← Book details Exile Princess Love And Power Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 44

Sashe 15

Exile Princess Love And Power Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariya sosai ya yi sannan ya mike tsaye ya tatare dishes din ya gyara wajen ya meda su kitchen sannan ya dawo ya wuce falo

Sai da ya zauna sannan shi ma Zayd ya taso ya shigo falon ya zauna ba wanda ya ce ma wani ufan har sai da Moussa ya koma bedroom din shi ya bar Zayd nan a falon

Misalin karfe 12 na dare

Ya na konce saman doguwar sofa ya daura hannun shi guda saman goshin dayan kuma saman ciki ya lumshe idanun shi

Ya na a haka ya jiyo takun mutun, a hankali ya ware idanun shi dan dama ba barci ya ke ba kawai ya lumshe idanun shi ne

A hankali ya dago kai ya kali saitin da ya ke jin takun mutun din

Sai da ya dan zaro idanu ganin ta , ta na tafiya a hankali idanu a rufe

Ya na kallon ta har ta shiga kitchen

Da sauri ya mike ya bi bayan ta , ya na shiga kitchen din ya gan ta rike da wuka ta na shirin caka ma kan ta

Dan zaro idanu yayi a dubu dari ya yi kan ta ya karbe wukar har sai da ta dan yanke shi , dan rumtse idanun kadan ya yi ya sake budewa a kan ta

Ta na tsaye waje guda sai tangal tangal ta ke ido rufe

" wai me ya ke damun yarinyar nan ' ya fada cikin zuciyar shi

A hankali ya kai hannu ya dauke ta cak kamar baby ya juya ya baro kitchen din, kai tsaye bedroom din shi ya meda ta ya kontar da ita saman gadon sannan shi ma ya Haye ya konta ya na kallon ta , a haka har barci ya dauke shi

Washe gari

Misalin karfe 4 na safe ya farka da ga barcin shi
Ya na bude idanu su ka sauka a kan ta , ta juyo su na fuskantar juna ta na sauke nunfashi a hankali

Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya juya a hankali ya sauko kafafun shi kassa sannan ya mike tsaye ya nufi closet din kayan shi ya bude ya dauki kayan shi wandon jeans light blue da t-shirt fara sannan ya fice dakin

Kai tsaye dakin Moussa ya wuce babu ko sallama ya shigo dakin kai tsaye ya wuce toilet
Shi kuma Moussa sai kwana ya ke da ga shi sai short ko shigowar Zayd bai ji ba , sai da ya fara jin saukar ruwa sannan ya bude idanun a hankali ya na motsi

Kallon kofar toilet din ya yi ya ga dakwai dan haske
Murmushi kadan ya saki kafin ya fara karanto adu'ar tashi da ga barci ya mike zaune .............................

❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥

( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )

STORY & WRITTEN BY : ANISH

Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

PAGE 10 ❤🔥

After some minutes ya fito sanye da kayan da ya dauko da ga bedroom din shi

Kallon shi da kyau Moussa ya yi kafin ya ce " ango ! Me kuma ya kawo ka toilet di na "

Ko kallon shi Zayd bai yi ba ya sa kai ya fice bedroom din
Ya na fita Moussa ya mike ya na dariya ya shiga toilet shi ma

Inaya

Misalin karfe 6 ta farka da ga barcin ta
Ta na bude ido ta fara bin dakin da kallo ,

Sai da ta dan dauki lokaci sannan ta mike zaune ta sauko kafafun ta kassa sannan ta mike tsaye ta fara takawa ta nufi toilet

Bai fi five minutes ba da shigar ta toilet ya shigo dakin ya na sallama a tunanin shi ta farka
Sai ya ga dakin ba kowa ga kuma karar ruwa
Sai ya tako bakin gadon ya zauna ya kai saman drawer ya dauki bakin glass din shi ya sa , ya sunkuyar da kan shi kassa

Bayan wasu mintina

Ya na zaune a haka ta fito da ga cikin toilet din ta na daure da towel a kirjin ta

Ta na ganin shi ta saki murmushi , a hankali ta tako wajen trolley din ta ta bude ta dauki uniform din ta

Har ta juya za ta koma toilet wata zuciyar ta ta ce mata " ina kuma za ki koma mutumin da ba gani ba ya ke "

Daga kafadun ta ta yi ta na turo baki nan na ta gaba ta koma ta ajiye kayan na ta saman trolley

Sannan ta kai hannu zame towel din jikin ta, ta koma naked

Hum kamar an ce mishi Zayd dago kai haka ya dago kai dai'dai lokacin da ta saki trolley din ya fadi kassa ta duka ta dauki pant din ta

Da sauri ya rumtse idanun shi ya kauda kai gefe cikin ranshi ya ce " na shiga uku ni Nawfel ba ta ga da mutun ne cikin dakin ko ita ma ta koma makafniya "

Tsab ta shirya war ta cikin uniform din ta, ita ta ma manta da mutun a cikin dakin

