← Book details Exile Princess Love And Power Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 44

Sashe 13

Exile Princess Love And Power Complete Hausa Novel · about 7 min read

Da sauri ta ce " ina son shi , duk da ban san meye so ba amma har cikin raina na ke jin shi , amma gashi yanzu kun rabu har abada Abba ya zan yi na cire son shi a cikin raina " ta kai karshen kamar ta yi kuka

Dan murmushi yayi kafin ya ce " to ai ba sai kin cire son shi ba a ran ki ba "

" Abba ya zan je gidan wani ina son wani kuma, ni gaskia Abba ba ni son wanda a ka aura min , ko da ba za ku yarda na auri yaya Zayd dan Allah Abba kar ku aura min wanda ba ni so "

" na ga yanzu ki ka ce ki na son ya kuma za ki juya zancen "

Kuka ta saki ta fara harba kafafun ta kamar karamar yarinya ta ce " ni Abba ba shi ba na ce na ke so "

Yar dariya ya yi dan da gangan ya ke jan mata rai

Sai da ya ida dariyar shi sannan ya ce " to shikenan wanene ki ka ce ki na so ? "

" yaya Zayd " ta fada cikin kukan nata

Hannun shi ya kai saman kafadar ta sannan ya ce " yo ai ni ma shi ni ke cewa, shi ne wanda na aura miki , amma tunda ba ki so zan kira shi in ce ba ki son auren " ya kai karshen ya na janye hannun shi da ga saman kafadar ta ya mike ya zai bar dakin

Har ya kai bakin kofar ya jiyo Muryar ta ta na fadin " sa gaske Abba yaya Zayd ku ka aura min ? "

A hankali ya juyo ya na kallon ta
Ta na zaune tsakiyar gadon ta na kallon shi idanun cike da hawaye

Jinjina mata kai ya yi sannan ya sa kai ya fice dakin

Wani irin sanyi ne ta ji cikin zuciyar ta lokaci guda ba ta san lokacin da wani kyakyawan murmushi ya kubce mata ba har da wata yar karamar dariya
Ta dauko pillow ta boye fuskar ta, ta na dariya ta koma ta konta

After one week

Kwana biyar bayan Malam ya fada mata cewa Zayd ne mijin na ta, ya dawo da ga tafiyar da ya yi, a ranar nan kuma a ka kai Inaya dakin mijin ta , tun bayan ta koma gidan shi har yanzu ba ta daura ido saman shi ba, kullum a falo ta ke kwana saman sofa sai in ta na bukatar yin wanka ko alwalla sannan ta ke tashi ta shiga bedroom din shi ta wuce toilet ta yi
Duk kayan ta su na cikin trolley din ta dama ba wasu kaya dayawa ba gare ta gashi ko lefe ba a yi mata ba

Bangaran Nesrine kuma kullum in ta je school sai Hafiz da Moctar sun saka ta gaba a kan ina Inaya amma sai ta ce musu ta koma gidan mijin ta
Nan Moctar ya tada tarzoma a kan karya ta ke ya bar college din cikin fushi shi da Hafiz
Tun ranar ba su sake dawowa college din ba
Abun da ba ta sani ba kullum sai sun zo , sun buya sai in an sauka su ke bibiyar ta amma kullum ita kadai ke tafiya gida har Hafiz ya fara gajiya ya kyale Moctar ya ci gaba da bibiyar ta shi kadai dan shi ya kwalafa rai sosai a kan Inaya

Misalin karfe 5 na yamma

Inaya

Zaune ta cikin falon gidan ta buga uban tagumi kamar ta yi kuka ita kadai cikin gidan

Ta na a haka ta ji a na sallama
A hankali ta dago kan ta, ta amsa sallamar

Zayd ne da Moussa su ka shigo gidan ko wane ya na rike da ledodi

Ta na ganin su ta saki murmushi ta ce " sannu da dawowa "

Moussa ne ya amsa mata ya na murmushi ya na takowa ya ajiye ledodin hannun shi saman sofa sannan ya zauna saman sofar da ke fuskantar ta ta

Shi ma Zayd takowa ya yi ya ajiye ledodin hannun shi saman table sannan ya zauna geffen Moussa ya jingina a bayan sofar ya daga kai ya lumshe idanu shi ta cikin glass din shi

