← Book details Exile Princess Love And Power Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 44

Sashe 27

Exile Princess Love And Power Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da ya dauki lokaci ya na kallon ta a haka kafin ya kai hannun shi slowly ya janye mata jelar gashin ta

Kamar jira ta ke ya na janye mata ta bude idanu ai ko sai cikin nashi sai da ta ji tsoro lokacin da ta ci karo da Hazel eyes din na shi

Da sauri ta yi baya za ta tashi da ga saman gadon

Hannun ta ya riko ya lumshe idanun shi dan ya san su ne su na bata tsoro cikin wata cool voice ya ce " dawo ina za ki je "

Cak ta tsaya ta lumshe idanun ta ta koma ta konta ta na sauke ajiyar zuciya

A hankali ta juyo da kan ta ta na kallon shi , ganin ya lumshe idanun shi ya sa ta cewa " yaya Zayd lafya ka rufe idanun ka "

Ba tare da ya bude su ba ya ce " no kar ki damu konta ki yi barchi ki "

" to Amma yaya Zayd ka bude su mana in gani "

" ba za ki ji tsoro ba , la ga kin tsorata da farko shi ya sa na rufe su "

Dan matsowa ta yi kusa da shi kadan , ta rage sautin Muryar ta ta ce " ka bude ba zan ji tsoro ba yaya Zayd "

Jinjina mata kai ya yi kafin ya fara bude idanun shi slowly , sai cikin nata dan ita ma shi ta ke kallo

Haka su ka tsaya su ka kurawa juna ido babu ko kiftawa duk sun kassa janye idanun su

" wai me ya ke shirin faruwa da ni ne haka, duk lokacin da na kalli yarinyar nan sai na ji zuciya ta ta yi min wani sanyi, why ? Na ke jin haka , na san a shekaru na ninka nata amma me ya sa ko wane lokaci na ke ganin kamar ta na dai'dai da ni ? " ya fada cikin ranshi ya na tsare ta da wadanan hazel eyes din na shi

Ita cikin ranta cewa ta ke " ban san dalilin da ya sa ni ke maka irin wannan son haka , why kai ma baza ka so ni ba ? " ta na fadar haka ta saki wani cool murmushi ta lumshe idanun ta slowly

A hankali shi ma ya lumshe idanun shi , ba jimawa barci ya yi gaba da su

Washe gari

Misalin karfe 8 na safe , Zayd da Moussa su ka bar gidan , su ka bar Inaya ita kadai ta na ta barci dan yau ba school ba za ta je

Gidan malam su ka nufa , dai'dai sun isa bakin kofar gidan , malam da Abdoul su ka fito da ga cikin gidan su na ta sauri har su ka wuce Zayd da Moussa ba su sani ba

Da sauri Moussa ya taro su ya na fadin " uncle ina zuwa haka "

Juyowa malam ya yi ya kaleshi ya ce " zan je police station na gaji da zaman jiran nan "

Jinjina kan shi Zayd ya yi kafin ya fara takawa ya na rike da hannayan shi a baya ya yi gaba ba tare da ya ce musu komai ba

Da sauri malam da Abdoul su ka bi bayan shi tare da Moussa
A haka su ka jera su ka nufi police station

Sun dauki wajen good 10 minutes su na tafiya kafin su iso police station

Zayd ne ya yi magana officer din bayan ya gaishe da shi ya ce mishi ya na son ganin DPO

Nan officer din ya ce mishi " sai dai ka yi hakuri in kara ce ku ka kawo ni za ku fada ma ba DPO ba "

Cikin sanyi Zayd ya ce mishi " ka yi hakuri ka sada mu da shi maganar ta na da mahimanci sosai "

Fir officer din ya ki ya ce " na fada muku duk karar da za ku shigar ni za ku fada ma DPO ba shi da lokacin kananan case "

Cikin bacin rai Zayd ya ce " an fada maka karamin case ne ya kawo mu , kanwa ta fa ta bata, ina son magana da DPO now ! " ya kai karshen ya na buga desk din da karfi

Da sauri sauran officer din su ka karaso wajen su na fadin " kai malam nan fa ba gidan ku ba ne , ka yi a hankali ko kuma na sa ka cell "

Tsaki Zayd ya ja ya kauda kan shi gefe kafin ya juya a hankali ya fice da ga cikin police station din

Ya na barin wajen malam ya matso ya ce da officer din " yi hakuri yaro zuciya ce ta debe shi , mun zo shigar da kara a kan batar yarinya ta, tun jiya da safe a ka aike ta har yanzu ba ta dawo ba "

