← Book details Exile Princess Love And Power Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 44

Sashe 22

Exile Princess Love And Power Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani dan karamin murmushi geffen fuska ya yi ba tare da ya dago kai ba ya ce " nassan abu mai wuya ne ki yarda da hakan amma bazan ga laifin ki ba , har yanzu ke yarinya ce , ko na fada miki wasu abubuwa baza ki fahimta ba , amma zan so ki sani , ni ba mayaudari ba ne banzo nan da niyar cutar wa ba , ban aure ki ba da niyar cuta , akasi ma ba a son raina ba a ka yi wannan auren kuma ban san manufar wannan auren ba , bazan iya sakinki ba , kuma bazan iya daukar ki a matsayin matata ba , kin yi min kannanta gaskia , amma zan rike ki a matsayin sister di ta , kema zan so ki dauke ni a matsayin brother din ki , duk wani abu da za ki bukata ki fada min , kar ki ji kunyar yi min wata magana , idan har kuma Allah ya saka miki soyayyar wani a cikin zuciyar ki zan so ki fada min da kai na zan aura miki shi a matsayi na na brother din ki "
Ya kai karshen ya na dago kai ya kale ta

Ita ma dago kai ta yi ta na murmushi ta kaleshi ta ce " shikenan yaya Zayd ni ma zan dauke ka a matsayin brother di na duk da dama a hakan na dauke ka "

Jinjina mata kai ya yi kafin ya ce " shikenan sister yanzu kin ga lokacin sallat ya yi sai ki tashi ki tafi ko , nan da next week ina son mu sauya gida dan ina ga fa wannan ya fara yi mana kananta "

Yar karamar dariya ta yi har sai da fararen hakoran ta su ka bayana sannan ta ce " shikenan yaya Zayd , kai ma ka tashi ku tafi massalaci idan kun dawo mu ci abinci a tare yau "

" okay ba matsala " ya fada mata a takaice

Murmushi ta yi kafin ta mike ta nufi corridor ta shiga bedroom din shi

Ta na shiga Moussa ya fito ya ce ma Zayd su tafi
Ba musu ya tashi ya bi bayan shi su ka tafi mosque

After one week

A takaice haka rayuwa ta ci gaba da tafiya a cikin wannan gidan , Tsakanin Inaya da Zayd shakuwa ta shiga tsakanin su sosai , idan ya na gida kullum su na a tare su na hira duk da yawwan ci ita ke yin ta , wani lokaci shi da kan shi ya ke rakata school , sannan in lokacin tashin su ya yi , kuma ya koma su dawo a tare , ya na kula da ita kamar kanwar shi ta gaskia , shi duk wannan abun da ya ga ta na yi mishi a zaton shi ta daina son shi , shi kuma bai san tarko su ka shirya mishi ita da Moussa ko wane tarko ne wannan oho ?
A cikin yan kwana kin Nesrine ta je ta bawa Zayd hakuri da mumunar kallon da ta ke yi mishi , ya nuna mata babu komai , da ga haka Inaya ta roke ta ta dinga zuwa ta na taya ta hira idan ba ta da aikin yi amma ta nuna baza ta iya ba dan ta na tsoron yin karo da idanun Zayd
A takaice dai su na rayuwar su cikin konciyar hankali duk sun manta da wata damuwar su

Inaya

Zaune ta ke cikin falon gidan ta na kallon shirin Akushi da Rufi na tashar Arewa 24 ,

Ta na zaune a haka Zayd da Moussa su ka shigo su na sallama kamar dai kullum ta Moussa a ka ji

Da murmushi a face din ta ta amsa musu sannan ta yi musu sannu da zuwa

Moussa ne ya amsa mata sannan ya wuce corridor ya shiga bedroom din shi
Shi kuma Zayd ya karaso ya zauna saman sofa da ya ke fuskantar ta ta

Ta na ganin ya zauna ta juya kai ta ci gaba da kallon Tv din ta , shi kuma ya kura mata ido a cikin bakin glass din shi

Sai da ya dauki lokaci ya na kallon ta kafin ya ce " Za muyi tafiya ni da Moussa , baza mu wuce one week ba , idan kin ga baza ki iya zama nan ke kadai ba za ki iya komawa wajen uncle duk lokacin da ki ka so , sannan ki kiyaye wajen zuwa college babu fashi , akwai kudi cikin bedside drawer ko da kin bukaci wani abu duk lokacin da ki ka yi niyar zuwa wajen uncle za ki iya tafiya "

Jinjina mishi kai ta yi ba tare da ta juyo ta kaleshi ba ta ce " yaushe za ku tafi yaya Zayd ? "

