan karan na so na gan su "

Dago kan shi ya yi a hankali ya na kallon Abdoul ta cikin glass din shi kafin ya sa hannu a hankali ya zame glass din shi

A tare zuciyar malam da Abdoul su ka buga da su ka ci karo da wadanan hazel eyes na Zayd ga shi ko ya na fuskantar lamps din wajen sai idanun shi su ka yi reflecting hasken lamps din sai su ka yi wani kyali na musaman su ka zama kamar idanun mage

Da sauri Abdoul ya ce " don Allah meda glass din ka wlh sai da na ji tsoro "

A hankali ya sunkuyar da kai ya Meda glass din shi sannan ya dago kai ya kali Abdoul ya ce " yanzu dai baza ka ce ba ka taba ganin idanu na ba "

" ni ko na gan so , ai wadanan ko a mafarki na gan su sai na gane su " ya kai karshen ya na yar karamar dariya

Malam dai ya yi sumar zaune ya rasa wane irin mutun ne Zayd , sam bai yi kama da mutanan Nigeria ba karewar zancen bai ma yi kama da mutanan Africa ba ki daya

Haka su ka ci gaba da hirar su wadda yawancin Abdoul da malam ke yin ta shi Zayd ya na zaune kamar gunki
Sai wajen karfe 10 na dare sannan ya mike zai koma gida, Abdoul ya dan raka shi kadan kafin ya komawar shi gida

Bayan ya koma gida bai tsaya bin ta kan Moussa ba kai tsaye ya wuce bedroom din shi

❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥

( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )

STORY & WRITTEN BY : ANISH

Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

PAGE 5 ❤🔥

Washe gari
Yau ta kama week-end ce Inaya da Nesrine ba su tafi college ba, sai misalin karfe 9 na safe Nesrine ta farka da ga barci

Inaya kuma sai wajen karfe 10 ta farka , ko da ta farka ta ji kan ta na yi mata dan ciwo amma sai ta jure

Ta mike ta fito dakin ta shiga toilet ta yi wanka sannan ta fito ta shirya cikin wando jeans baki da doguwar riga zuwa guyiwa pink colour ta saka dan karamin hijab zuwa kirji sai tashin kamshi ta ke

Kai tsaye kitchen ta nufa dan ta taya mama girki tun da yau week-end

A tare su ka yi dafuwar su cikin konciyar hankali har misalin karfe 12 na safe sannan su ka Kamala

Bayan sun ida Inaya na shirin shiga dakin ta ta tsinci Muryar malam ya na fadin " Auta dan Allah dauki abincin Zayd ki kai mishi " ya fada ya na ida shigowa cikin gidan

Dan murmushi ta yi sannan ta ce mishi to ta juya ta koma kitchen
Dama mama ta fida mishi na shi cikin wani kwano ta ajiye gefe dama sun saba fida mishi abincin rana kullum wani yaro da ke sangayar malam ke zowa ya kai mishi wannan karan ne na farko da za ta kai mishi da kan ta
Chapter 7 · 0% Book details