← Book details Exile Princess Love And Power Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 44

Sashe 36

Exile Princess Love And Power Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi malam ya yi kafin ya ci gaba da cewa " a haka mu ka ci gaba da rayuwa , ina kula da shagon nan har bayan wasu shekaru Allah ya ba mu kyakyawar yarinya wadda na sakawa sunnan Nesrine , bangaran Youssef kuma kishin nan nashi ya na nan har ya kai wani lokaci ya daina zuwa zaman da mu ke yi bayan sallar isha a cen gida na , hakan bai dame ni ba dan a tunani na aiki ne ya yi mishi yawwa saboda shi ma ya na da nassa ahalin kuma ga shi ya shiga harkar siyassa , bayan shekara uku , Allah ya sake ba mu haifuwar kyakyawar baby kamanin ta sak da na Nesrine , na saka mata sunnan mahaifiya ta wato Inaya , ranar da a ka yi zanan sunan ta , mu na zaune bakin kofar gida ni da Issa da Youssef mu na hira , mu na a haka ingozomar da ta karbi haihuwar matata tun ta Abdoul ta fito za ta tafi , cikin murna na tare ta ina yi mata godiya har na bata dubu biyar na hanya , har ta tafi na dawo , ina zauna tare da su issa kawai sai ganin ta na yi ta dawo , na tambaye ta ko ta yi mantuwa ne na shiga na dauko mata sai ta ce min " a'a ban yi mantuwa ba , ya kamata na sanar da kai , wannan yarinyar da Allah ya baka, ba kamar kowace yarinya ta ke ba , na ji a jiki na ta na da kashin arziki kamar mahaifiyar ta , musaman ga mijin da za ta aura , sannan akwai wani boyayen al'amari a tatare da ita , na ji a jiki na ta na da wata baiwar da Allah ya yi mata dan ganin karshe wani zalinci , ka kula da ita kar ka bari ta fada hannun mara gaskia mai niyar cutar wa , kaddarar ta na gaba , na ga wani batacen bakko mai cike da ayar tambaya , tabas kaddara za ta hadasu , haduwa ta har abada " ta na gama fadar hakan ta juya ta yi tafiyar ta , ni duk cikin abun da ta fada kashin arziki kawai na rike , har da ma Youssef , ashe cikin zuciyar shi dakwai abun da ya shirya , sannu sannu lokaci na tafiya har ya kai Inaya ta kai shekara 7 , kassuwanci na sai habaka ya ke yi , yayin da Youssef ya shiga harkar siyassa ta mugayan mutane masu anfani da tsafi wajen ganin sun yi nassara , har ya kai matsayin minister cikin gida , bayan Inaya ta ci ka shekara 8 wani mumunan abu ya faru da ni , shago na ya kone kurumus babu abun da ya yi saura , wasu sun ce barayi ne , wasu kuma su ce ba mu kashe injin shagon ba , mun tabka babbar assara ni da uban gida na , da ya ke mutumin ya na da kirki sai ya ce Allah ne ya rubuta hakan ya hakura ba komai , ganin bazan iya ci gaba da kula da shagon ba sai na ce mishi ya dauki Abdoul ya dinga taimaka mishi , a lokacin ya na shekara 18 ba musu ya yarda, duk lokacin da Abdoul ya sauko da ga school sai ya tafi shagon wajen aiki , ni kuma na bude wata karamar makarantar islamya inda na ke koyar sa yaran unguwa da kuma nawa yaran , bayan Inaya ta cika shekara 10 Youssef ya tado zancen ya na son ya nemawa yaron shi auren ta a lokacin ta na karama sosai a waje na sai na ki yarda hakan ko ba karamin bata mishi rai ya yi ba , har ya dauki gaba ya bani , wata daya bayan faruwar hakan na je na bashi hakuri dan Allah ya sani da zuciya daya na ke tare da shi tun farko , ba musu ya yarda shi ma ya bani hakuri da cewar shi ne mai laifi ba ni ba , mu na zaune a wajen Inaya ta tardo mu da gudu su na wassa ita da Nesrine , ta na ganin Youssef nunfashin ta ya dauke lokaci guda , ta shiga yin kara kamar dai yanzun nan ta na fadin " Abba shi ne , shi ne ya kone maka shagon ka " cike da rudu na shiga rarrashin ta dan ni ban san abun da ta ke fada ba , ashe dalilin da ya sa Youssef ke son ya aurawa yaron shi Inaya , sun je wajen bokan su ne sai ya ke fada mishi abun da ingozomar nan ta taba fada mana , nan bokan ya ke ce mishi wai matata ita ce silar arziki na tsawan shekaru , kuma duk wanda ya auri Inaya duk kofofin arziki za su bude mishi, sannan ya gani cewa ta na da wasu aljanu na gado da ga wajen mahaifin mamar ta , wadanan aljanu ko shi bai san irin su , dole sai ya kawo mishi Inaya in har ya na son ya tantance wane irin aljinu ne gare ta , duk yadda Youssef zai yi don ya ga ya kai Inaya wajen bokan sai da ya yi amma da Inaya ta sauke idanu saman shi ta ke tserewa ta buya , har ya kai abun ya fara bawa Youssef haushi , ya fara yi mana barazana a kan dole sai na aurawa yaron shi Inaya in ba haka ba ya kashe mu ba ki daya , a lokacin na yi matukar girgiza don na san halin shi ba karamin mugu ba ne in har ya yi niya , cike da tsoro na tatara iyali na cikin tsohon dare mu ka bar gidan , mu ka bar kaduna baki daya mu ka taho kano inda ba mu san kowa ba , a ranar da na roke ka, ka auri Inaya , ranar ina zaune na ga issa ya wuce , cike da mamaki na tsayar da shi na ke tambayar shi ya mutanan gida me ya kawo shi kano kuma , nan take kuka ya kubce mishi lokacin da ya ke sanar da ni cewa bayan tafiyar mu Youssef ya tarda shi ya yi mishi barazana a kan ya fada mishi inda muke sai dai shi kuma bai sani ba , har ya sace mishi yarinyar shi babba ya bawa bokan su ita , dalilin haka ya tsere shi ma ya tafi kwayan su , ya ce min a yanzu haka Youssef ya zama vice-president na Nigeria kuma har yanzu ya na neman mu , jin hakan ba karamar girgiza na yi ba har na baro issa nan tsaye na tafi gida dan na ce musu su shirya yanzu ma mu bar Garin , kawai sai na gan ka , lokaci guda wani tunani ya fado min , idan na aura maka Inaya , ba sai na bar garin ba tun da yanzu aure tsakanin ta da yaron Youssef ba zai yi yu ba , ni a lokacin ban duba nakassar ka ba kamai ina neman ceton ran yarinya ta ne "

