← Book details Exile Princess Love And Power Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 44

Sashe 3

Exile Princess Love And Power Complete Hausa Novel · about 8 min read

SAI MUN HADU GOBE 🤘 KAR KU MANTA KU NA TARE DA ALKALAMIN ANISH , WANNAN SO MA TABI NE

❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥

( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )

STORY & WRITTEN BY : ANISH

Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

PAGE 2 ❤🔥

After some minutes ya fito sanye da wandon three cuter black colour da t-shirt fara mara nauyi , babu takalmi a kafar shi , ya na sanye da bakaken glass kamar kullum

Takowa ya ke cike da izza da kwarjini , hannun shi na rike da wata dankareriar waya kirar Iphone 13 pro max mai launin Gold sai shining ta ke kamar zinaryar gaske

A hankali ya shigo falon ya nufi sofa three seaters ya Haye ya konta
Bayan ya konta ya daura hannun shi daya saman forehead din shi, dayan kuma ya fara latsa wayar shi

( KENAN BA MAKAHO BA NE DUK BASAJA CE YA KE 🥺🥺 TOH ME YA SA SHI YIN HAKAN 🤔🤔 )

Bai fi ten minutes ba da konciyar shi wani kyakyawan matashi ya shigo falon ya na sallama hannun shi rike da ledodin restaurant

Ko motsawa Zayd bai yi ba , ko sallamar shi cen kassan makoshi ya amsa mishi ita

Dan karamin murmushi saurayin ya yi kafin ya tako ya zauna saman sofa two seaters da ke geffen wadda Zayd ke konce sannan ya ajiye ledodin hannun shi saman table

" Al-Amir Nawfel ga abinci ka nan " ya fada ya na kallon shi ta wutsiyar ido

A dubu dari Zayd ya mike zaune ya matse fuska ya nuna saurayin da dan yatsa cikin turanci ya ce " kar na sake jin ka kira ni da wannan sunnan Diya idan ba haka ba "

Dariya sosai saurayin ya yi shi ma da turanci ya ce " In haka ne ni ma ka daina kira na da Diya , ni fa yanzu suna na Moussa " ya kai karshen ya na kashe mishi ido guda

Dan tsaki Zayd ya ja kafin ya ajiye wayar shi gefe ya matso bakin sofar , ya kai hannu ya janyo table din gaban shi sannan ya bude ledodin da Diya wato Moussa ya kawo mishi

Moussa kuma kallon shi ya ke ya na murmushi har sai da ya ga ya fara cin abincin sannan ya ce " Zayd wai ka na da labarin......... "

Bai karasa maganar shi ba Zayd ya daga mishi hannu akan ya isa haka

" Haba Amir yanzu haka za mu ci gaba da zama yanzu wajen shekara hudu kenan , ba ka kewar Al-Amira Tesnim da Malikat Al'Umu ka na tunanin halin da su ke ciki , ko kuma ka manta da Malik "

Shiru Zayd ya yi bai ce komai , ya ci gaba da cin abincin shi

Sai da ya ida sannan ya mike tsaye ya nufi dining room ya bude fridge ya dauki gorar ruwa guda ya dawo ya zauna inda ya tashi sannan ya bude ta ya fara sha

Jinjina kan shi Moussa ya yi cikin ranshi ya ce " Gaskia kam jinin sarauta ba wassa ba ne , ko da ba cikin masarautar ya ke ba "

" Amir wai yanzu haka za mu ci gaba da wannan zaman , mu fa jinin mayaka ne , zama ba na mu ba ne " Moussa ya fada cikin raunin murya

Sai da Ya ida shan ruwan shi sannan ya mike ya nufi corridor ya na fadin " ai ka san hanyar komawa ni ban tare ka ba "
Ya na gama fadar haka ya shige corridor ya shiga bedroom din da ya fito

Jinjina kan shi kawai moussa ya yi ya na murmushi ya ce " ni anya ba diyar malan din nan ya fara so ba , ka san dama an ce soyayya ke meda sarki bawa " ya kai karshen ya na bushewa da dariya

Sai da ya ida dariyar shi sannan ya mike ya dauki ledodin saman table ya kai kitchen sannan ya dawo ya nufi corridor ya shiga dayan bedroom da ke kussan wanda Zayd ya shiga

Misalin karfe 8 na dare

Gidan su Inaya

Zaune su ke cikin harabar gidan saman tabbarma su na sanye da hijab dark blue har kassa ,
Malan na gaban su zaune ya na karatun kur'ani , su kuma sun sunkuyar da kai su na sauraron shi
Mama kuma ta na zaune geffen shi ita ma ta na sanye da hijab amma fari

Su na a haka wani dan matashin saurayi ya fito da ga cikin dakin da ke fuskantar na su Inaya

Ya hadu ba laifi skin din shi chocolate kamar ta Inaya amma ta Inaya ta fi dan haske
Ya na da dogon hanci da kontancen saje , ya na da dara daren idanu brown colour , ya na da dan tsayi da mudewar jiki amma ba sosai ba a shekaru ba zai wuce 26 ba amma ya tare kassunba ga kwarjini
Sanye ya ke da wando three cuter Fari da shirt red kamar jini ya na rike da waya kirar Tecno pop 6 sai latsawa ya ke

