← Book details Exile Princess Love And Power Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 44

Sashe 29

Exile Princess Love And Power Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jingina bayan shi Zayd ya yi a jikin sofar ya lumshe idanun shi ya ce " Diya na san wannan duka, amma ba yadda zan yi kassan ba zan iya tafiya na bar yarinyar nan ba ko "
Ya kai karshen ya na bude idanun shi ya kali Inaya da ta sharar barcin ta kamar babu ita a wajen

" shikenan yanzu ina son ka fada min za ka koma masarauta ko kuma ba za ka koma ba " Moussa ya tambaye shi

Dawo da kallon shi ya yi kan Moussa kafin ya ce " za mu koma Diya, za mu koma amma ba za mu zauna ba , tafiyar tsaye za mu yi "

Ya na gama fadar haka Inaya ta fara motsi ta na son tashi

A tare shi da Moussa su ka dawo da kallon su saman ta

A hankali ta ware idanun ta , ta fara karanto adu'ar tashi da ga barci , ta fara bin wajen da kallo

Idanun ta na sauka kan Zayd ta saki wani dan murmushi ta mike zaune ta kai hannun ta guda ta na murza idon ta cikin shagwaba ta ce " yaya Zayd tun da safe na ke ta jiran ku ku dawo mu yi breakfast har kwana ya dauke ni "

Murmushi Moussa ya yi kafin ya ce " sorry baby na , wlh wani aiki ne ya tseda mu "

Murmushi ta yi ta na bude idanun ta ta kai kallon ta kan Zayd da ya tsare ta da wadanan hazel eyes din na shi ta cikin glass

Ta na shirin magana wayar Moussa ta fara ringing

Da sauri ya sa hannu cikin aljihu ya fido ta ya na kallon screen , dago kai ya yi ya kali Zayd da ya kurewa Inaya kallo

Daukar kiran ya yi ya kai ga kunne ya na sallama

A daya bangaran kuma amsa mishi sallamar shi DPO ya yi kafin ya ce " sir an gano inda yarinyar nan ta ke "

Da sauri Moussa ya mike tsaye ya ma manta da ya na gaban Inaya ya ce " da gaske ta ina to "

" sir muna jiran ka babban likitan gari " ya na gama fadar haka ya katse kiran

Kallon screen din wayar ya yi ya ce " babbar likatan gari kuma , me ya kai su cen "

Ya na gama fadar haka ya dafa kafadar Zayd ya ce " Amir an gano inda ta ke amma ya ce min su na likita "

Lumshe idanun shi ya yi a hankali kafin ya sake bude su ya mike tsaye ya kali Moussa ya ce " shikenan mu tafi za musu san abun da ya faru "

Ya kai karshen ya na medo da kallon shi kan Inaya ya ce " yo hakuri za mu je mu dawo ba za mu jima ba "

" shikenan yaya Zayd a dawo lafya , amma in za ka dawo ka biyo min da sweet " ta fada cikin shagwaba

Da to ya amsa mata kafin ya juya ya fara takawa ya fice falon Moussa na biye da bayan shi

Su na fita ta tashi ta shiga kitchen dan ta shirya musu abun da za su ci

Zayd kuma bayan sun fita kai tsaye babban Hospital su ka nufa
Ba yin da Moussa bai yi ba a kan su tafi da motar su amma ya ki ya ce da kafa za su tafi

Sun dauki wajen good 30 minutes kafin su iso Hospital din da DPO ya fada musu

Su na isa Hospital din su ka tardo DPO a reception ya na jiran su

Ya na ganin su ya mike ya ce da Zayd " sir mu karasa dakin ta , anyi mata duk wani abu da za ta bukata , amma ta shiga doguwar suma "

Da sauri Zayd ya kaleshi ya ce " what doguwar suma ? Me ya faru da ita ne "

" zai fi idan ka gan ta za ka gane abun da ya faru da ita " Ya na kai karshen maganar shi DPO ya yi gaba

Da sauri Zayd da Moussa su ka bi bayan shi duk da bai cika tafiya da sauri ba yau sai da ya yi ta

Da sallama bakin su , su ka shigo dakin da DPO ya kawo su

Cen su ka hango Nesrine konce saman gado ta na sanye da wata riga blue zuwa guyiwa, hannun ta sanye da catheter a na mata karin jini , fuskar ta duk ta kumbura kamar wadda ta kwana ta na kuka , ga wasu allamun yaga a hannayan ta kamar wadda ta yi fada da mage

Cike da rudu Moussa ya kali DPO ya ce " me ya same ta haka ? "

Cikin girmamawa ya ce " sorry sir ta rasa jini dayawa dalilin da ya sa ta shiga doguwar suma "

Cikin tsawa Moussa ya katse shi da cewa " How ? ta ya ta rasa jini haka , ba dai kokarin kashe kan ta ta yi ba ? "

Dan jinkirtawa DPO ya yi kafin ya ce " sorry sir , raping din ta a ka yi , allamu sun nuna ba sau daya ba a........"