Shiru Zayd ya yi kamar mai tunanin wani abu
Yayin da Moussa ya zuba mishi ido ya na kallon shi , ya na son ya karanta yanayin sa

Cen kuma sai ya dago kai ya kali malam ya ce " uncle zan iya sannin sunnan yaron da ku ke magana a kan shi "

" e sunan shi Sudais " malam ya fada

❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥

( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )

STORY & WRITTEN BY : ANISH

Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

PAGE 24 ❤🔥

Mikewa tsaye Zayd ya yi ya shiga cikin bedroom din shi ya rufe kofar

Ya na shiga Moussa ya mike tsaye shi ma ya ce wa malam " uncle ni zan tafi "

Shi ma malam mikewa ya yi ya na fadin " mu je to , ni ma wajen Nesrine din na ke son zuwa "

Dan murmushi Moussa ya yi ya na sunkuyar da kai dan malam ya gano shi
A tare su ka jera su ka fito part din sannan su ka sauko falon kassa

Zayd

Tsaye ya ke bakin gadon shi ya zubawa Inaya da ke konce saman bed din shi ido , kamar mai barci

Dogon nunfashi ya ja kafin ya karaso bakin gadon ya zauna ya na ci gaba da kallon ta ya rasa dalilin shi na yin haka

Ya dauki wajen good 30 minutes a haka kafin ya ga ta fara motsi ta na son tashi

Bai motsa ba ya ci gaba da kallon ta , har ta bude idanun ta , ta na kallon ceiling ta kassa motsi

A hankali ya matso kussa da ita ya kai hannu saman kumatun ta ya ce " are you okay ? "

Kallon shi ta yi cikin ido ta ce " yaya Zayd me ya faru ne ? "

" nothing Mimi , ya jikin na ki ? " ya fada ya na taimaka mata ta zauna ta jingina a bayan gadon

Dan murmushi tayi kafin ta ce " yaya Zayd ni fa lafya lau na ke "

" kin tabbata ? " ya fada ya na daga mata gera guda

Murmushi mai dan sauti ta yi har sai da dimple din ta ya lotsa , sannan ta jinjina mishi kai allamun e

Geffen ta ya dawo shi ma ya zauna ya jingina a bayan gadon sannan ya kai hannu ya dauki remote ya kunna Tv din gaban su

Sannan ya kale ta ya ce " za ki kali cartoon ? "

Girgiza mishi kai ta yi kafin ta ce " yaya Zayd ni film na ke son kallo " ta fada cikin shagwaba

Jinjina mata kai ya yi , ya kali Tv din ya na neman chanel din da su ka saka film a yanzu

Cikin sa'a ko first chanel da ya saka , su na haska wani film na Avengers mai dadi

A tare su ka kali film din har sai da ya kamala dai'dai an fara kiran sallat
Chapter 36 · 0% Book details