Sai da ta gama shiryawa sannan ta dauki towel din da ta yadda kassa ta meda shi toilet sannan ta fice dakin

Duk takun ta ya na jin ta amma ya ki bude idanu ya na tsoron ya sake bude su ya yi arba da ilahirin surrar jikin ta

Sai da ya ji ta bude kofa ta fita sannan ya bude idanun shi slowly ya kali saitin kofar ya sauke ajiyar zuciya mai karfi

Inaya kuma bayan ta fita kitchen ta wuce ta shirya musu breakfast

Sai wajen karfe 7 cib sannan ta baro kitchen din ta shirya musu komai saman dining table sannan ta koma bedroom din ta

Ya na nan zaune inda ta bar shi ko motsi bai yi ba

Bakin ta dauke da sallama ta shigo dakin

Cen cikin zuciyar shi ya amsa mata

A hankali ta tako gaban shi ta tsaya sannan ta Zube saman guyiwowin ta ta ce " ina kwana yaya Zayd "

Jinjina mata kai kawai ya yi bai ce mata komai ba

Murmushi ta yi kafin ta mike ta nufi trolley din ta, ta dauki hijabin ta ta saka ta dauki school bag din ta sannan ta dawo gaban shi dan nesa kadan ta ce " yaya Zayd zan biya wajen Nesrine sai mu ta fi tare "

Jinjina mata kai ya yi kafin ya sa sannu shi cikin aljihun wandon shi ya ciro gudi yan dubu dubu sun kai goma sannan ya mika mata

Dan zaro idanu ta yi ta na kallon kudin ta na tunanin ina ya sami wadanan kudade duka

Ganin har yanzu ba ta karba ba ya sa shi dago kai a hankali ya kale ta
Da sauri ya rumtse idanun shi dan ya tino kallon da ya yi mata ta na naked

Ita kuma ba ta lura ba da ya datse idanun shi ba dan ya na sanye da glass bakake

Ajiyar zuciya ta sauke ta yi murmushi kafin ta ce " yaya Zayd ka barshi kawai "

Girgiza mata kai ya yi ya mike tsaye ya tako a hankali gaban ta ya kara mika mata kudin

Wannan karan ba yadda za ta yi sai da ta karba ta na yi mishi godiya sannan ta saka su cikin bag din ta

Sai da ya ga ta sa kudin cikin jakar ta sannan ya juya ya fice
Da sauri ta bi bayan shi ita ma ta fito dakin

A nan falo su ka isko Moussa ya na zaune saman sofa ya na latsa wayar shi

Ya na dago kai ya gan su ya saki dan murmushi ya ce " baby na har kin fito ? "

Sunkuyar da kai kassa ta yi ta na fadin " ina kwana yaya Moussa "

" lafya lau baby na , sa fatan wannan jarabbaben bai takura miki ba " ya kai karshen ya na medo da kallon shi kan Zayd da ya zauna saman sofa da ke fuskantar tashi

Girgiza mishi kai tayi kafin ta ce " yaya Moussa na shirya muku breakfast din ku , ko ku na bukatar wani abu ne ? "

Girgiza mata kai ya yi kafin ya ce " no baby hakan ma ya isa , sai kin dawo Allah kiyaye hanya "

Da amine ta amsa mishi sannan ta fara takawa ta fita falon

Ya na jin ta fita ya sa hannu ya janye glass din shi ya ajiye su geffen shi ya zubawa Moussa wadanan hazel eyes din shi

Sarai Moussa ya lura da shi amma ya yi banza da shi ya tashi ya nufi dining room ya fara breakfast

Inaya

Bayan ta fita gidan ta fara tafiyar ta cikin minti biyar ta iso gidan su

Da sallama ta shigo cikin gidan

Mama na zaune bakin kofar dakin ta , dai'dai lokacin da Nesrine ke fitowa da ga dakin su ta na sanye da uniform ita ma

Ta na ganin Inaya ta saki wani kyawatencen murmushi da gudu ta je ta rungume ta ta na fadin " na yi kewar ki sosai "

Rungume ta ita ma Inaya ta yi ta na murmushi

Cen su ka tsinci Muryar mama ta na fadin " toh malama kin sake ta, ta zo ta gaishe ni ko ? "

A tare su ka yi dariya su na raba jikin su da na juna sannan Nesrine ta riko hannun ta su ka nufi mama

Ta na isa mama ta bude mata hanayan ta akan ta zo
Ba musu ta fada jikin ta ta na murmushi ta ce " ina kwana mama ? "

" lafya lau autar mama ya ki ke komai dai'dai ko " ta fada ta raba jikin ta da na Inaya

Kallon ta da kyau mama ta yi cike da mamaki ta ce " ban gane ba school za ki koma tun wuri haka "

Murmushi Inaya ta yi kafin ta ce " eh mama yaya Zayd da kan shi ya sayo min uniform ki na gani ? " ta kai karshen ta na juyawa

" shikenan sai kun dawo " mama ta fada ta na murmushi
Chapter 15 · 0% Book details