Murmushi ta yi kafin ta mike ta nufi dining table ta bude fridge ta dauko jug na ruwa ta ajiye saman tray da glass biyu
Sannan ta dauko tray ta komo falo , ta ajiye shi saman table ta zuba ruwan cikin glass ta mika wa Moussa
Karba ya yi ya na murmushi ya yi mata godiya

Har ta dauki guda glass za ta zubama Zayd Moussa ya yi saurin cewa " bari ba sai kin zuba mishi ba azumi ya ke "

Dago kai ta yi ta kaleshi sannan ta saki dan karamin murmushi sannan ta mike ta koma saman sofar da ta tasso ta na sunkuyar da kai

Ta na zama ko , Zayd ya mike tsaye ya nufi corridor ya shiga bedroom din shi

Da kallo su ka raka shi ita da Moussa har sai da ya shiga bedroom din shi sannan ta kali Moussa ta ce " yaya Moussa ina ganin yaya Zayd ba ya so na "

Dan murmushi yayi kafin ya ce " haba babyn malam ya isa ma ya ce ba ya son ki kawai aiki ne ya yi mana yawa kwanan nan shi ya sa ki ka ga ba ma yawwan zama gida "

Jinjina mishi kai tayi sannan ta sunkuyar da kai ta fara wassa da dan yatsun ta

Dan murmushi yayi kafin ya matso bakin sofar ya kai hannu ya dauki ledodin da su ka zo da su sannan ya mike ya tako gaban ta ya ajiye mata su sannan ya ce " Ga tsarabar ki nan, sannan ki shirya gobe za ki koma school "

Da sauri ta dago kai ta kaleshi ta ce " yaya Moussa school fa ? Yaya Zayd ya yarda ? "

Jinjina mata kai ya yi kafin ya ce " yes ya yarda mana shi da kan shi ya je ya sayo miki sabon uniform , da sauran abubuwan da za ki bukata "

Da sauri ta mike tsaye ta na tsale ta na dariya kamar karamar yarinya

Shi dai Moussa ya tsaya ya na kallon ta ya na murmushi " she is si innocente " ya fada cikin ranshi dai'dai lokacin da ya ke juya wa zai shiga corridor

Har ya yi nisa ya tsinci Muryar ta ta na fadin " nagode yaya Moussa "

Ba tare da ya juyo ba ya ce " ba ni ya kamata ki yi ma godiya ba "
Ya na gama fadar haka ya ci gaba da takawa ya nufi bedroom din Zayd

Bai mishi knocking ba kawai ya wuce bedroom din kai tsaye

❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥

( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )

STORY & WRITTEN BY : ANISH

Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

PAGE 9 ❤🔥

Zayd

Ya na zaune bakin gadon shi ya na rike da wayar shi amma ya cire bakin glass din shi

Geffen shi Moussa ya tako ya zauna sannan ya ce " Amir ! "

Ba tare da ya dago kan shi ba ya ce mishi " uhmm ? "

" Amir na yi tunanin maganar da na yi maka za ka saurare ni , wai me ya sa duk abun da na fada maka in dai ba ka niya ba baza ka yi shi ba , yanzu sati guda da ka je gidan su yarinyar nan ka dauko ta amma ko kalma daya ba ka taba ce mata ba , ka ce min akwai binciken da ka ke son yi a kan ta, in ba ta zauna kusa da kai ba ta ya za ka yi binciken , Zayd wlh ba na jin dadin abun da ka ke mata , shin minene laifin ta a ciki, ka na ga karama ce sosai ko ba za ka iya soyayya da ita ba ka kula da ita a matsayin kanwar ka mana "

Shi dai Zayd ko dago kai bai yi bare ya ce mishi wani abu

Sai da ya gaji da zubar shi sannan ya ce " Amir ina son in san dalilin da ya sa aka aura maka ita "

Wannan karan sai da ya dago kai slowly ya kale shi kafin ya ce " a kan hakan ni ke bincike "

Dan zaro idanu Moussa ya yi kafin ya ce " ban gane ba kawai malam zowa ya yi ya ce ka aure ta kai kuma ka yarda ? In da ba ka son ta na minene za ka yarda "
Chapter 13 · 0% Book details