← Book details Exile Princess Love And Power Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 44

Sashe 34

Exile Princess Love And Power Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya na konce a hakan ya ji a na takowa stair a hankali
Slowly ya ware idanun shi ya na kallon ceiling amma bai motsa ba

Ko bai duba ba ya San ko wanene , dan ya san bayan ita ba wanda ke saukowa a irin wannan lokacin

A hankali ya sauko da kafafun shi ya mike tsaye , sannan ya nufi hanyar dining table ya na taku a hankali cikin ranshi ya na fadin yau sai ya ga wainar da ta ke toyawa cikin daren nan

Cen kassan makoshi ya yi sallamar shi , sannan ya tsaya bakin kofar kitchen ya zuba mata idanu , ya nade hanayan shi a kirji

Sanye ta ke cikin kayan barci kanana pink colour , ta na tsaye gaban counter ta na yankar fruits

Slowly ya fara takowa inda ta ke ya na yi mata gyaren murya

Da sauri ta juyo ta ga ko wanene dan ita ba ta ji shigowar mutun cikin kitchen din ba

Ta na ganin shi ta saki murmushi ta ce " yaya Zayd har ka bani tsoro " ta kai karshen ta na juyawa ta ci gaba da yankar fruits din ta

Takowa ya ci gaba da yi har ya karaso geffen ta ya tsaya ya na kallon kananan hanayan ta , ta na yankar fruits cikin konciyar hankali

A hankali ya kai hannun shi ya riko nata da sauri ta dago kai ta kali face din shi , yayin da shi kuma hannayan ta ya ke kallo

Cikin sanyi murya ta ce " yaya Zayd me ya faru ? "

Sai da ya dauki lokaci kafin ya ce " ba ki jin tsoron ki ji tsiwo da wadanan kananan hannayan na ki ? "

Dan murmushi mai sauti ta yi kafin ta janye hannayan ta da ga cikin nashi slowly ta ci gaba da yankar fruits din ta

Sai da ta Kamala sannan ta dauki tray din ta juya ta bar kitchen din ta bar shi nan tsaye

Sai da ta fita sannan shi ma ya fara takawa ya fice falon
Nan ya hango ta zaune saman sofa ga table gaban ta , ta daura tray din fruits a sama sai ci ta ke a hankali

Geffen ta ya karaso ya zauna , a hankali ya kai hannu saman tray din ya dauki barin Apple guda ya kai baki

Ba tare da ta kaleshi ba ta ce " yaya Zayd , don Allah ka fada min abun da ke damun ka "

Shiru ya yi bai amsa mata ba, sai ma konta wa da ya yi a jikin sofar ya daga kai sama ya lumshe idanun shi

Dago kai ta yi ta kaleshi, duk sai ta ji zuciyar ta ba dadi

Nan take idanun ta su ka kawo ruwa , ba ta san lokacin da kuka ya kubce mata ba

Da sauri ya bude idanun shi ya dago ya na kallon ta
Cike da rudu ya ce " me ya faru ki ke kuka ? "

Ko kallon shi ba ta yi ba ta ci gaba da kukan ta , hawaye wasu na bin wani

Duk ya bi ya rude sai tambayar ta ya ke me ya faru amma ina ko kallon shi ba ta yi

Da ya ga abun na ta ba mai karewa ba ne sai ya kai hannu ya rungumo ta a jikin shi ya na dan bubuga bayan ta ya ce " stop crying please , me ya faru ki ke wannan kuka haka ? "

Cikin disashashiyar murya ta ce " ba kai ne ba yaya Zayd , kullum sai na tambaye ka abun da ke damun ka amma kullum sai ka ce ba komai "

Da sauri ya katse ta da cewa " i'm sorry, yi hakuri ki daina kukan nan wlh ba na so "

Dagowa ta yi daga jikin shi ta na goge hawayen ta, ta ce " shikenan yaya Zayd na bar kukan amma don Allah ka fada min abun da ke damun ka ! "

Mikewa tsaye ya yi sannan ya mika mata hannu a kan ta tasso
Ba musu ta daura hannun ta saman nashi sannan ta mike tsaye ta na kallon shi cikin ido

Ta na mikewa tsaye ya fara takawa ya yi gaba ita kuma ta bi bayan shi

A haka su ka Haye stair a tare ya na rike da hannun ta
A tunanin ta bedroom din da ta ke barci nan za su koma sai ta ga ya wuce ta

A haka har su ka wuce duk bedroom din da ke sama , su ka nufi bedroom na karshe
Tun da ta shigo gidan ba ta taba shigo shi , kuma ba ta taba ganin wani ya bude shi ba ya shiga

