Sashe 35
Exile Princess Love And Power Complete Hausa Novel · about 6 min read
A tare kowa ya kai duban shi kan kofar Banda Inaya da Zayd
Kowa ya zubawa kofar ido ya na jiran ya ga wanda zai shigo
Nan su ka ga nurse din da Zayd ya dauko ta kula da Nesrine ta shigo falon ta na sallama ta na rike da Nesrine sanye da wata riga blue ta na jan kafa
A dubu dari mutanan falon su ka mike su ka yi kan ta
Mama har da sakin kuka ta rungume ta , ta na fadin " Nesrine di ta ke ce , Allah na gode maka, sannu kin ji "
Ita ma rungume mama ta yi da kyau ta na sakin kuka mai cin rai
Duk abun da ke faruwa Zayd ko janye idanun shi bai yi ba da ga saman Inaya
Ita ma ta kurawa Tv ido babu ko kiftawa
Ya na tsaka da kallon ta ya ga ta ja wani dogon nunfashi ta saki wata razananiyar kara da karfi ta ce " kar ku zo ku kyale ni , ku kyale ni ahhhhhhhhhhh " ta kai karshen ta na sake sakin kara
Dan lumshe idanun shi Zayd ya yi dan dama abun da ya ke tunani kenan dan ya na tune ta taba yin hakan
Da sauri mutanan gidan su ka jiyo su ka kale ta , ta sa hannayan ta duka biyu ta toshe kunnuwan ta sai kara ta ke
Da gudu malam ya juyo ya yi kan ta ya na fadin " auta lafya ? Me ya faru ?"
Cikin fitar hayaci ta ce " Abba sun san muna nan , sun sani , sun sani " ta kai karshen ta na sakin kuka
Da sauri Zayd ya mike ya yi kan ta , sai dai kafin ya iso ta dauke lokaci guda ta sume a wajen
Ya na isa bai tsaya yi wa malam magana ba kawai ya dauke ta da hannayan shi biyu kamar baby ya nufi stair da ita
Malam na nan zaune ko wani kwakwaran motsi bai yi ba
Sakin Nesrine mama ta yi ta tako wajen malam ta dafa kafadar shi ta ce " Abban Abdoul me ya same ta kuma "
Ta na taba shi ya dawo cikin hayacin shi , da sauri ya mike tsaye ya nufi stair da gudu
Ya na barin wajen Moussa ya kali Nesrine ya ce " sister ya jikin na ki ? "
Dan karamin murmushi ta yi kafin ta bude baki ta ce " da sauki " sai dai lips din ta ne kawai su ka motsa sautin bai fito ba
Murmushi shi ma ya yi mata ya jinjina mata kai sannan ya juya shi ma ya nufi stair ya Haye
Dakin Inaya malam ya tafi sai dai ya na shiga ya ga bedroom din ba kowa a ciki
Da sauri ya juyo ya fito dakin dai'dai lokacin da Moussa ya hayo wajen
" Moussa ina kuma Zayd ya kai ta ? " malam ya tambaye shi
Kallon kofar dakin Zayd ya yi, ya ga ta na bude kadan kafin ya juyo ya kali malam ya ce " uncle , ina ga bedroom din shi ya wuce da ita ! "
" bedroom din shi kuma ? " malam ya tambaya cike da rudu dan a iya sannin shi kullum a falo ya ke ganin Zayd na barci
Jinjina mishi kai Moussa ya yi sannan ya ce su tafi ya yi gaba
Ba musu malam ya bi bayan shi su ka nufi part din Zayd
Sallama Moussa ya yi sannan ya shigo falon part din , malam na biye da shi a baya
Zayd kuma , ya na zaune saman sofa ya na latsa wayar shi , cen kassan makoshi ya amsa musu sallamar su
Da sauri malam ya nufo shi ya na fadin " Zayd ina auta , ba abun da ya same ta dai ko "
Ba tare da ya dago kan shi ba ya ce " zauna uncle , ina ga yanzu lokaci ya yi da za ka fadamin gaskiyar abun da ke damun ta "
Wasu yawu malam ya hadiye kafin ya zauna geffen shi ya sunkuyar da kai
Sai da ya dauki lokaci kafin ya fara magana kamar haka " ni dai suna na Ibrahim , cikaken bafulatani da ga gari yola , a cen a ka haife ni , a cen na taso , bayan na cika shekara 23 na baro Garin neman aiki na taho jahar kaduna inda mahaifiyar mu ke da wasu yan uwa na sauka a gidan su , sannu sannu na fara fitowa neman aiki har Allah ya hada ni da wasu abokanai na , Issa da Youssef , a tare mu ka tafi neman aikin har Allah ya sa wani mai kanti ya dauke mu a tare , to dai haka mu ka ci gaba da aikin mu tsawan watanni , bayan wani lokaci a ka kawowa Aunty ta wa wata yarinya da ga ilori za ta zauna a wajen ta ta dinga yi mata aiki , kawai sai na ji na kamu da son yarinyar nan , duk yadda zan yi ta kula ni sai da na yi , a haka har mu ka fara soyayya da ita , har mutanan gidan su ka sani , gudun kar shaitan ya shiga tsakanin mu ba su bata lokaci ba a ka daura auren mu , na kama mana gida mu ka koma cen da zama , bayan shekara guda haka Allah ya ba mu yaro wanda ya ci sunnan Abdoul , abun kamar da wassa sati biyu bayan zuwan shi duniya , uban gida na ya ba ni amanar shagon shi saboda wata tafiya da ta tasso mishi , cikin wani ikon Allah da ma na fara kula da shagon, kasuwanci ya habaka , kullum sai mun ninka ribar jiya , abun ba karamin dadi ya yi wa mai shagon ba , hakan ya sa ya buda min wani shagon daban na dinga kula da shi , abun da ban sani ba Youssef ya na bala'in kishi na, musaman da ya ga uban gidan mu ya ba ni shago na dinga kula da shi ....... "
Katse shi Zayd ya yi da cewa " wait uncle ni fa ban gane inda ka dosa ba abun da na tambaye ka daban , why za ku ba ni wannan labarin ? "
Malam na shirin magana Moussa ya riga shi cewa " kai fa Amir matsalata da kai gajen hakuri , ka tsaya ka saurari abun da zai fada ko "
Jinjina mishi kai ya yi kafin ya kali malam ya ce " uncle ci gaba "