← Book details Exile Princess Love And Power Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 44

Sashe 18

Exile Princess Love And Power Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da ya dauki wajen good two minutes kafin ya kai hannu slowly ya zame bakaken glass din shi

Dum Nesrine ta ji gaban ta ya fadi dan ba karamar razana ta yi ba da ganin wadanan hazel eyes din na shi ga shi sai wani kyali su ke saboda hasken rana

Ta na a haka ta jiyo wannan zazzakar Muryar ta shi ya na fadin " ban san abun da na yi miki ba da ki ka tsane ni haka , a sani na tun lokacin da ku ka shigo gidan nan ko kalma daya ba ta taba shiga tsakani na da ke amma yau sai da ki ka sa na yi miki magana ba da so na ba , kamar yadda ki ke ji ni ba kurma ba ne ina magana kamar yadda ki ke magana sannan kuma ina ganin ki kamar yadda ki ke gani na a tsaye gaban ki , ban zo gidan nan dan na fada muku ko ni wanene ba , na zo ne dan na fada muku dalilin da ya sa ku ke min kallon makaho da kuma kurma , shekara biyar kenan da na zo Nigeria kuma a nan kano na sauka , Lokacin da na shigo Garin nan ba na jin haoussa da ga turanci sai larabci kuma ba kowa ba ke jin su dalilin da ya sa na dinga yin shiru dama cen ni ba ma'abocin magana ba ne shi ya sa duk wata magana da zan yi sai dai na yi ta da hannu in kuma tambaya ce na girgiza kai a haka har mutane su ke min daukar kurma kuma kuka zo ku ka same ni a hakan, sannan kallon makahon da ku ke min na san ya samo nasaba ne da bakaken glass di na da na ke sanye da kullum, ina saka su ne saboda nassan a nan Africa ba kowa ba ke da colour din idanu na hakan na tsoratar da mutane su na yi min wani kallo cen daban dalilin da ya sa na ke saka su , sandar da ki ka ga ina yawwan rikewa kuma "

Ya kai karshen ya na sa hannu shi cikin aljihun shi ya fido wani dan abu kamar remote
Ya na danna shi nan take abun ya yi wata kara ya kara tsayo ya koma kamar sanda
Sannan ya sake danna button din sandar ta koma kamar da farko

" ba sanda ba ce kamar yadda ki ke tunani , duk wani mumunar zato da ki ke yi a kai na yau na tabbatar miki da ba gaskia ba ne , zan so nan gaba ki fara sannin wanene mutun kafin ki kaskantar da shi , da zan fada miki ainahin wanene ni to za kiyi mamaki ki tambayi kan ki abun da ya kawo ni nan amma bazan fada miki ba nassan wannan karamar kwakwolwar ta ki baza ta dauka ba amma ki sani ba sunana Zayd ba duk ranar da ki ka samo sunana na gaskiya ki zo ki fada min zan baki kwatar dukiyar da ko jikokin jikokin ki sai sun ci albarkacin ta " ya na gama fadar haka ya meda bakin glass din shi ya juya ba tare da ya ce komai ba ya bar gidan

Nan ya bar Nesrine baki sake tun lokacin da ya fara magana ta na zaro idanu

Sai da ya fita sannan ta kali mama ta kali malam
Ta na shirin magana Abdoul ya riga ta cewa " Nesrine me ki ka ma Zayd kuma "

Cike da mamaki ta ce " yaya Abdoul ba ka mamakin yadda yaya Zayd ke magana ko dai kunnuwa na ne "

Malam ne ya bata amsa da cewa " ba kunne ki ba ne Zayd ya na gani kuma ya na magana , a sani na bai taba bude baki ya ce miki shi kurma ne ko makaho ni ban san me ki ka mishi ba amma zan tambaye shi , kai Abdoul wuce mu tafi massalaci " ya kai karshen ya na juyawa ya fita gidan

Shi ma Abdoul takawa ya yi ya bi bayan shi su ka bar gidan su ka bar mama da Nesrine nan tsaye sai faman muzurai su ke

Sai yanzu Nesrine ta tuno da kalamun Inaya da ta ke ce mata " wai Nesrine wa ya fada miki yaya Zayd kurma ne , ko kuma shi ya fada miki shi makaho ne " kennan Inaya ta san cewa ba makaho ba ne shi ya sa ta ke son shi ? Ko kuma ya zancen ya ke ?

