← Book details Exile Princess Love And Power Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 44

Sashe 6

Exile Princess Love And Power Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jinjina mishi kai kawai ta yi ta ci gaba da tafiyar ta

Su kuma juya su ka bi bayan ta, ba yadda Zayd ya iya dole ya hakura ya bi bayan shi su ka tafi

Tun da su ka kamo hanya ya ke kallon ta ta cikin glass

Ita kuma sai wasu juye'juye ta ke ta na halba kafa ta na wassa yadda kassan me shekara biyar haka ta ke

Shi kuma Zayd wannan abun da ta ke ya na yawwan tuno mishi da kanwar shi dan ita ma haka ta ke da rawan kai

Kawai sai ya tsinci kan shi ya na jin wani bakon yanayi , cikin zuciyar shi ya ce " she is so cute and innocente why malam zai aura min ita da karancin shekarun ta haka , ya kamata na tambaye shi dalilin shi na yin hakan "

Sai magana ya ke cikin zuciyar shi har su ka karaso sangayar Malam bai sani ba, sai da Moussa ya kai hannu ya taba shi ya na fadin " Amir ba ka ji ne malam na gaida ka ? "

A dan razane ya juyo ya kali Moussa sannan ya meda kallon shi kan Malam da ke zaune saman tabbarma sanye da manyan kaya ga Inaya geffen shi ta rungume shi ta na murmushi

Dan murmushi malam ya yi kafin ya ce " malam Zayd tunanin mi ka ke haka "

Girgiza mishi kai kawai Zayd ya yi allamun ba komai sannan ya dawo da kallon shi kan Moussa ya mishi allamun su tafi

Jinjina mishi kai ya yi sannan ya kali malam ya ce " malam za mu wuce sai mun dawo "

Dan murmushi malam ya yi ya ce " shikenan Allah kiyaye hanya , Auta baza ki raka su ba " ya fada ya na medo da kallon shi kan Inaya da ke konce a jikin shi kamar baby

Cikin shagwaba ta ce " Abba yanzu fa su ka rako ni , sannan kuma na sake rakiyar su , ni gaskia babu inda zan je "

Malam na shirin magana ya ga Zayd ya kama hannun Moussa ya ja shi su ka bar wurin

Ta na kallon su ta kassan ido har su ka bar wajen sannan ta mike da ga jikin malam ta ce " Abba , yaya Zayd sunnan shi ne hakan na gaskia ko "

Jinjina mata kai malam ya yi ya na son ya ji abun da za ta cewa

" to amma Abba me ya sa yaya Moussa ke kiran shi da Amir , Amir ai ya nufin yarima " ta fada ta na kallon malam

Shi kuma malam juya kan shi ya yi ya kali su Zayd da su ka yi nisa cikin tafiyar su
Ba tare da ya juyo ba ya ce " ni ma ban sani ba, halan sunnan da ya ke kiran shi ne da shi lokacin su na kanana kin San ba dole sai dan sarki ba a ke kira da Amir "

Cikin ranshi kuma ya na tambayar kanshi shin wanene assalin Zayd din da su ka sani

( TOOOO ! MU MA DAI MU NA SON MIJI WAYE AINAHIN ZAYD DIN NAN 🙄 )

Haka ta zauna wajen malam ta na ta zuba mishi shagwaba shi kuma ya na biye mata sai da su ka ga magriba ta gaba to sannan su ka tashi su ka koma gida a tare , ta na rike da hannun shi ta na wassa da shi

( Ita dai wannan yarinyar da wuya ta zauna ba ta motsi 😑😑 )

Bayan sun koma gida , da kanta ta debo ma malam ruwa cikin buta ya yi Alwalla sannan ya tafi mosque

Bayan ya fita ita ma debo ruwa ta yi Alwalla ta koma bedroom din su dan ta yi sallat

Ta na shiga dakin ta tarda Nesrine ta na zaune saman dadduma ta daga hannayan ta sama ta na adu'a

Dauko daddumar ta Inaya ta yi ta zo ta shinfida geffen Nesrine sannan ta tada sallar ta
Ba su tashi da ga kan daddumar sai da su ka hada da sallar isha su ka yi a tare

Bayan sun ida Nesrine ta mike ta nade daddumar ta ta mayar da ita wajen ta sannan ta fito da ga dakin

Ta na fitowa ta ji sallamar Abdoul
Dum ta ji gaban ta ya buga dan ta san da wuya ya kyale ta bai mata fada ba

Kamar ko ta sani da sauri ta juya za ta koma dakin su ya kira sunan ta

Wasu yawu ta hadiye a hankali ta juyo ta ce " na'am "

Takowa ya yi ya zo gaban ta ya tsaya sannan ya ce " su waye samarin nan da na gan ku a tare "

Sunkuyar da kai ta yi , Cikin in'ina ta ce " ni ma ban san su ba kawai sun tseda mu ne saman hanya wai mu je su rage mana hanya "

