← Book details Exile Princess Love And Power Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 44

Sashe 38

Exile Princess Love And Power Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hannayan shi ya kai saman kafadun ta , ya dago ta ya na kallon face din ta ya ce " ki daina cewa haka mana , ba ga ni ba "

Tsit ta tsaya da kukan nata ta dago kai ta na kallon shi cikin ido , duk sai ta nemi kukan ta ta rasa kawai sai kallon shi ta ke yi cikin ido

Ganin ta yi shiru ya sa shi sakin dan karamin murmushi ya na daga mata gera guda ya ce " to na mine ki na yi min irin wannan kallo kuma , ko na fadi ba dai'dai ba ? "

Girgiza mishi kai kawai ta yi ba tare da ta janye idanun ta da ga cikin nashi ba

" okay , yanzu tashi ki je lokacin sallat ya yi " ya kai karshen ya na janye hannayan shi da ga saman kafadun ta
Sannan ya juya ya na kokarin sauka da ga saman gadon
Ya koma bakin gadon ya yi tsaye ya na kallon ta fuska dauke da murmushi

Ita dai ta tsaya ta na kallon shi ta rasa dalili

Daga mata gera guda ya yi ya na fadin " ko sai na taimaka miki ? "

Da sauri ta girgiza mishi kai ta sauko da ga saman gadon , a hankali ta fara takawa ta na jan kafa ta na rumtse idanun ta dan fa har yanzu zafi wajen ke yi mata

Da kallo ya rakata har sai da ta shiga toilet sannan ya saki wani cool murmushi ya sa kafa shi ma ya bar dakin

Bayan sallar isha

Zayd

Zaune ya ke cikin harabar gidan saman wasu chair irin na shan iska , ya daga kan shi sama ya na kallon stars

Ya na zaune a hakan Moussa ya karaso wajen ya na yi mishi sannan sannan ya zauna saman daya chair din da ke fuskantar ta Zayd

Cen kassan makoshi Zayd ya amsa mishi sallamar shi ba tare da ya sauko da kai ba

Hannu Moussa ya kai ya bugi cinyar Zayd ya na fadin " kai dan Allah malam sauko da kan ka , kar ya yi maka ciwo "

Ko sauraron shi ma Zayd ba ya yi ga Dukan allamu ya yi nisa cikin tunanin shi

Murmushi Moussa ya yi ya na fadin " tunanin mi ka ke yi haka ne Amir ? "

Sai da ya dauki dan lokaci kafin ya ce " Diya , ina ji a jiki na wani mumunan abu na shirin faruwa da ni "

Da sauri Moussa ya katse shi da cewa " kontar da hankalin ka ba abun da zai faru da kai da yardar Allah "

Lumshe idanun shi Zayd ya yi kafin ya ce " zan iya yi maka wata magana , please be serious "

Gyara zaman shi Moussa ya yi kafin ya ce " ina jin ka mai martaba " ya fada dan yau ya ga allamun na mulkin ke sama

Jinkirtawa Zayd ya yi kafin ya ce " ka na ganin zan iya komawa gida da wannan yarinyar "

" me zai hana ran ka ya dade , na ga ai matar ka ce ta sunna dole ne ka tafi da ita , ta ga ahalin ka , su ma su ga sirikar su "

" but ba na tunanin uncle zai yarda , it's not sure idan na je za su yarda su karbe ta a matsayin gimbiya , she is so small "

" ran ka shi dade idan har kai ka karbe ta a matsayin matar ka , dole za su karbe ta "

Dan tsaki Zayd ya yi ya na bude idanun shi ya sauko da kan shi ya na kallon Moussa ya ce " please Diya , ni fa yanzu friend di na , na ke bukata , kai daina cewa ranka shi dade , i don't like that "

Murmushi Moussa ya yi ya na kallon abokin nashi ya ce " Amir na san ba wannan maganar ka ke son yi min ba , ka fi kowa sani , idan har ka koma Daular saudiya da ita ka ce matar ka ce , babu wanda ya isa ya ce a'a har shi Malik , kamar yadda ka ce friend's din ka ka ke bukata , zan yi maka magana a hakan , Nawfel , fada min gaskia ka na son yarinyar nan ko ba ka son ta "

Ajiyar zuciya Zayd ya sauke kafin ya sake daga kan shi ya na kallon sama ya ce " i don't know "

" you lie , ka sani sarai kawai dai har yanzu zuciyar ka ta ki yarda da hakan ne dan har yanzu kallon yarinya ka ke yi mata "

Sauko da kan shi Zayd ya yi ya matse fuska ya ce " Diya ni ka ke cewa karya na ke ? "

Da sauri Moussa ya mike tsaye ya nufi hanyar shiga falon gidan ya na fadin " e na fada karya ka ke "