Nesrine na shirin magana mama ta riga ta cewa " kar ki tambaye ni abun da ki ka ji shi na ji " ta na gama fadar haka ta wuce ta shiga dakin ta

Ita ma Nesrine ta juya ta koma dakin ta zuciyar ta na duka uku uku kamar ta ga abun tsoro

Inaya

Ta na jin ya fara takawa ya bar dakin ta dago kai ta bi bayan shi da kallo har sai da ya fita dakin sannan ta mike tsaye ta gyara komai na cikin dakin sannan ta shiga ta yi wanka ta shirya cikin wandon palazzo pink colour da riga zuwa guyiwa white colour ta saka dan karamin hijab zuwa kirji

Falon gidan ta fito nan ta ga babu kowa duk sun fice , sai ta wuce kai tsaye kitchen dan ta shirya musu abinci

Misalin karfe 5 na yamma ta Kamala girkin ta shirya komai saman dining table sannan ta gyara gidan tsab har da bedroom din Moussa ta wanke toilet din dakin , har da harabar gidan sai da ta fito ta share sannan ta koma ta feshe gidan da turare

Wajen kiyaye²n sallar magriba ta koma dakin ta ta yi wanka ta dauro Alwalla sannan ta sauya kayan jikin ta ta saka gown mara nauyi purple sannan ta saka hijab har kassa shi ma purple sannan ta gabatar da sallar ta , bayan ta gama ta zauna yin karatun kur'ani , ba ta Kamala ba sai da a ka yi kiran sallar isha ta tashi ta gabatar da sallar

Misalin karfe 8 na dare

Ta na zaune cikin falon gidan ta cire hijabin jikin ta , ta ajiye shi gefe ta saki wani dark hair din ta har cikin baya , kun san fulani su ma ba baya ba wajen gashi bare uwa bafulatana uba bafulatani kun ga ba mamaki ta yi gashi

Ta na zaune ta na kallon tashar Arewa 24 a Tv duk hankalin ta ya na wajen Tv din a na shirin mata a yau

Ta na a haka ta jiyo sallamar Moussa
Dan murmushi ta yi kafin ta amsa sallamar shi ta na yi mishi sannu da zuwa

Murmushi ya yi kafin ya tako a hankali ya zauna saman sofar da ke fuskantar ta ta
Ya na zama Zayd ya shigo falon ya na sallama cen kassa kassa yadda shi kadai ya san ya yi abu ne

Abun mamaki kuma sai da Moussa ya amsa sallamar dan ya san abokin shi da wuya ya shigo wuri bai yi sallama ba, ko da kuwa ba wanda ya ji ta

A hankali ya karaso cikin falon ya zauna geffen Moussa
Sannu da zuwa Inaya ta yi mishi ta na murmushi , jinjina mata kai kawai ya yi ya na kallon ta ta cikin bakin glass din shi , kamar bai taba ganin ta ba

Ya na a haka ya tsinci Muryar Moussa ya na fadin " baby me kuma a girka mana ni fa yunwa na ke ji "

Da sauri Zayd ya juyo ya kaleshi ya juya ya kali Inaya sai ganin ya yi ta saki murmushi ta mike tsaye ta dauki hijabin ta ta saka ta ce mishi " yaya Moussa ni fa tun dazu na gama ina jiran ku " ta na gama fadar haka ta shiga dining room

Mikewa Moussa ya yi ya bi bayan ta ya shiga dining room ya ja kujera guda ya zauna sai bin ta ya ke idanu

Shi kuma Zayd sai kallon su ya ke wata zuciyar na ce mishi ya tashi ya shake Moussa ko ya rage zafin kishin da ya ke ji

Ya na kallon su har Inaya ta yi serving din shi ta mika mishi plate din ta na murmushi sannan ta janyo kujerar da ke fuskantar tashi ta zauna ta yi serving din kan ta , sannan ta fara ci

Da allamun ta manta da mijin na ta baki daya sai abincin ta ta ke ci su na hira ita da Moussa har da dariya

Zayd kuma ganin abun na su na neman ya yi mishi katutu ya sa ya mike a hankali ya nufi corridor ya shiga bedroom din shi kai tsaye ya Haye saman bed din shi ya yi rub da ciki

Moussa da Inaya kuma sun ma manta da shi sai hirar su su ke , sai da su ka Kamala cin abincin su sannan su ka tatare dishes su ka kai kitchen su ka wanke a tare sannan su ka dawo falo su ka zauna, Moussa ya saka musu wani horror film su ka fara kallo

Su na a haka Zayd ya fito da ga cikin corridor sanye da wando three cuter baki da t-shirt purple yanzu ma ya na sanye da bakin glass din shi

❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥

( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )

STORY & WRITTEN BY : ANISH

Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

PAGE 13 ❤🔥

A hankali ya takowa cikin falon cike da izza kai a sunkuye
Har sai da ya karaso sofar da Moussa ke zaune ya zauna shi ma ya na kallon Tv din

Jim kadan da zaman shi Moussa ya mike ya ce ma Inaya sai da safe shi zai shiga barci da to ta amsa mishi sannan ya juya ya shiga corridor ya wuce bedroom din shi ya bar ta nan ita Zayd

A haka su ka ci gaba da kallon film din a tare har sai da a ka zo wajen wata scene mai ban tsoro
Chapter 18 · 0% Book details