← Book details Exile Princess Love And Power Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 44

Sashe 23

Exile Princess Love And Power Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yanzu kwana shida kenan da tafiyar su Zayd , Inaya kuma ta koma gidan malam dan ya ce ya na tsoron wani abu ya same ta a cikin gidan , akasin sa a ka samu lokacin da ta dawo gidan malam ta manta ba ta dauko wayar da Zayd ya ce mata ta dauka cikin bedside drawer , ranar da ta koma gidan malam a ranar ya yi mata kira na farko ba ta daga ba tun da ga lokacin kullum sai ya kira ta amma ba ta dagawa, sannu sannu har ya fara damuwa a kan ta , Inaya kuma sam ba ta san abun da ke faruwa ba dan ta na cen gidan su ta na sha'anin ta da Nesrine da ga school sai gida , sai kuma islamyar da malam ke yi musu a cikin gidan kuma , kwana biyu duk ta bi ta wanke dan wannan karan mama ta ce ba za ta bar ta ta koma gidan mijin ta a haka ba , kun dai san Haoussa fulani da iya gyaren jiki to haka Inaya ta sha gyara har wani haske ta kara skin din ta ta kara fitowa chocolate gwanin burgewa kamar ka sace ta ka gudu
Shin cikin ku ba wanda zai tambaye ni da Moctar kuma ?
Hum tun ranar da Inaya ta mare shi ya saka mata ido , har tafiyar da Zayd ya yi ya na sane da ita , har komawar ta gidan su duk ya na sane , lokaci kawai ya ke jira dan ya aiwatar da abun da ya shirya mata

TOHHHH KO WA NE ABU NE WANNAN , DA GA JI DAI NA SAN BA AL'HERI BA NE 😓

Washe gari ( week-end )

Abuja

Zayd

Wani katafaren office na glass , da ga ciki ka na iya hangen abun da ke waje amma na waje ba ya iya ganin na ciki , komai na cikin office din fari ne kal , har tiles din wajen farare ne kal sun sha mopping sai kyali su ke kamar yanzu a ka saka su , a geffen dama wasu lalawsan sofas ne farare guda uku , guda three seater da biyu two seaters su na fuskantar juna , sai wata yar karamar table a tsakiya , bayan doguwar sofar wani madaidaicin fridge ne , a geffen hagu kuma wani closet ne dauke da wasu files colour daban daban , sai wani desk da ke fuskantar kofar shigowa office din da wani computer a sama, sai dan takardu da files a gefe daya, a daya geffen kuma wani kwalin tissue ne , bayan desk din wata lalawsar chair ce fara kal cikin ledar ta da allamun sabuwa ce , office din sai tashin wani dadaden kamshi ya ke

A hankali ya turo kofar office din ya shigo kai a sunkuye ya na kallon wayar shi , ya na sanye da wando jeans baki da t-shirt purple , gashin kan shi ya dan taru dan yanzu ya kai mishi har bayan wuya ya zubo saman shoulder din shi , sai baza kamshi yake duk irin kamshin da office din ya ke sai da kamshin turaren shi ya kashe shi

Slowly ya ke takowa, Moussa na bayan shi ya na rike da wani file ya na dubawa sai magana ya ke mishi amma sam ba ya jin shi ya yi nisa cikin duniyar tunanin shi

Sai da ya karaso wajen sofas ya zauna saman three seaters ya na latsa wayar shi, Moussa na biye da shi ya na mishi magana

Sai da su ka dauki lokaci kafin Moussa ya dago kai ya kaleshi ya ce " me ka ke tunani a kan wannan file din "

Dago kan shi ya yi slowly ya kali Moussa ya ce " wane file "

Zaro idanu Moussa ya yi kafin ya ce " ka na nufin duk abun da na yi ta fada maka sam ba ka ji ni ba "

" dama magana ka ke yi ne " ya kai karshen ya na meda kallon shi kan wayar hannun shi

Hararrar shi Moussa ya yi ya ce " amma wlh Amir ka ci uwar raina min hankali, yanzu duk zubar da na yi zaune ina yi ba ka ji ni ba , tsaya ma tukunna me ka ke kallo cikin wayar nan "

Shiru za ya yi bai tanka mishi ba, sai da ya dauki lokaci kafin ya mike tsaye ya fara takawa zai bar office din ya na fadin " ka shirya mu koma kano yanzun nan "

Da sauri Moussa ya ce " Amir mu koma fa , ko aikin da ya kawo mu ba mu gama ba ka ce mu koma "

Ba tare da ya tsaya da ga tafiyar shi ya ce " za ka iya zama ni ka ga tafiya ta " ya fada dai'dai lokacin da ya isa bakin kofar ya ficewar shi

Da kallo Moussa ya raka shi har sai da ya fita sannan ya ce " hmmm ni na san ba a banza ka ce mu koma kano , kawai ka kewar babyn ka amma ba ka iya fitowa ka fadi ba komai hakan ma wata nassara ce " ya kai karshen ya na mikewa ya bar office din shi ma

