Sashe 14
Exile Princess Love And Power Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ajiye wayar hannun shi ya yi saman bedside drawer sannan ya juyo da kyau ya kali Moussa sannan ya ce mishi " ba haka ba ne , shekara biyu baya , lokacin ka tafi Abuja dibo company , dai'dai na fito da ga cikin gida na hadu da malam ya na tafiya da sauri ko kallon gaban shi ba ya yi, a haka har ya kai min karo ya yi baya zai fadi , bayan na taro shi ya na yi min godiya kuka ya kubce mishi har da hawaye, na yi matukar mamaki ya babban mutun na kuka haka kamar karamin yaro , na so na ki dalilin kukan na shi , sai na ja hannun shi mu ka shigo gidan nan na zaunar da shi sannan da hannu na tambaye shi minene ya ke kuka nan ya ke ce min " Zayd kashe min auta ta za su yi yanzu shekara biyu ina boye ta amma ina ji a jiki na wannan karan sai sun gano mu ban San ya zan yi ba " ni sam ban gane abun da ya ke nufi, sai na tsaya ina kallon shi ina son in karanci abun da ya ke nufi, sai da ya ida kukan shi sannan ya riko hannu na ya ce min " don Allah Zayd ina son in roke ka wata Alfarma " jinjina mishi kai na yi , ina kallon shi ya mike tsaye ya dawo gaba na ya zube saman guyiwowin shi ya ce min " don Allah Zayd ina son ka auri Inaya " a rude na mike tsaye ina fadin " what aure ? " mikewa malam ya yi ya na zaro idanu ya na kallo na ya ce " Zayd, dama ka na magana ? " ban amsa mishi tambayar shi ba na ce " uncle yi hakuri gaskia babu aure a sha'anin rayuwa ta bare kuma wannan yarinya ta yi min kannan ta " komawa ya yi ya zube saman guyiwowin shi ya riko kafafuna ya roke ni da na yarda na aure in ba haka ba komai zai iya faruwa da ita kuma duk abun da ya faru da ita da hannu na a ciki tun da na samu damar ceton rayuwar ta amma na ki duk ya bi ya kashe min jiki ba yadda zan yi na yarda , a ranar a ka aure na da ita, limamin massalaci ya zama waliyi na, shi kuma malam na ta na biya sadaki a ka aura mana aure , duk lokacin da na tambayi malam dalilin da ya sa a ka aura min ita sai ya ce min in bari in lokacin ya yi zan sani , dalilin da ya sa na ce yanzu ta dawo gaba na na dinga ganin ta ko zan gano dalilin da ya sa malam ya aura min ita " ya kai karshen ya sauke ajiyar zuciya ya dan lumshe idanun shi dan ba karamar wuya ya sha ba wajen yin wannan maganar duka
Jinjina kan shi Moussa ya yi kafin ya ce " yanzu me ka ke tunani a kai ? "
" duk yadda a ka yi akwai wanda ke bibiyar rayuwar ta , ka manta ranar nan ta na zaune ta fara sakin kara kamar wadda a ka dauke da karfi , wai ba ka lura da wasu abubuwa da ta ke kamar mara hankali "
Dariya Moussa ya yi kafin ya ce " O'O kenan ka na lure da duk wane abu da ta ke "
" of course ba matata ba ce " ya fada a takaice ya na mike wa ya wuce toilet
Da kallo Moussa ya raka shi har sai da shiga toilet sannan ya ce " matar ka ko , to za ka ga yadda zan yi wufff da ita dan rainin hankali "
Sai da ya ida sambatun shi sannan ya mike ya fice ya koma bedroom din shi
Bai jima da fita ba Zayd ya fito da ga cikin toilet ya yi Alwalla sannan ya fito dakin kai tsaye corridor ya baro ya shigo falo ta na nan zaune saman sofa ta na kallon Tv
Har ya yi gaba zai wuce ya tsaya cak a hankali ya juyo ya zuba mata ido
Ta na zaune waje guda kamar kungi ko kifta ido ba ta yi
Slowly ya tako ya tsaya gaban ta ya dan sunkuyo ya na kallon face din ta
Ko motsi ba ta yi kamar wanda ya suma
Yatsun shi biyu ya kai saitin face din ta ya kyasta mata
Da karfi zuciyar ta ta buga ta yi baya ta fadi konce saman sofar ta na nunfashi sama sama idanu a lumshe
Shi duk ya bi ya rude ya rasa mai zaiyi ya tsaya kawai ya zuba mata idanu
Sannu sannu nunfashin ta ya fara dawowa dai'dai
A hankali ta bude idanun ta ta na kallon ceiling din falon
A haka Moussa ya fito ya same su
Ya na ganin su a haka ya saki murmushi cikin ranshi ya ce " me kuma ka yi ma y'ar mutane ? "
