← Book details Exile Princess Love And Power Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 44

Sashe 4

Exile Princess Love And Power Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bangaran Inaya kuma ta na shiga dakin su ta fada saman gadon su ta yi rub da ciki

Bugun ta a baya Nesrine ta yi kafin ta ce " ke dan Allah malama yi a hankali kar ki kare mana gado "

Dago kai Inaya ta yi ta zauna ta na kallon ta
Dan turo baki tayi cikin shagwaba ta ce " kin ga ko ku daina bugu na ko in fada ma Abba "

" ina ruwa na tashi muje na raka ki ma " ta fada ta na meda kallon ta saman book din hannun ta

Marairaice fuska Inaya ta yi kafin ta ce " Nesrine, wai Abba tambaya ta ya yi in ina son yaya Zayd " ta kai karshen kamar ta yi kuka

Dago kai Nesrine ta yi ta kale ta da kyau kafin ta bushe da dariya har da dafe ciki

Marairaice fuska Inaya ta yi kamar ta yi kuka ta ce " haba Nesrine ya zan yi miki magana ki yi zaune ki na yi min dariya "

Dan tsagaita dariyar ta Nesrine ta yi kafin ta ce " Yau ni tambayar Abba ce ta bani dariya , yo mi ne abun so cikin wannan abun , mutumin da ba ya magana , ba ya gani wa zai iya zama da shi ai ni ko sadaka a ke bani shi wlh ba ni so " ta kai karshen ta na sake bushewa da dariya

Hararrar Inaya ta yi kafin ta ce " kin ga matsala ta da ke wlh ba a iya magana da ke "

" yo ai wannan ba magana ba ce zancen gaskia wa zai iya son Zayd, ba dan kyawon shi ba ai ko kallo bai isa wani ba "

" wai ke me ya sa ki ke yawwan cin zarafin mutane, me ya yi miki, kullum sai kin kaskantar da shi , ko dan kin ga ba ya da kowa ba ya da idon gani , ba ya da bakin magana ko dan bashi da kudi , kin je makaranta ki yi karatun kur'ani ki san Allah ba ya son mai kaskantar na kassa da shi , yanzu in kin wayi gari kin koma kurma ko makafniya ki na tunanin wani zai so ki ne , wlh Nesrine ki ji tsoron duniya wannan jiji da kai da ki ka dauko ba na familyn mu ba ne , ba mu gado wannan ba gwara tun wuri ki tambayi kan ki ina ki ka dauko su "

" ke dan Allah malama ya isa dan kawai na tabo wani banza cen shi ne za ki yi zaune ki na min fada kamar wata uwa ta , ai ba karya na yi ba dan ko ke da kan ki da ki ke kare shi ba son shi ki ke ba dan haka ki bani lfy sakara kawai , kamata ya yi ki tafi massalaci ki dauki speaker ki ringa yi musu wa'azi ko ba komi kin samu lada no sens " ta kai karshen ta na saukowa da ga saman gadon ta fice da ga dakin

Ta kallo Inaya ta rakata har sai da ta fita sannan ta ce a fili " wlh karya ki ke, duk abun da zai sa mace ta so namiji yaya Zayd ya malake shi , dan ya ma fi sauran mazan wlh ko cikin dubu za ki duba da wuya ki samu kamar yaya Zayd " ta kai karshen hawaye na zubo mata

Da sauri ta koma ta yi rub da ciki ta fara kuka kassa kassa

Zayd

Tafiya su ke saman hanya shi da Abdoul, sai zuba ya ke mishi amma shi kuma ko kalma daya bai ce da shi ba

" Zayd wai mi ne sunan ka na gaskiya " Abdoul ya tambaye shi

Cak ya tsaya da tafya ya na kallon gaban shi kamar ya ga wani abu ya kassa gaba ya kassa baya

A hankali ya medo da kallon shi kan Abdoul ya zuba mishi ido mai ce komai

Ganin ya yi shiru kuma ya tsaya ya na kallon shi ya sa Abdoul cewa " ko sunnan na ka ma ka manta "

Jinjina mishi kai Zayd kafin ya fara takawa ya yi gaba

Dan murmushi Abdoul ya yi kafin ya ce " to tun da ka san hanya ni zan koma gida " ya fada ya na daga mishi murya

Bai ce mishi komai ya ci gaba da tafiyar shi

Ganin bai ce komai ba ya sa Abdoul juyawa ya koma gida

Shi ma Zayd hanyar gidan shi ya kama
Bai fi minti biyu ba ya iso gida

Da sallama bakin shi ya shigo falon gidan nan ya isko Moussa ya na zaune saman sofa da ga shi sai short da singlet ya na latsa wayar shi

Dago kai ya yi ya na amsa mishi sallamar shi kafin ya ce " Amir wai ina ka tsaya ne haka tun dazu ni ke jira ka "

