← Book details Exile Princess Love And Power Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 44

Sashe 32

Exile Princess Love And Power Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri D.P.O ya bi bayan shi su ka isa office din shi ya ce mishi ya zauna
Ba musu D.P.O ya zauna ya na fuskantar doctor ya ce " please doctor me ya same ta ? "

" calm down D.P.O , zan fada maka komai amma zan so in san minene alakar ka da ita ? " doctor ya fada ya na tsare shi da ido

" ban san ta ba, kawai an kawo karar cigiyar ta ne , saurayin sa ya kawo ta ne ya ce na fara kai ta likita kafin na kira familyn ta "

Jinjina kan shi doctor ya yi kafin ya ce " ya yi tunani mai kyau dan na san idan su ka gan ta cikin wannan halin ba za su yi dadi ba "

Da sauri D.P.O ya katse shi da cewa " don Allah doctor fada min me ya ke damun ta ne "

Cikin sanyi doctor ya ce " calm down , zan fada maka , gaskia sai dai ku yi hakuri raping din ta a ka yi , ga Dukan allamu kuma ba sau daya ba har dinki sai da mu ka yi mata , sannan ta zubar da jini dayawa hakan ya jefar da ita cikin doguwar suma , ta yiyu ta tashi ko kuma akasin haka , i'm sorry "

" Ina'lillahi wa'ina illaihi raji'un " shi ne kadai abun da ya ke fitowa da ga bakin D.P.O
Cikin ranshi ya na fadin " kenan shi ya sa governor ya kira ya ce a kashe case din dan ya san dan shi ne ya yi aikin "
Shi a tunanin shi Hafiz ne ya yi hakan saboda shi ne ya kawota sam bai kawo Moctar a rai ba

Ya na a haka ya tsinci Muryar doctor ya na fadin " ya kama ta ku kira familyn ta ku fada musu mun riga da mun yi na mu aikin , yanzu haka ku na iya zuwa ki gan ta an sauya mata daki "

Godiya D.P.O ya yi wa doctor kafin ya mike ya fice office din ya tafi dakin da a ka kontar da Nesrine

Bai fi ten minutes ba ya fito ya kira Moussa ya sanar da shi inda su ke

❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥

( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )

STORY & WRITTEN BY : ANISH

Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

PAGE 22 ❤🔥

STORY 🔥

A hankali Zayd ya juyo ya na kallon D.P.O ya na shirin magana Moussa ya rika shi cewa " D.P.O ka ba ni amsa mana , kun kamo wanda ya yi mata hakan "

" ku yi hakuri bazan iya kama shi ba , umarni a ka ba ni daga sama a kan na rufe case din nan , ko da na san wanda ya yi hakan bazan iya kama shi ba , kuyi hakuri " D.P.O ya fada cikin rarrashi

Da karfi Moussa ya ce " what ? Kun san wanda ya yi mata hakan, ina ruwa na da umarni da ga sama ya yi laifi dole a kama shi ....."

Da sauri Zayd ya dafa kafadar shi ya katse shi da cewa " Diya yi hakuri , abun da ya faru ya riga da ya faru , ko da an kama shi bazai goge abun da ya yi mata ba " ya fada cikin nitsuwa

Katse shi Moussa ya yi da cewa " Amir me ka ke fada haka kennan yanzu ya yi mata hakan ya ci bilis kennan ba za mu dauki wani mataki a kai ba "

Girgiza mishi kai Zayd ya yi kafin ya ce " a'a bai ci bilis ba , ya je shi da Allah , nasan dole ka ji zafin abun da ya faru saboda son da ka ke mata , amma ka san ba laifin ta ba ne abun da ya faru , nasan da wuya yanzu a ce ka ci gaba da son ta bayan abun da ya faru , ina mai baka hakuri a madadin ta "

Ya na kai karshen ya juya ya fara takawa zai bar dakin

Har ya riko handle din kofar ya tsaya ba tare da ya juyo ba ya ce " zan yi magana da doctor , za mu tafi da ita Abuja yanzun nan , za a ci gaba da kula da ita a cen , idan har yanzu ka na da sha'awar auren ta ka min magana zan nema maka auren ta wajen uncle "
Ya na gama fadar haka ya yi ficewar shi ya bar D.P.O da Moussa nan tsaye

Sai da ya tafi sannan D.P.O ya ce da Moussa " ni zan tafi , don Allah ina mai kara ba ku hakuri akan abun da ya faru " sannan shi ma ya ficewar shi

D.P.O na fita Moussa ya zauna saman chair din bakin gadon ya zubawa Nesrine ido

Bangaran Zayd kuma ya na fita ya nufi office din doctor ya sanar dasshi zai kai yar uwar shi Abuja za a ci gaba da kula da ita a cen

