← Book details Exile Princess Love And Power Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 44

Sashe 41

Exile Princess Love And Power Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cike da rudu Moussa ke kallon Abdoul ya ce " Abdoul ni fa ban ga Inaya a wajen da mu ka dauko Zayd, ko dai ta na cikin motar shi "

Girgiza mishi kai Abdoul ya yi kafin ya ce " ni da kai na Zayd ne kawai na gani a wajen , sam tunani na bai kawo Inaya ba ta wajen "

" kai dan Allah ku min bayani yanda zan gane, ina Inaya ta ke " mama ta fada ta na daga murya kadan

A tare Moussa da Abdoul su ka kale ta su ka ce " mama, an sace Inaya "

Sannan Moussa ya daura da cewa " tabass sace ta a ka yi , nassan wajen ceton ta ne Zayd ya ji ciwo "

Bai gama rufe bakin shi ba, Nesrine ta saki wata irin razananiyar kara ta na kiran sunan Inaya , mama kuma sumar tsaye ta yi dama abun da malam ke gudu kenan yau ya tabata

Da sauri Moussa ya nufi Nesrine ya rungume ta dan ya lura ta na neman ta fita cikin hayacin ta , haka ya shiga rarrashin ta har sai da doctor ya fito

Da sauri Abdoul ya nufe shi ya na tambayar shi ya jikin Zayd

" adu'ar ku ya fi bukata a yanzu , mu mun yi na mu aikin " ya na gama fadar haka ya yi gaba zai bar wajen

Sakin Nesrine Moussa ya yi ya taro doctor ya ce " doctor ban gane abun da ka ke fada ba "

" sorry , ya shiga doguwar suma saboda jinin da ya zubar , ga shi ya samu mumunan bugu a kai , mun yi mishi karin jini da duk wani abu da zai bukata amma ba na tunanin zai iya tashi , da wuya ya wuce yau ko gobe , adu'a kawai za ku yi mishi " ya na kai karshen ya bar wajen

Sumar tsaye Moussa ya yi ya shiga girgiza kan shi ya fara juyawa waje guda kamar zarare ya na fadin " na shiga uku , wlh Malik kashe ni zai yi , yanzu shikenan Amir mutuwa zai yi , Kaiii, don Allah in mafarki na ke ku tashe ni " ya kai karshen kamar zai yi kuka

Dafa kafadar shi Abdoul ya yi ya na fadin " ka kontar da hankalin Moussa da izinin Allah zai tashi adu'a kawai za mu yi mishi "

" kai Abdoul akwai matsala in Amir bai tashi ba , wlh akwai matsala , cire min kai kawai Malik zai sa a yi "

Shi dai Abdoul sam bai gane sambatun Moussa ba sai rarrashin shi ya ke , ya na kontar mishi da hankali

Mama da Nesrine kuma ba su da bakin magana dan su ma cikin irin halin Moussa su ke , ba malam ba Inaya to su na ina ? Tashin hankali ba a sa maka date

Ga Zayd konce tsakanin rai da mutuwa , an sace malam da Inaya a rana guda duka wane tashin hankali da me ya yi kama

❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥

( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )

STORY & WRITTEN BY : ANISH

Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

PAGE 28 ❤🔥

After some hours

Inaya

Konce ta ke cikin wani daki baki kirin babu haske ko kadan ciki ko Windows babu

A hankali ta fara motsi ta na karanto kalmar shahada , sannan ta ware idanun ta slowly amma ba ta ganin komai

Mikewa zaune ta yi ta dan jujuyawa ta na fadin " yaya Zayd ka na ina "

Kamar da ga sama ta jiyo Muryar malam ya na fadin " Auta ke ce "

Dum ta ji gaban ta ya fadi nan take kuka ya kubce mata ta na fadin " Abba , Abba , ina ka ke Abba "

" kontar da hankalin ki Auta , kar ki motsa " ya fada mata ya na tashi ya fara laluban ta cikin wannan uban duhu

Cikin sa'a ko ya gano ta da sauri ya Zube saman guyiwowin shi ya na fadin " auta, me ya kawo ki nan "

Ta na jin ya tabo ta ta fada jikin shi ta na kara sautin kukan ta ta ce " Abba , ni ma ban sani ba, mu na tafe ne ni da yaya Zayd, wata mota ta tsaya a gaban mu wani katon mutun ya fito ya dauke ni , sai yanzu da na bude ido "

Rungume ta tsam malam ya yi ya na fadin " ki kontar da hankalin ki , va abun da zai faru kin ji ko "

Kassa amsa mishi ta yi saboda kukan da ta ke , haka ya shiga rarrashin ta har ya samu ta yi shiru su ka yi zugum waje guda kowa da irin abun da ya ke sakawa a cikin zuciyar shi