A hankali ya sa hannu ya zame glass din idanun shi
Allahuma barik ashe ba banza ba ya ke saka glass ba
Ya na da dara daran idanu Farare kal kamar madara
Launin idanun shi Hazel mai bala'in kyau, sai wani shining ya ke abun har ya ba ka tsoro kamar idanun mage cikin dare haka su ke

Karasowa ya yi cikin falon ya ajiye glass din saman table sannan ya jingina bayan shi a jikin sofar ya daga kan shi sama ya lumshe idanun shi

Duk abun da ya ke Moussa ya na kallon shi amma bai ce da shi komai ba dan ya san abokin na shi ba karamin miskili ba ne ba bazan ba a ka kassa gano shi ba kurma ba ne

Ajiye wayar shi Moussa ya yi saman table kafin ya matso bakin sofar ya kai hannu shi ya dafe cinyar Zayd

Medo kan shi ya yi a hankali sannan ya bude idanun shi ya daga mishi gera allamar minene ?

" Amir wai me ya ke damun ka ne , duk ka bi ka sauya kamar ba Al-Amir Nawfel ba magajin Malik , ko dai ka fada soyayya ne " ya kai karshen ya na kashe mishi ido guda

Dan tsaki Zayd ya ja kafin ya kauda kan shi gefe kafin ya ce " Diya dan Allah ka bar kira na da wannan su nan, wannan sunnan ya goge da ga cikin rayuwa ta tun lokacin da mu ka shigo garin nan "

" in haka ne ka daina kira na da Diya ni ma , yanzu Amir baza ka koma ka karbi mulkin ka ba "

Da sauri ya katse shi da cewa " ai Malik bai mutu ba , har yanzu ya na kan mulki kuma ko ya mutu ba ni son mulkin, a kan shi a ka nemi halaka ni dan haka su je na bar musu kayan su , na ga ai kaima yarima mai jiran gado ne me ya sa baza ka koma masarautar ku ba ka karbi mulkin "

Yar dariya Moussa ya yi ya na dauke hannun shi da ga saman cinyar Zayd sannan ya ce " haba kai ma Zayd ta ya zan karbi mulki bayan ni ne na uku babban yayan mu na raye zan ce na karbi mulki shi ya sa na baro musu kayan su , ni fa mulki sam ba ya cikin tsarin rayuwa ta ba yadda za ka yi an haifo ka cikin jinin sarauta dole ka hakura "

Mikewa tsaye Zayd ya yi ya bar falon

Har zai shiga corridor ya tsaya ba tare da ya juyo ba ya ce " ka na da labarin Amira da Malikat Al'Umu ? "

Dan murmushi Moussa ya yi kafin ya ce " kar ka damu su na cikin koshin lafya "

Jinjina kan shi kawai ya yi sannan ya fara takawa ya shiga corridor din ya shiga bedroom din shi

Ya na shiga shi ma Moussa ya mike ya koma bedroom dinshi shi ma

Washe gari

AMINU KANO COLLEGE OF EDUCATION

Nesrine

Zaune ta ke kassan wata bishiya cikin harabar college din ta na rike da wani book ta na karatu

Kamar da ga sama ta ji an zabce mata book din ta

A dubu dari ta dago kai , wata irin mumunar faduwa gaban ta ya yi lokacin da ta yi arba da wanda ya zabce mata book din ta

Wasu samari ne guda biyu su na tsaye gaban ta

Wanda ke rike da littafin ta ya fi dayan tsayi kadan ya kuma fi shi haske ya na da dogon hanci da kananan idanu ya dan tara gashin kai
Ya na sanye da crazy jeans blue da t-shirt blue ita ma

Daya kuma ya na da dan duhu kadan amma kamanin su daya sai dai wannan bai tara gashin kai ba, idanun shi brown colour ne , kuma ya na da saje lips din shi kuma sun dan yi pink kadan
Shi kuma ya na sanye da jeans baki da t-shirt fara

Wanda ke rike da book din ta ya fara magana ya ce " baby wai ba na ce da ke ba ki ringa samu na a wajen parking space lokacin break ba "

Wasu yawu Nesrine ta hadiye murya na kerma ta ce " yi hakuri Hafiz bazan sake ba "

Geffen ta ya zo ya zauna ya na mika mata book din ta ya ce " ba komai baby nan din ma ya na da dadin zama sai dai da mutane dayawa shi ya sa na ce ki ringa tarda ni parking space "

Ta na shirin magana ta ji Muryar Inaya ta na yi musu sallama

A tsorace ta dago kai ta kale ta

Inaya kuma ta yi zaton classmate din nesrine ne sai ba ta ka komai a ran ta ba ta kali yar uwarta ta ce " Nesrine dan Allah in kin tashi tafya gida ki jira ni "
Ta na gama fadar haka ta juya da gudu ta bar wajen kamar ta ga wani abun tsoro

Tun da ta iso wajen saurayin da ke tsaye ya tsare ta da idanu sai kallon ta ya ke ya na hadiye yawu
Chapter 4 · 0% Book details