Kano ( Gidan malam )

Misalin karfe 10 na safe

Zaune su ke cikin yar runfar kofar dakin mama saman wata tabbarma

Nesrine na tsintar shinkafa , Inaya kuma na yankar kayan lambu , mama kuma ta na kallon su gwanin ban sha'awa

Su na a haka Inaya ta kali mama ta ce " mama ina son in koma cen gida in gyara shi , gobe yaya Zayd zai dawo dan gobe ya ke cika one week da tafiya kuma ya ce min one week za su yi "

Murmushi mama ta yi dan har cikin ran ta ta ji dadin maganar Inaya
" babu komai bari in malam ya dawo zan fada mishi , in yamma ta yi sai ku tafi ke da Nesrine ta kama miki "

Da to ta amsa mata kafin ta ci gaba da aikin ta

Misalin karfe 4 na yamma bayan sun ida girki sun yi duk wasu ayika na cikin gidan sannan su ka tafi gidan Zayd , nan ma su ka gyara gidan tsab su ka share ko ina har da bedroom , su ka yi mopping , sannan su ka kunna ma gidan turaren wuta da mama ta basu su biyo da shi

Sai wajen kirayen sallar magriba sannan su ka Kamala , Nesrine ta so su koma gida ita da Inaya amma ta ce nan za ta kwana a haka ta hakura ta koma gida ita kadai

Inaya kuma bayan ta gabatar da sallar magriba ta fara daura girkin abun da za ta ci , sai bayan sallar isha sannan ta Kamala

A nan falo ta zauna ta ci abincin ta ta na kallon Tv hankali konce ba ta ma tsoron wani abu ya same ta cikin gidan

Bayan ta Kamala cin abincin ta , ta gyara wurin ta kai dishes din kitchen ta wanke sannan ta dawo ta ci gaba da kallon Tv din ta

Sai wajen karfe 11 na dare ta tashi ta shiga bedroom din Zayd ta konta ba jimawa barci ya yi gaba da ita

Misalin karfe 1 na dare

A hankali ya ke takowa cikin corridor din gidan hannun shi rike da torch ya na haska inda ya ke takawa

Sai da ya kai bakin kofar dakin farko ya kai hannu ya murda handle din a hankali kamar barawo ya tura kofar ya shiga

Sai da ya haske ko ina na cikin dakin da torch din hannun shi ya ga babu kowa sannan ya juya a hankali ya bar dakin

Ya ci gaba da tafiyar shi har ya karaso kofar dakin da Inaya ke ciki
A nan ma a hankali ya kama handle din kofar ya shiga a hankali

Ya na shiga dakin ya fara haske wajen da torch din shi

Cen Moctar ya hango Inaya konce ta gadon ta na sanye da kayan barcin ta wando da riga rigar ta nade mata har a na iya ganin cibiyar ta , wannan dark hair din ta ya baje saman pillow ta na barcin ta cikin konciyar hankali

Ya na ganin ta ya saki wani makirin murmushi ya nufi dressing mirror ya ajiye torch din hannun shi a hankali sannan ya fara takowa a hankali ya nufi gadon

Sai da ya tsaya ya kare mata kallo da kyau cikin zuciyar shi ya ce " yau dai zancen ya kare ba ni ki ka mara zan miki abun da zai kin mutu ba ki manta ba "

Ya na gama fadar haka ya kai hannu ya cire rigar jikin shi ya tila ta saman gadon sannan ya zame belt din wandon shi

( WAYOOO , ALLAH KA KAWO MA BABYN ZAYD DAUKI KAR YA CUTAR DA ITA 😭😭 )

Tila belt din ya yi saman rigar shi ya kai hannu zai zame wandon shi , sai ya ji an damko hannun shi ta baya

Dum zuciyar shi ta buga dan bai yi tunanin dakwai mutane cikin gidan

Ya na shirin juyowa ya ga ko wa ya riko shi ya ji an toshe mishi baki, aka murde daya hannun da a le rike da da karfi har da ya yi wata kara

Nan take idanun Moctar su ka kawo ruwa ya na son ya yi kara dan zafi amma ba hali

Ya na a haka ya ji an juyo da shi a ka fara tura shi su ka bar dakin ba tare da an janye hannun da ya toshe mishi baki

Su na fitowa falon gidan, Moussa ya shigo ya na janye da trolley

Zaro idanu Moussa ya yi ya na kallon su cike da mamaki ya ce " Amir wanene wannan kuma "

Bai bashi amsar tambayar shi ya wuce zai bar falon

Da sauri Moussa ya kauce ya bashi hanya ya na sakin trolley din hannun shi ya bi bayan su da sauri

Shi kuma Zayd ya na fitowa ya nufi parking space ,
Chapter 23 · 0% Book details