← Book details Exile Princess Love And Power Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 44

Sashe 12

Exile Princess Love And Power Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hafiz dai babban d'a ne ga governor din Kano, Moctar na bi mishi sannan Ramatou sai autar su Nabila , a shekaru zai kai 25 , Moctar kuma 21 , Ramatou 19 years sai Nabila da baza ta wuce 15 years ba
Tun bayan mahaifin shi ya zama governor wata izza da jiji da kai su ka saukar mishi
Duk abun da ya gani ya ce ya na so to sai ya same shi ko da ta karfi ce
Ga shi ba ya da mutunci ko kadan mahaifin nashi ma in ya bata mishi rai sai ya bishi kaca'kaca dan ba raga mishi ya ke ba
Tun haifuwar Nabila mahaifiyar su ta rasu , mahaifin na su ya sake aure har wajen sau uku
Amma duk wadda ya auro ba ta one month ta ke barin gidan sakamakon Dukan tsiyar da Hafiz ke yi musu
Mahaifin shi na sane amma ya ki yi mishi magana dan ya san ba karamin aikin Hafiz ne ba shi ma ya rufe shi da duka
Shi ya sa ya ja bakin shi ya yi shirin ya zuba mishi ido dan ya fi karfin shi
Duk wata badakala sa ya ke yi mahaifin shi na sane , sannu sannu har ya fara janyo Moctar cikin badakalar ta shi
Kullum su ne tafiya nightclub, ga shan giya da kayan maye
À takaice ba abun da ba su sha, sai dai ba su taba kusantar mace ba da sunnan Zina
Karewar zancen Nesrine da Inaya su ne mata na farko da su ka gani su ka ji su na son ta
Yadda a ka yi Hafiz ya hadu da Nesrine
Wata rana ce driver din Ramatou bai zo daukar ta ba sai ta kira Moctar a kan ya zo ya dauke ta
A lokacin su na tare da Hafiz
Da su ka iso school din , su na tsaye bakin gate ita da Nesrine
Tun da Hafiz ya daura ido saman ta ya ji ya na son ta
Sai bayan sun koma gida ne ya ke tambayar RAMATOU wacece wanan yarinyar da su ke tare
Nan ta fada mishi wacece Nesrine sai dai ba ta fada mishi ba ta na da kanwa
Goben shi tun karfe 7 ya je bakin gate fin school din ya jiran ta
Amma wani ikon Allah ranar nan Nesrine ba ta zo school ba
Sai da ya gama tsayuwar shi ya gaji sannan ya koma gida ,
Goben shi ma haka ya dawo school din
Wannan karan ta zo amma ta na baya dan Inaya ta riga ta fitowa shi ya sa a bai gane Inaya kanwar ta ba ce
Babu ko sallama ya kira ta cike da girman kai
Kallo guda ta yi mishi ta gane yayan Ramatou ne dalilin da ya sa ta fara sakin mishi fuska
Sannu sannu ta fara ganin halayan shi na gaskiya
Kullum sai ya zo college din su dan ya gan ta
Wata rana har waya mai tsada ya kama ta amma ta ki karba
Haka kuma ba karamin bata mishi rai ya yi ba har ya tsinka mata mari cikin fushi sannan ya bata wayar da karfi ya ce zai kire ta
Inda ya ajiye wayar nan ta bar ta ta yi tafiyar ta ko wa ya dauke ta oho !
Washe gari bayan ta zo school ya isko ta ya ke tambayar ta ina wayar da ya bata
Nan ta mishi karyar wai Mamar ta ta gan ta kuma ta amshe ta
Bai yi mata magana ba kawai ya bar school din , sai da ya yi wajen sati bai zo ba
Nan Ramatou ta zo ta hura mata kunne a kan Hafiz tsakani da Allah ya ke son ta ta daure ta ringa kula shi ko ya ji dadi
Abotar da ke tsakanin su ya sa ta yarda da zancen ta, dan ko ba komi yayan ta ne bai kamata ta wulakan tashi haka ba
Sannu sannu ta fara kula shi har ta fada soyayyar shi
Amma shi kuma ya na nan kamar dai kullum, bai sauya ba sam dan wani lokaci in ta bata mishi har marin ta ya ke wai a haka wai ya na son ta ( ni dai na ce humm)
Babu irin gift din da bai kama ta ba amma ko wane lokaci sai dai ta yarda shi tsakar hanya ko kuma ta bar shi nan inda ya bata shi
Sannu har soyayyar da ke mishi har ta fita zuciyar ta dan a ganin ta, Hafiz ba al'heri ba ne a rayuwar ta shi ya sa yanzu ta daina kula shi, shi kuma hakan ba karamin zafi ya ke mishi ba

TO KUN DAI JI WANENE HAFIZ DA KUMA ABUN DA KE TSAKANIN SHI DA NESRINE ✌

❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥

( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )

STORY & WRITTEN BY : ANISH

Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

PAGE 8 ❤🔥

Zayd

Zaune ya ke cikin motar su wajen mai zaman banza ya na rike da wayar shi ya na latsa wa ya na sanye da tracksuit sky blue colour ya na sanye da wadanan bakin glglass din nashi na gado

Yayin sa Moussa shi kuma ke tukin, ya na sanye da Jeans baki da t-shirt Red colour

Su na a haka Moussa ya katse shirun na su da cewa " wai Amir ka fada ma babyn ka za ka yi tafiya ne ? " ya kai karshen ya na dan satar kallon shi

Shiru bai amsa mishi ba ko dago kai bai yi ba ya ci gaba da aikin shi

Dan murmushi geffen fuska Moussa ya yi sannan ya ce " Amir wai me ya sa ba ka kula yarinyar nan "

Ba tare da ya dago kai ba ya ce " meye ruwan ka a ciki ? "

" babu kawai gani na yi bai dace abun da ka ke mata ba, ka ga fa kallon makaho da kurma ta ke maka ba ta san kai ainahin wanene ba, ba ta san kowa na ka ba, ko cikeken sunnan ka ba ta sani amma a haka ta ke son ka "

A dubu dari Zayd ya dago kai ya kali Moussa ya ce " me ka ke son cewa ? "

Yar karamar dariya Moussa ya yi kafin ya ce " lalle ma ka cika dan rainin sens, yanzu ka na son ka ce min duk soyayyar da ta ke maka ba ka ganin komai, lalle ma yau ka cika babban makaho " ya kai karshen ya na sake bushewa da dariya

" wait ! Maganar me ka ke yi haka, wannan baby har ya san minene soyayya ? na ga ai gaban ka ta ce dakwai wanda ta ke so " ya kai karshen ya na medo da kallon shi kan wayar hannun shi ya ci gaba da aikin shi

" humm wai kenan ba ka gane ba da sunnan ka ne ta so fada ba, dan ka na wajen ne ya sa ta yi shiru , kai a ganin ka duk abun nan da ta ke ma da sunnan makobtaka ne kawai, no Amir ! Wlh pure love ne ta ke yi maka, kallo guda za ka yi mata ka gane soyayyar ka a idanun ta, nassan wadanan bakin glass din ya hana ka gani, Amir kai ka ce min ka na son ka manta rayuwar ka ta baya , to wannan damar ka ce , ka karbi matar ka , and found your family "

Shiru Zayd ya yi bai ce da shi komai ba amma cikin ranshi ya na tunanin kalmomin Zayd tabass wanda ke maka kallon makaho da kurma , kuma a hakan mutumin ya so ka ya tabbata soyayyar gaskia ya ke maka

" no ! Gaskia she is to small for me , wannan ko dauko ta ba na tunanin za ta iya bare har a yi tunanin wata familyn, gaskia ban yarda da abun da Diya ke fada ba " ya fada cikin zuciyar shi

Cen kuma wata zuciyar ta ce mishi " in ta tabbata yanzu kai ma ka na son ta ? "

Da sauri ya girgiza kan shi ya ce " no ! Impossible i can't do that "

Kallon shi Moussa ya yi kafin ya ce " what you can not do ? "

Dago kai ya yi ya kali Moussa sannan ya ce " nothing ! " sannan ya meda bayan ya jingina a bayan kujerar shi ya lumshe idanun shi

Daga kafadun shi Moussa ya yi irin ban damu ba cikin ranshi ya ce " in ta yi tsami ma ji "

Haka su ka ci gaba da tafiyar su ba wanda ya ce ma wani ufan har su ka isa inda za su je

Inaya

Konce ta ke saman bed din su ta na kallon ceiling ta daura hannu daya saman ciki dayan kuma saman gashin ta, ko tunanin mi ta ke oho !

Ta na a haka malam ya shigo dakin ya na sallama

Ba tare da ta motsa ba ta amsa mishi sallamar mishi

Bakin ya karaso ya zauna sannan ya kai shi ya daura saman nata ke saman cikin ta ya ce " auta, wai me ya ke damun ki ne tun shekaran jiya na lura yanayin duk ya sauya ko waje na da ki ke zuwa kin daina ko laifi na yi miki ? "

A hankali ta janye hannun ta , sannan ta juya ta bashi baya sai ta ce " Abba me ya za ku min aure ba tare da na sani ba, nassan ku na ikon yin hakan amma Abba ni ba ni son wanda a ka aura min , gaskia Abba a raba auren nan "

" dalilin da ya sa wacen ranar na tambaye ki in kina son shi , amma ba ki ba ni amsa ba ki ka tashi ki ka tafiyar ki "

" ni Abba ba ku tambaye ni in ina son shi ba , "

" to shikenan yanzu bara na sake tambayar ki , ki na son Zayd ? "
Chapter 12 · 0% Book details