Cikin ko in kula ya ce " ya wuce ta bi saurayin ta sun tafi yawon cin duniyar su ku na nan kun damu a kan ta , ta na cen ta cin dadin ta " ya kai karshen ya na dariya
Su ma sauran officer din su ka bushe da dariya

KAI JAMA'A YANZU KO GIRMAN MALAM BAI GANI BA DA YA FADI HAKAN 😔😔

❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥

( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )

STORY & WRITTEN BY : ANISH

Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

PAGE 20 ❤🔥

Maganar ba karamin bata musu rai ta yi ba , da Zayd na wuri ya yi maganar da tuni zuciya ta debe shi ya musu dukan mutuwa , shi fa Zayd irin mutanan nan ne da ba su son raini duk girma kan idan ka ce za ka raina shi to wlh sai dai a dauki gawar ka , dalilin da ya sa ba ya sakewa Inaya fuska dan kar ta ga ranar shi raini ya shiga tsakanin su

Su na tsaka da dariyar su DPO ya fito da ga cikin office din shi ya na sanye da kakin su na soja , ba laifi ya dan lattijantaka , ya na da kyasumba amma ba sosai ba ya na sanye da hular su irin ta sojawa ba a iya ganin gashin kan shi , fuskar shi babu yabo babu falassa

Su na ganin shi kowa ya shiga tai'tayin shi , duk su ka sara mishi su na fadin " sir! "

Bai bi ta kan gaisuwar su ba ya ce " dariyar me ku ke yi haka ? "

Da sauri daya da ga cikin su ya ce " ba komai sir " ya fada cikin girmamawa

Jinjina kan shi ya yi kafin ya kali daya da ga cikin officer din da ke tsaye bakin kofar office din shi ya ce " PDG din Shell Petrolium ya na waje , je ka mishi iso zuwa office di na "

Ya na gama fadar haka ya juya zai koma office din shi , officer din kuma ya mike zai fita

Har ya yi nisa ya jiyo DPO ya na fadin " ya na sanye da jeans black da t-shirt white " sa ga haka ya shige office din shi officer din ya fice

Ya na fita Moussa ya dafe forehead din shi ya ce " Amirrrr ! Ba dai kiran DPO kai tsaye ka yi ba ? "

Da sauri malam ya kaleshi ya ce " me ka ke nufi Moussa "

Cike da rudu Moussa ya kali malam ya na zaro idanu shi ya ma manta da su na tare da malam

Officer din kuma bayan ya fito harabar police station Ya duba dama ya duba hagu bai ga kowa ba

Har ya juya zai koma ya hango wani mutun cen nesa tsaye ya bashi baya ya na sanye da jeans baki da t-shirt fara kamar yadda DPO ya fada mishi ya sunkuyar da kai ya na latsa wayar shi

A hankali officer din ya tako gare shi ta bayan shi ya tsaya ya sara mishi ya ce " Good morning sir "

Ko juyowa Zayd bai yi ba bare ya amsa mishi ya ci gaba da latsa wayar shi

Ganin bai amsa mishi ba ya sa officer din cewa " sir DPO n........" kut maganar ta yanke sakamakon juyowa da Zayd ya yi ya fara takawa ya bar wajen

Officer din sumar tsaye ya yi kennan shi ne PDG din Shell petrolium, tun dazu ya ce ya na son magana da DPO amma su ka raina mishi hankali , yanzu zai iya kai kararshi gaban DPO ma kuma ta zauna shikenan an koreshi ?

Da sauri ya juya ya bi bayan Zayd da har ya kusa shiga police station din
Kafin ya shiga ya tarbo shi ya mara mishi baya

Babu ko sallama Zayd ya shigo police station din kai tsaye ya na sanye da bakin glass din shi , ya rike hannayan shi a baya , ya nufi office din DPO

Officer din nan na farko na ganin shi ya matse fuska ya ce " kai gidan ku ne nan da za ka shigo babu ko sallama "

Da sauri officer din da ke bayan Zayd ya girgiza mishi allamun ya yi shiru

Malam da Abdoul na ganin irin shigowar da ya yi duk su ka bi su ka rude sun ka ce anya wannan Zayd ne , dan fa nan kwarjinin shi ya karu fiye da farko taku ya ke cike da izza da isa kamar shi ne president din Nigeria baki daya

Su na isa bakin kofar office din , DPO ya fito ya na murmushi ya mikawa Zayd hannu ya ce " welcome sir ! "

Kallon hannun DPO ya yi kafin ya dago kai ya kali Moussa , ya juya ya shiga office din DPO ya bar shi nan tsaye

Da sauri Moussa ya karaso wajen ya riko hannun DPO su ka yi musbaha ya na murmushi ya ce " Sorry DPO bai cika gaisawa da mutane ba ne "
Chapter 27 · 0% Book details