Da gudu Zayd ya mike ya bi bayan shi da gudu su ka shiga cikin falon gidan

A cikin falon kuma Malam, mama da Abdoul su na zaune su na hira su ka ga Moussa ya shigo da gudu kamar an koro shi

Da sauri malam ya ce " Moussa lafya ka ke wannan gudun "

Bai kai ga rufe bakin shi ba ya ga Zayd shi ma ya shigo da gudu ya bi bayan Moussa su ka Haye stair

Da kallo malam ya bi su ya na sakin dan karamin murmushi ya ce " Allah dai ya shirya tun da haka ne "

Bangaran Zayd kuma , Moussa na Hayewa stair ya nufi part din Zayd

Har ya kai bakin kofar ya tsaya ya juyo , ya na kallon Zayd da ya tunkaro shi da gudu

Zayd na karasowa wajen ya kai hannu zai damko shi

Da sauri Moussa ya gauce gefe , sai ga Inaya tsaye a bayan shi ta sunkuyar da kai ta na gyara hijabin jikin ta

Zaro idanu Zayd ya yi ya na kallon ta , ya na kokarin ya dakatar da kan shi amma ina sai da ya fada mata , su ka yi fuuu baya su ka fadi

Yar siririyar kara ta saki ta na datse idanun ta da karfi

Gumshe dariya Moussa ya yi ya na sa kafa ya bar wajen , dama ya na shirin shiga dakin ya ga Inaya ta fito da ga cikin bedroom kai a sunkuye , kawai sai ya tsaya har ta karaso dan ya yi ma Zayd tarko , kuma ya fada

Ya na barin wajen Zayd ya sa hannayan shi biyu ya mike ya mata runfa da kirjin shi ya na kallon face din ta , har yanzu ta na lumshe idanun ta

Slowly ya bude baki ya ce " Mimi ba ki ji ciwo ba ? "

A hankali ta fara ware idanun ta , sai cikin nashi
Shiru ta yi ta na kallon shi cikin ido babu ko kiftawa ta kassa cewa komai

Daga mata gera guda ya yi ya na fadin " me ki ke kallo ? "

Da sauri ta dawo cikin hayacin ta , ta kauda kai gefe ta ce " ba komai yaya Zayd "

" shikenan to , ai yanzu sai ki tashi ko " ya fada da allamun ya manta shi ne ya hana ta tashi

A hankali ta juyo da kan ta, ta na kallon shi , kassa kassa ta ce " yaya Zayd tashi to "

Daga mata gera guda ya yi ya na fadin " in tafi ina ? "

Dan murmushi ta yi mai sauti kafin ta ce " yaya Zayd ka tashi da ga sama na na fara gajiya da koncin nan "

A hankali ya dan lumshe idanun shi , sannan ya koma geffen ta ya zauna

Ya na sauka da ga saman ta , ta tashi ta mike tsaye ta juya ta koma cikin part din

Da kallo ya rakata har sai da ya ga ta zauna saman sofa sannan ya tashi , ya na taku a hankali ya shiga falon ya na sallama kassa kassa

Kamar ta san ya yi sallamar a fili ta amsa mishi ta na kallon Tv

Geffen ta ya karaso ya zauna ya na kallon Tv din shi ma

A hankali ta juyo ta kaleshi cikin sanyi murya ta ce " yaya Zayd , yaushe zan koma school , na gaji da zama a gida "

Ba tare da ya kale ta ba ya ce " okay gobe ki shirya , sai mu je ki ga college din da na zaba miki "

Cike da murna ta washe baki ta na murmushi ta ce " da gaske gaske yaya Zayd ? "

Jinjina mata kai kawai ya yi , bai kai ga bude bakin shi ba ya ji ta fado mishi a jiki ta rungume shi ta na fadin " nagode yaya Zayd "

Tsit ya dauke na wucen gadi , dan bai shirya wa hakan ba da ga gare ta

Ajiyar zuciya ya sauke ya lumshe idanun shi slowly ya bude , ya kai hannu shi saman bayan a hankali ya dan bubuga cen kassan makoshi kamar mai rada ya ce " okay Ya isa haka "

❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥

( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )

STORY & WRITTEN BY : ANISH

Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

PAGE 26 ❤🔥

A hankali ta dago da ga jikin shi ta na kallon face din shi ,
Da sauri ya kauda kai gefe dan ba ya son ya kali face din ta

Murmushi mai dan sauti ta yi kafin ta mike da ga jikin shi ta koma gefe ta zauna ta na kallon Tv

Washe gari

Misalin karfe 8 na safe

Tsaye Inaya ta ke cikin falo, ta na sanye cikin wata gown mai bala'in kyau navy blue da na da wani madauri a tsakiya
Ta saka wani dan karamin hijab zuwa kirji sky blue ta yi kyau over
Chapter 38 · 0% Book details