After two days

Kwana uku yanzu kennan da kontawar Zayd doguwar suma , a kullum bugun zuciyar shi kara rayuwa ya ke tun likoci na san ran zai tashi har ya kai sun daina , Moussa kuma kamar ya yi hauka don ya san idan Zayd bai tashi ba tabass shi ma sai ya bi shi
Adu'a babu dare babu rana ya ke samu da ga wajen mama dan ba abun da ke tada ta da ga saman sallayar ta , kullum ta na cikin yi wa ahalin na ta adu'a
Ga shi kuma har yanzu malam da Inaya shiru , sun je police station din amma abun mamaki sai dai a ce musu su je gobe su dawo , sau uku Abdoul ya na zuwa police station kai kara amma kullum su ce mishi ya dawo gobe har ya gaji ya bar zuwa ya mika al'amarin wajen ubangiji , ko da ma su satar mutane ne za su kira su
Nesrine ma ba a bar ta a baya ba wajen yi ma yan uwan ta adu'a , dan yanzu ta samu dauki amma ba sosai ba , a yanzu kuma ita ke debe ma Moussa kewa ta na taya shi hira duk lokacin da su ka je kai mishi abinci likita dan har yanzu su na cen shi da Zayd
In mu ka leko malam da Inaya kuma , tun ranar a ka sa su cikin wannan dakin , ba a sake waiwayar su ba , abinci ma sau biyu a rana a ke basu, shi ma bai fi ka yi spoon biyu ko uku ba
Amma a haka har su na samun damar su mika kukan su ga ubangiji, kullum cikin adu'a su ke ita da malam babu fashi

Misalin karfe 10 na safe

Yau dai kwana hudu da faruwar wannan abun

Inaya

Konce ta ke ta tada kai da cinyar malam, ya sa hannu ya na shafa mata kai ya na karatun kur'ani

Su na a haka su ka ga an bude kofar dakin
Da sauri malam da Inaya su ka datse idanun su dan sun saba da duhun dakin

Ba su kai ga bude idanun su ba su ka ji an dauke su an mikar da su tsaye a na fadin " mazza ku fita "

Riko hannun Inaya malam ya yi su ka fito wannan dakin

A hankali su ka fara ware idanun su , su na bin wajen da kallo
Wani katon falo ne , dauke da duk wasu kayan more rayuwa , da ga sofa har zuwa su Tv , amma komai black colour ne dakin duk zagaye ya ke da irin wadanan gardin da ya dauke Inaya sun kai su goma , kowa sanye da bakaken kaya fuskar a daure tamau kamar hadari , sai shan tsami suke

Cen su ka hango wani bokan zaune tsakiyar falon ga wata kwariya cike da wasu ruwa jajaye a gaban shi, sai wani karatu ya ke mara dadin ji

Su na tsaye su na kallon shi wani ya turo malam ya yi gaba zai fadi
Da sauri Inaya ta taro shi ta na fadin Abba

Riko hannun ta ya yi ya na fadin ba komai , sannan ya mike su ka karaso cikin falon

Cak malam ya tsaya ya na zaro idanu , zuciyar shi na duka uku uku
Ba komai ba ne ya gani face Youssef , ya yi wani zaman kasaita saman sofa geffen bokan ya na kallon malam ya na sakin wani makirin murmushi

Ya na ganin malam ya tsaya ya bushe da wata shegiyar dariya kafin ya mike tsaye ya karaso gaban malam ya tsaya ya na fadin " ohhhh Ibrahim , yaushe rabo " ya kai karshen ya na rungume malam

Shi dai malam ya kassa motsi sai kallon waje guda ya ke ya na faman muzurai da ido

Ganin bai motsa ba ya sa Youssef sakin shi ya yi baya kadan ya kali Inaya,
Wani cool murmushi ya saki kafin ya ce " my daughter gaskia kin girma ba ki dai manta da uncle din ki ba " ya kai karshen ya na kai hannu zai taba fuskar ta

Cak ya ji malam ya damko hannun shi
Da sauri ya dago kai ya na kallon malam

Cikin dakiya malam ya ce " kar ka kuskura ka taba min yarinya ta "

Murmushi Youssef ya yi kafin ya kauce hannun shi ya juya ya koma sofar da ya taso ya zauna ya kali bokan ya ce " Barbushi ga yarinyar da na ke baka labarin ta "

Dago kai barbushi ya yi kafin ya ce " tabass ita ce , dan ina jiyo kamshin arzikin ta , amma auren ka da ita ba zai yi yu ba "

Mikewa tsaye Youssef ya yi ya na fadin " what kamar ya bazan iya auren ta ba "

Barbushi na shirin magana malam ya riga shi cewa " Youssef kenan dama ba Sudais ka yi niyar aura ma ita ba , kai ne za ka auri yarinyar da ka yi jika da ita, saboda me Youssef , kawai saboda abun duniya , wlh ka ji tsoron Allah "
Chapter 41 · 0% Book details