Bai bi ta kan mutanan gidan da le zaune kussan kofar dakin shi ba ya sa kai ya fice da ga gidan

Malan na kallon shi ta kassan ido amma bai ce da shi komai ba , sai da ya ida karatun shi saman ya dago kai ya kali su Inaya ya ce " Auta, ina ga za mu tsaya a nan gobe sai mu ci gaba "

Jinjina mishi kai su ka yi a tare ba su ce komai ba , su ka mike su ka shiga dakin su dan su ajiye littafan su

Bayan mintina goma Inaya ta fara fitowa ta na sanye da doguwar riga irin ta barci da dan guntun kyale ta ya yafa a kan ta

Ta na fitowa ta ji ana sallama
Cak ta tsaya ta na kallon kofar gidan kafin ta amsa sallamar

Wani dan karamin murmushi ta saki ganin waye ke tare da yayan na ta
Da gudu ta je ta fada jikin yayan ta ta na fadin " yaya Abdoul kenan yaya Zayd ka je nemowa " ta fada ta na kallon Zayd ta geffen ido

Raba jikin ta ta yi da na Abdoul sannan ta ce " sannu da zuwa yaya Zayd "

Jinjina mata kai kawai ya yi bai ce komai ba

Duk abun da su ke Malan ya na kallon su amma bai ce komai ba sai ma murmushi da ya ke

" malan Zayd ku karaso mana " malam ya fada cikin zolaya

Yar dariya Inaya ta yi ta riko hannun Abdoul, shi kuma ya riko hannun Zayd su ka fara takawa a jere

Saman tabbarma sa malam ke zaune su ka karaso

Saki hannun ta Abdoul ya yi sannan ya ce ma Zayd su zauna

A tare suka zauna geffen Malam su ka sa Zayd a tsakiya

Ta na ganin sun zauna ta juya ta fara takawa ta nufi hanyar kitchen dan ta taimaka wa mama

Kamar an ce ya dago kai ya kali gaban shi
Ya na dagowa idanun shi ba su sauka ko ina ba sai saman hips din ta , gashi rigar da ta ke sanye yar shara shara ce a na ganin shape din ta

Sai da ya ji zuciyar shi ta buga a dubu dari ya sunkuyar da kan shi dan ya yi arba da abun da ya fi karfin shi

Malam sa Abdoul sarai su ka lura da shi, dan Abdoul har kumshe dariya ya ke

Dan murmushi Malam ya yi kafin ya matso cikin rada ya ce " Zayd in ka shirya ni ban da matsala ka zo ka dauki matar ka ta tare a dakin ka "

Dago kai ya yi ya kali malam ya na zaro idanu duk da su na cikin bakin glass

Yar dariya malam ya yi dan dama tsokanar shi ya ke son yi
Shi ma Abdoul yar dariya ya yi kafin ya daura hannun shi saman kafadar Zayd ya ce " Bro ka yi sauri fa dan kar ayi maka wufff da ita "

Dan tsaki Zayd ya ja ya na kauda kan shi gefe
Dai'dai lokacin da Inaya je fitowa da ga kitchen ta na rike da tray

Da sauri ya kauda kan shi dayan geffen cikin ranshi ya na fara danasanin abun da ya yi shekarun da su ka wuce

Gaban su ta zo ta ajiye tray din sannan ta mike ta juya ta koma dakin su

Ta na barin wajen Abdoul ya kai hannu ya janye tray din na sama , ya dauki spoon ya mika ma Zayd da malam sannan ya ce musu bismillah

A tare su ka fara cin abincin , har su ka Kamala ba wanda ya ce ma dan uwan shi wani abu

Sai da su ka ida mama ta zo ta gyara wajen ta kawo musu jug na ruwa da glass biyu , su ka sha sannan Zayd ya ce da Abdoul ya raka shi gida

Sai da ya tsokane shi sannan su ka tashi su ka bar gidan a tare

Ya na fita Inaya ta fito da ga dakin su
Ta na ganin malam zaune shi kadai

Da sauri ta karaso wajen shi ta ce " Abba yaya Zayd har ya tafi " ta kai karshen ta na kallon wajen kofar gidan

Dan murmushi yayi kafin ya mata nuni da gefen shi
Ba musu ta tako ta zauna geffen shi ta na sunkuyar da kai ta fara wassa da yatsun ta

Hannu shi ya daura saman kan ta kafin ya ce " Auta , fada min gaskia , ki na son Zayd "

A razane ta dago kai ta kaleshi ta na zaro idanu, ta ma rasa amsar da za ta bashi

Daga mata gera yayi kafin ya ce " ba ki ba ni amsa ba "

Da sauri ta ce " a'a Abba ba ni son shi " ta na gama fadar haka ta mike da sauri ta koma dakin su
Ya na kallon ta har ta shiga dakin su , sannan ya saki murmushi ya na girgiza kan shi
Chapter 3 · 0% Book details