Bai karasa maganar shi ba sakamakon katse shi da Zayd ya yi da cewa " me ku ke jira har yanzu ba ku kamo wanda ya yi hakan ba ? " ya fada cike da nitsuwa

Sunkuyar da kai DPO ya yi dan bai da amsar da zai ba shi

( TOOOO , KO WA YA YI WA NESRINE WANNAN AIKI HAKA ? 😭😭😭 )

ONE DAY BEFORE

NESRINE

Misalin karfe 8 na safe Nesrine ta farka da ga barci da ya ke yau week-end ne ,
Bayan ta share gidan ta yi duk wani aiki na gidan da ya kamata , wajen karfe 9 ta shiga wanka sannan ta fito ta shirya cikin riga da skert ta zauna cikin dakin ta ta na karatu

Ta na tsaka da karatun ta mama ta shigo dakin ta na sallama

Amsa mata sallamar mata Nesrine ta yi ta na dago kai

Murmushi mama ta yi kafin ta ce " abokiyar fadan ta tafi ko ? "

Murmushi ita ma Nesrine ta yi kafin ta ce " mu daman ba fada ne mu ke yi ba mama , ita ce dai ta cika tsokana ta "

" ke kuma ba ki da hakuri gashin ai yanzu ba ta nan "

" ina kewar ta sosai mama har mafarkin ta na yi jiya wai ta na da ciki " ta kai karshen ta na bushewa da dariya

" yanzu ke Nesrine takurar da ki ke ma auta har ya kai ki yi mafarkin ta da ciki , to minene matsalar a ciki ai ni abun da na ke son gani ma kenan "

" laaaaa mama abun da ki ke son gani fa ? Tabbb ai in wacen tsohon makahon ya taba min kanwa sai na kai karar shi , da wasu idanun shi kamar na mujiya "

Dariya mama ta yi kafin ta ce " ai gwara ita ta na da makahon mai idanun mujiya ke fa har yanzu gaban iyayen ki ki ke, ga kanwar ki cen gidan mijin ta "

Turo dan bakin ta ta yi cikin shagwaba ta ce " yo ai mama komai lokaci ne , ni ma lokacin nawa na zuwa "

Murmushi mama ta yi sannan ta ce " shikenan Allah ya kawo shi wannan lokacin , yanzu dai tashi ki je ki yo min cepane tun rana ba ta fito ba "
Ta na gama fadar haka ta juya ta bar dakin

Ta na fita Nesrine ta sauko da ga saman gadon ta ta nufi closet ta dauki hijabin ta ta saka sannan ta fito

Cen bakin dakin ta ta hango mama ta na zaune ta na jiran ta
Gaban mama ta karaso ta tsuguna ta na jiran mama ta bata kudin cepane

Nan ta mama ta ba ta dubi biyar ta fada mata duk wani abu da za ta bukata sannan ta mata gargadi a kan banda tsayawa ragaita

Dariya Nesrine ta yi ta na kokarin mikewa ta ce " ni fa mama ba Inaya ce ba , ita ce in ka aike ta sai ka manta da ita "

Ta na gama fadar hakan ta juya ta fice gidan
Da kallo mama ta rakata har sai da ta fita sannan ta mike ta shiga dakin ta

Nesrine kuma bayan ta fito gidan, ba ta tsaya wani bata lokaci ba kai tsaye ta nufi shagon da su ke yin cepane kullum

Bayan ta Kamala ta juyo ta kama hanyar gida , ta na tsaka da tafiyar ta kwatsam wata mota ta buge ta

Da sauri mutane su ke yi kan ta su na tambayar ta lafya
Da sauri shi ma matukin motar ya fito , ya na sanye da jeans baki da t-shirt blue, ya na sanye da face mask baki shi ma da wata cap baki ita ma , sam ba ka iya ganin face din shi da kyau

❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥

( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )

STORY & WRITTEN BY : ANISH

Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

PAGE 22 ❤🔥

Da sauri shi ma matukin motar ya yi kan ta ya na tambaya ba ta ji tsiwo ba

Girgiza mishi kai ta yi murya na kerma dan tsoron da ta ji ta ke fadin " ba ba komai ba...n ji tsiwo ba "

Da sauri matukin motar ya ce " yi hakuri yar uwa ban gan ki ba ne amma don Allah tashi mu tafi Hospital a duba ki kar a je kin ji rauni "

Da sauri ta yi kokarin tashi ta na dafa gaban motar shi ta ce " a'a na gode a na jira na a gida "

Cikin dabara ya sa kafar shi ya bike kafar ta har sai da ta saki kara ta fadi ta konta
Chapter 29 · 0% Book details