Jinjina kan shi ya yi sannan ya ce " shikenan nan gaba kar ku sake tsaya wa ko sun muku magana ku kyale su "

" to yaya Abdoul " ta fada ba tare da ta dago kai ba dan tsoron ta ke ji ya wanke ta da mari

Shi kuma tsaya wa ya yi ya kare mata kallo da kyau ya ga yadda ta ke ta rawar jiki kamar ya ce zai dake ta

Sai da ya dan jima a haka sannan ya juya ba tare da ya ce komai ba ya shiga bedroom din shi

Ita kuma ta na jin ya fara takawa ta dago kai ta ga ya nufi dakin shi ta sauke ajiyar zuciya har da dafe saitin zuciyar ta ta na jan nunfashi a hankali

Sai da ta nitsu da kyau sannan ta kama hanyar kitchen

❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥

( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )

STORY & WRITTEN BY : ANISH

Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

PAGE 4 ❤🔥

Da sallama a bakin ta shigo kitchen din, nan ta isko mama gaban murhu, har ta gaba girki

Dan juyo wa mama ta yi ta kali Nesrine sannan ta ce " lafya idanun duk sun kumbura haka ? "

Ta na shirin magana ta tsinci muryar Inaya ta na fadin " kuka ta yi shi ya sa "

A tare duk su ka jiyo su ka kale ta
Ta na tsaye bakin kofar kitchen din ta na sanye da doguwar riga mara nauyi ta saka dan karamin hijab zuwa kirji

Hararrar ta Nesrine ta yi kafin ta ce " tooo malama miye ruwan ki a ciki ? "

Hannayan ta duka biyu Inaya ta sa ta rike kugun ta, ta ce " da ruwana , sai dai ki yi abun da za ki yi " ta kai karshen ta na murguna mata baki

Da sauri Nesrine ta dauki wani plate ta juya za ta bugawa Inaya

Da gudu Inaya ta juya ta bar kitchen din ta na kara

Ita ma Nesrine bayan ta ta biyan ta ta na fadin " yau sai na yi maganin ki "

Inaya kuma ido a rufe ta yi da gudu za ta bar gidan

Har ta kai bakin kofa ba ta sani ba, kawai sai ji ta yi ta bugi wani abu da karfi ta yi baya za ta fadi ta na sakin kara mai karfi, wanda ya sanya shi toshe kunnuwan shi da duka hannayan shi biyu

Cak Nesrine ta tsaya ta na kallon su ta na zaro idanu

Malam ne da Zayd su ka shigo gidan sai da su ka yi sallama amma Inaya ba ta ji su ba , har sai da ta bugi kirjin Zayd da karfi

Shi kuma ya kassa taro ta dan ya na tsoron ya taro ta wani ya lura da hakan ya yi mishi wata magana da za ta bata mishi rai shi ya sa ya kyale ta ta fadi

Inaya kuma ta na faduwa kan ta ya bugu dum ga kassa har sai kassar ta dan girgiza

Da gudu Nesrine ta saki plate din hannun ta ta nufo ta da gudu ta na fadin " Inaya, Inaya , Inaya " kamar ta yi kuka

Shi ma malam da ke tsaye geffen Zayd da gudu ya yi kan ta ya talabo ta ya na kiran sunan ta

Ina ita ko jin su ba ta yi sai kuka ta ke kamar karamar yarinya

Ganin yadda su ka bi su ka rude ya sa shi kauda kan shi gefe ya saki dan siririn tsaki

A hankali ya fara takowa inda ta ke konce ta na kuka

Dukowa ya yi gaban ta, ya sanya hannayan shi duka biyu ya dauke ta cak kamar baby ya mike tsaye sannan ya nufi tabbarma da ya gani a shinfide kussan dakin Abdoul

Da sauri malam ya bi bien shi , ita kuma Nesrine ta tsaya ta na kare mishi kallo cikin ran ta, ta na tunanin ya akayi ya san tabbarma ta na cen wajen

Malam kuwa bai kawo komai a ran shi ba dan ya san akwaye makafi dayawa da su ke aiki kamar ma su idanu ba mamaki ya hadace inda su ke zama kullum shi ya sa ya nufi wajen kai tsaye

( HAKAN NA NUFIN MALAM YA SAN ZAYD BA KURMA BA NE AMMA BAI SAN SHI BA MAKAHO BA NE 🤔 )

Sai da ya karaso wajen tabbarma sannan ya kontar da ita a wajen ya koma gefe ya zauna , ita kuma har yanzu kuka ta ke kamar baby ba ta ma san an dauke ta ba

Ya na kontar da ita malam ya karaso wajen ya zauna geffen ta ya talabo kan ta ya zaunar da ita ya rungume ta ya na fadin " ya isa haka auta daina na kukan nan haka kar ki janyo wa kan ki ciwo "

A hankali ta fara rage sautin kukan ta ta na hadiyar zuciya

Ta na a haka ta ji an tabo mata kafar ta

Ta na konce a jikin malam din ta dago kan ta ta kale shi
Chapter 6 · 0% Book details