Ya na gama fadar haka ya karaso geffen Zayd ya tsaya ya kale shi ya ce " Amir lafya wani abu ka yi mata ? "
Girgiza mishi kai Zayd ya yi ba tare da ya ce komai
Medo da kallon shi kan Inaya ya yi kafin ya kira sunan ta
" Na'am " ta amsa mishi ta na kallon ceiling din
" me ya faru ne ? " ya tambayeta ya na lekon face din ta
A hankali ta fara kokarin dagowa ta gyara zaman ta sannan ta ce " yaya Moussa yi na yi kamar an danne min zuciya, duk ta yi min nauyi "
Murmushi kadan Moussa ya yi kafin ya ce " shikenan ba komai har yanzu ki na jin hakan ? "
Girgiza mishi kai ta yi kafin ta dago kai a hankali
Idanun ta ba su sauka ko ina ba sai cikin nashi, shi ma ita ya ke kallon ta cikin bakin glass din shi
Da sauri ta sunkuyar da kan ta ta takure waje guda
Kai a sunkuye ta ga ya miko mata hannu
Da sauri ta dago kai ta kaleshi ta na son ta yi magana amma ta ki fitowa
A hankali ta medo da kallon ta kan hannun shi kafin ta dago nata slowly ta daura a saman na shi
Dum zuciyoyin su su ka buga lokacin guda , dalilin mi ? Oho su kadai su ka sani
Ta na daura hannun ta, ya janyo ta ta mike tsaye sannan ya juya su ka fara tafiya a hankali ya na rike da hannun ta
Sai da su ka shiga bedroom din shi sannan ya saki hannun da hannu ya mata allamun " ki shiga ki yi Alwalla ki yi sallat sai ki konta "
( WAI DAMA ANA MAGANA DA HANNU 🤔🤔 )
Jinjina mishi kai tayi ba tare da ta ce komai ba
Juya wa ya yi ya fara takawa har ya kai bakin kofar dakin ya tsinci Muryar ta, ta na fadin " a dawo lafya yaya Zayd ! "
Jinjina mata kai kawai ya yi ba tare da ya juyo ba ya ci gaba da tafiyar shi
Ya na fita ita ma ta juya ta shiga toilet din
Shi kuma ya na fitowa ya tardo Moussa zaune saman sofa ya na latsa wayar shi
Ya na ganin shi ya saki murmushi ya ce " na dauka , ka na cen ka cin angoncin ka ka kyale ni nan "
Dan tsaki ya ja ya ci gaba da takawar shi zai bar falon
Dariya Moussa ya yi kafin ya mike ya bi bayan shi da sauri
Su na fitowa harabar gidan Moussa ya kaleshi ya ce " Amir ka gano abun da ke damun ta ne ? "
Sai da su ka fita gidan sannan ya ce " na gano nan gaba "
Jinjina mishi kai kawai Moussa ya yi su ka ci gaba da tafiyar su har su ka isa mosque
Basu dawo gidan ba sai bayan sallar isha, nan su ka isko ta gyara gidan tsab sai kamshin turare ya ke , har da abinci ta girka musu ta jera komai saman dining table
Kallon Zayd Moussa ya na murmushi ya ce " kai da ka cewa mu wuce restaurant mu sayo abinci, madam har ta shirya mana ashe "
Kauda kan shi gefe Zayd ya yi sannan ya ci gaba da takawa ya shiga corridor ya wuce bedroom din shi
Nan ma wajen a gyare ya ke sai tashin turare ya ke , ta share ko ina ta goge ta canja mishi bedsheet
Sai da ta gyara komai sannan ta yi wanka ta sauya kaya ta Haye bed din ta konta
Dan karamin murmushin geffen fuska ya yi sannan ya juya ya bar mata dakin dan ba ya son tada ta
Falo ya fito nan ya ga Moussa saman dining table sai cin abincin ya ke
Chair din da ke fuskantar tashi ya ja ya zauna sannan ya fara serving din kan shi dan shi ma fa yunwar ya ke ji , ya na iya jure komai a duniya amma banda yunwa shi ya sa duk irin fushin da zai yi bazai yi fushi da abinci ba
Bayan ya yi serving din kan shi ya deba a spoon ya kai baki
Sai da ya dan zaro idanu lokacin da ya ji taste din abincin, ba karamin dadi ya yi mishi ba
Duk abun da ya ke Moussa na kallon shi ta kassan ido, cikin ranshi ya ce " tukunna ma sannu sannu sai ta mamaye wannan zuciyar ta ka ta dutse "
Haka su ka ci gaba da cin abincin ba wanda ya ce ma wani kala har sai da su ka ida su ka sha ruwa su ka daura da juice sannan Moussa ya riga shi cewa " Amir gaskia da ga yau na daina cin abincin restaurant baby na zai dinga girka min "
Kallon shi da kyau Zayd ya yi kafin ya ce " wane baby kuma ? "