" yanzu " ya fada a takaice

Da sauri ta juyo ta kaleshi lokaci guda idanun ta su ka kawo ruwa
Ta na shirin magana ya riga ta cewa " no please kar ki yi kuka , just one week za mu yi , sannan akwai waya a cikin bedside drawer zan ringa kiran ki kullum dan na ji ko lafya , ki kontar da hankalin ki , baza mu dade ba "

Ya na gama fadar haka ya mike tsaye dai'dai lokacin da Moussa ya fito da ga cikin corridor janye da trolley din su

Hawayen da su ka tsaya mata a ido ne su ka fara zubowa a hankali ta na kallon Zayd da ke kallon ta shi ma

Dan lumshe idanun shi ya yi kafin ya bude su a hankali cikin zuciyar shi ya na jin ba dadi zai rabu da ita ba karya yan kwana kin nan da su ka yi ya saba sosai da ita dan ta na rage mishi kewar kanwar shi

A hankali ya bude hannayan shi ya yi mata allamun ta zo
Da gudu ta taso ta fada saman fafadar kirjin shi ta na sakin kuka

Shi kuma ya rufe hannayan shi ya rungume ta tsam kamar na ce zan kwace mishi ita

Tabe baki Moussa ya yi ya na kallon su cikin ranshi ya na kara godewa Allah da ya nuna mishi wannan ranar

Da sauri ya ciro wayar shi da ga cikin aljihun shi ya dauke su hoto har wajen biyar

Bayan ya meda wayar shi cikin aljihu ya yi musu gyara murya ya na fadin " Romeo saki Juliette don Allah mu tafi kar mu makara " ya kai karshen ya na gumshe dariya sannan ya fara takawa ya fice falon

A hankali Zayd ya zame hannayan shi da ga bayan ta ya raba jikin su sannan ya kai hannayan shi saman face din ta ya goge mata hawayen ta sannan ya ce " ki kula da kan ki zan kira ki idan mun isa "

Jinjina mishi kai kawai ta yi ta na sunkuyar da kai dan kar wasu hawayen su zubo mata idan ta kaleshi

Ya na fadar haka ya juya ya fara takawa zai bar falon

Har ya kai bakin kofar ya tsaya , sai da ya dauki wajen good one minute kafin ya juyo a hankali ya tako ya tsaya gaban ta

Babu shirin ta ji saukar wadanan lalawsan lips din shi saman forehead din ta
Dan zaro idanu ta yi kafin ta lumshe su à hankali ta na sauke a zuciya

Kafin ta bude idanun ta tuni ya fice falon
Kallon kofar ta yi kafin ta saki wani dan murmushi ta ce " Allah ya kiyaye hanya yaya Zayd, Allah ya medo ku lafya "

Ta na gama fadar haka ta koma zaune saman sofa ta buga uban tagumi

❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥

( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )

STORY & WRITTEN BY : ANISH

Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

PAGE 16 ❤🔥

Washe gari

Washe gari kamar dai kullum yau ma karfe 6 na safe ta farka da ga barcin ta , ta yi duk wasu ayika na cikin gidan sannan ta shirya breakfast din ta ta ci sannan ta shiga wanka

Misalin karfe 7 ta baro gidan ta na shirye cikin uniform din ta, ta na rike da school bag din ta, ta na tafiya cikin konciyar hankali

Dai'dai ta karaso kofar gidan su Nesrine ta fito tare da malam

Ta na ganin malam ta fada jikin shi da gudu ta na murmushi ta ce " ina kwana Abba "

Murmushi shi ma ya yi ya na kai hannu saman kanta ya shafa ya na fadin " lafya lau Auta , ya ki ke ? Ina mai gidan na ki ? "

Raba jikin ta da nashi ta yi kafin ta ce " sun yi tafiya shi da yaya Moussa "

" shikenan Allah ya medo su lafya, wuce ku tafi car ku yi late "

Da to su ka amsa mishi ita da Nesrine kafin su riko hannun junna su yi tafiyar su

Sai da malam ya jima ya na kallon yada su ke tafiya su na wassa sannan ya juya ya koma cikin gida

Su Inaya kuma sai da su kussa isowa college din su sannan Nesrine ta ce mata " yaya Zayd bai fada miki lokacin da zai dawo gida ba ? "

Ba tare da ta kaleta ba ta ce " one week ya ce min za su yi "

Jinjina kanta Nesrine ta yi su ka ci gaba da tafiyar ba wanda ya ce ma wani uppan har su ka karaso college din su, a nan ne kowace ta nufi class din ta

After some days
Chapter 22 · 0% Book details