A hankali ya kai hannu ya murda handle din kofar ya tura ta ya shiga

Nan ta ga wani falon daban , dauke da wasu sofas biyu white colour guda three seaters dayar one seater sai wasu biyu two seaters sky blue , da ga tsakiyar su kuma wata table ce ta glass saman wani carpet fari mai ratsin blue , geffen doguwar sofa akwai wasu kananan tables na glass , sannan ta na fuskantar wata makekiyar Tv plasma makale a bango

Ba ta ida shan mamaki ba, sai da su ka shiga bedroom din
Kyawon bedroom din wannan book din ya yi kadan ya fade shi , girman shi ya fi falon part din , komai na cikin dakin white colour ne ,

Da ga shigo dakin sai saman wani makeken royal bed fari kal shinfida da bedsheet fara , ya na fuskantar wata makekiyar Tv plasma girman ta daya da ta falon da su ka baro
A geffen gadon kuma na hagu wani dressing mirror ne dauke da perfume da lotion kala kala
Dressing mirror din na tsakiyar wasu door , guda toilet guda dressing room
( a nawa tunanin 🤷‍♀️ )
A geffen dama na Tv din wata door ce ta glass wadda za ta sada ka da balcony din dakin

❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥

( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )

STORY & WRITTEN BY : ANISH

Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

PAGE 23 ❤🔥

Da kallo ta ke bin shi cikin zuciyar ta ta na tambayar kan ta wanene Zayd

Ta yi nisa cikin tunanin ta ta cintsi murya shi ya na fadin " konta ki yi barci ina zuwa "

Da to ta amsa mishi sannan ta saki hannun shi ta zauna bakin gadon

Shi kuma ya ci gaba da takawa ya nufi daya daga cikin kofofin geffen dressing mirror

Ya na shiga ta ida Hayewa gadon ta konta

Bayan wasu mintina ya fito daga toilet sanye da bathrobe , bai tsaya shafa lotion ba ya wuce dayan door ya shiga dressing room
Jim kadan ya fito sanye da kayan barcin shi ash colour ma su kyau

Gadon ya nufa ya Haye geffen guda ya konta ya na fuskantar ceiling

Cen ya juyo da kan shi ya na kallon ta , ta juya mishi baya har ta yi barci

Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya lumshe idanun shi ya sake bude su slowly a kan ta

Cikin sanyin murya ya ce " ko na fada miki ba za ki gane ba , akasi ma ni da kai na ban san abun da ke damu na ba , amma na san duk lokacin da na ke tare da ke ina jin sauki a cikin zuciya ta , ina ji a jiki wani mumunar abu na shirin faruwa da ni kamar zan rasa wani abu mai mahimanci a rayuwa ta , duk da san ba tabas abun da na ke ji ya faru ba , amma ba ni fatan na rasa ki cikin rayuwa ta , dan a yanzu ke kadai ce family na , na so na yi miki irin son da ki ke yi min amma zuciya ta ta kassa ban san dalili ba "

Ya kai karshen ya na juyo da kan shi ya fuskanci ceiling ya lumshe idanun shi

Kamar da ga sama ya tsinci wannan zazzakar Muryar ta ta, ta na fadin " na sani yaya Zayd ba laifin ka ba ne dan ba ka so na , laifi na ne da na fada soyayyar ka da karancin shekaru na , na yi maka alkawari zan yi kokarin na cire shi da ga cikin zuciya ta "

Cikin nitsuwa ya katse ta da cewa " ni ban ce ki cire shi da ga cikin zuciyar ki ba "

Slowly ta juyo ta kaleshi, sannan ta ce " me ya sa to baza ka iya so na ba , ba ni da kyau ne ? "

" pleaseeee ni ba wannan ba , kin fi kowa sanin ki na da kyau Masha Allah "

" to minene matsalar yaya Zayd ? " ta fada kamar za ta yi kuka

Juyo da kan shi ya yi ya kale ta cikin idanun ta da su ka kawo ruwa ya ce " i have never been in love , na hadu da mata dayawa a duniya , masu kyau , masu dukiya da mulki amma ko kallon kirki ban taba yi musu ba , ni a tsarin rayuwa ta ban shirya zama da mace ba , amma ke kin shigo lokaci guda kuma har ga Allah ba ni fatan ni fita da ga cikin rayuwa ta "
Ya kai karshen ya na mika matta hannu a kan ta zo

Ba musu ta karaso ta fada jikin ta boye fuskar ta a kirjin shi
Rungume ta ya yi a jikin shi , ya lumshe idanun shi a haka har barcin da ya jima bai yi ba ya dauke shi

Washe gari

Misalin karfe 10 na safe

Duk mutanan gidan su na a zaune a falo na kassa Banda Nesrine da ke cen konce a word room

Sai hirar su su ke cikin konciyar hankali banda Zayd da ya kurawa Inaya ido cikin bakin glass din shi , ita kuma ta kurawa TV ido kamar ita ta ke kallo

Su na tsaka da hirar su su ka ga an turo kofar shigowa falon
Chapter 34 · 0% Book details