Ba musu doctor ya yarda ya sa a ka shirya musu ambulance din da za ta dauke ta

Da ga haka kuma ya baro likitar baki daya ya yi tafiyar shi

After some minutes ya iso gidan malam

Kai tsaye gidan ya shiga ya na sallama , ban ya isko duk mutanan gidan su na zaune harabar gidan sun yi zugum kamar an turo musu mutuwa

A tare su ka dago kai su na amsa sallamar shi
Malam na ganin Zayd ya mike da sauri ya nufe shi ya na fadin " Zayd an gan ta ne ? "

Riko hannun shi Zayd ya yi ya dawo da shi inda ya tashi ya ce " uncle zauna zan yi wata magana "

Ba musu malam ya koma ya zauna dan shi fa yanzu ba ya cikin halin yin jayyaya da shi a kan wani abu

Tsaya wa Zayd ya yi ya na rike da hannayan shi a baya ya zuba musu idanu ta cikin glass din shi

Sai da ya dauki lokaci kafin ya ce " ku kontar da hankalin ku uncle an gan ta , amma sai dai ku yi hakuri ta samu hatsari dalilin da ya sa ma ta kassa dawowa gida , yanzu haka na sa an wuce da ita Abuja za a ci gaba da kula da ita a cen , ina son ku shirya kayan ku nan da two hours zan sa a zo a dauke ku tare za mu koma Abuja da zama "

Da sauri malam ya mike shi da Abdoul ya na fadin " Zayd mu fa ba mu da gida a Abuja idan mun je ina za mu zauna , karatu na da aiki na duk na yi yaya da su ? "

" duk ba damuwa ba ne , ka fadi duk makarantar da ka ke so a Abuja ka fada min zan nema maka admission, batun gida kuma a gida na za ku zauna , ku shirya nan da two hours za a zo daukar ku " ya na gama fadar haka ya juya ya na taku cike da nitsuwa ya bar gidan

Ya na fita Abdoul ya kali malam ya ce " Abba ya za muyi ne , haka za mu bar gidan nan lokaci guda ? "

Malam na shirin magana mama ta mike da sauri ta ce " e tafiya za muyi , wlh duk inda yarinya ta , ta tafi sai na tafi bazan kyale ta wani abu ya sake faruwa da ita " ta kai karshen kuka na kubce mata ta juya da sauri ta shige dakin ta

Ta na barin wajen malam ya kali Abdoul ya ce " to ba yadda za muyi , la shiga kawai ka shirya kayan ka sai mu tafi "

Da to Abdoul ya amsa mishi sannan kowa ne ya kama hanyar dakin shi dan su shirya kayan su

Zayd

Bayan ya baro gidan malam kai tsaye gidan shi ya nufa

Bakin shi dauke da sallama ya shigo falon gidan , kai tsaye ya nufi doguwar sofa ya zauna ya jingina a bayan sofar ya daga kan shi sama sannan ya sa hannu ya cire glass din shi ya ajiye gefe shi ya lumshe idanun shi

Ya na zama Inaya ta fito da ga kitchen ta na rike da tray dauke da kwanonin abinci ta nufi dining room ta ajiye

Ta na juyowa ta ga Zayd a zaune har sai da ta ji tsoro dan ita sam ba ta san lokacin da ya shigo gidan ba

A hankali ta fara takowa ta karaso inda ya ke , ta zauna geffen shi ta na kare mishi kallon cikin ran ta , ta na fadin lalle akwai abun da ya ke damun shi dan yanayin shi ba haka ya ke kullum ba

A hankali ta gyara zaman ta ta konta ta tada kai da cinyar shi ,

A razane ya sauko da kan shi ya bude idanun shi ya na kallon ta , shi sam bai san lokacin da ta iso wajen

Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya mayar da kan shi ya sake lumshe idanun shi , ta kai hannu saman kan ta slowly ya fara shafawa

Ta na jin saukar hannun shi saman kanta ta saki dan karamin murmushi ta ce " yaya Zayd me ya ke damun ka ne ? "

Ba tare da ya bude idanun shi ba ya ce " me ki ka gani ne ? "

" yadda ka fita ba haka ka dawo ba , duk yanayin ka ya sauya , me ya ke damun ka ne "

Gaskia maganar ta ba karamin dadi ta yi mishi cikin zuciyar shi , kennan har ta iya gane yanayin da ya ke ciki lokaci guda haka

" ba komai , ba abun da ya ke damu na kar ki damu "

Da sauri ta katse shi da cewa " a'a yaya Zayd ni na san akwai wani abu da ya ke damun ka amma ba ka son ka fada min "
Chapter 32 · 0% Book details