Sashe 9
Dahuwar Kaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Kun ji me nace ko? Kuma idan kuka yi sallama sai kun ji an amsa an ce ku shigo, idan ba haka ba wallahi dukan da zan yi wa mutum sai ya fi wannan." Baki yana rawa yaran suka amsa, ya ɗauko alawa ya damƙa wa kowa a hannu sannan ya lallashe su cikin nasiha ya tashi ya fita.
ÆŠakin Bilkisu ya shiga, saboda tun da ya yi mata magana ta yi zuciya ta fice ta tafi É—aki. A zaune ya same ta ta haÉ—e fuska, shi ma fuskar ya sake haÉ—ewa ya ce.
"Bilikisu!"
Shiru ta yi masa ba ta amsa ba, ya dube ta ya cigaba da cewa.
"Ba zan zura ido ki lalata mini tarbiyyar yara ba, saboda kishin rashin hankalin da kike yi, daga yau sai yau idan kika kuma tura mini yara ina ɗakin Amina ba tare da ƙwaƙƙwaran dalili ba sai ranki ya ɓaci. Ni ba hana su shiga ɗakinta zan yi ba, amma ke ma ki san lokacin da za ki dinga tura su. Wai duk wannan abin da kike yi na mene ne? Ba dai don kana da na yi mu'amala da ita ba ne? To me ya yi saura yanzu? Na fahimci duk karar da nake yi miki da mutumtawar da nake yi miki ba kya gani. Bari ki ji, yadda kike matata haka Amina take a wurina duk matsayinku ɗaya, yadda kika san ni a matsayina na mijinki haka ita ma ta san ni. An faɗa miki kishi hauka ne? Ke wanne irin abu ne ba ki yi ba a lokacin da yayanki zai ƙara aure, ba ke ce amara ba har da ɗauko auko? Amma a kaf dangina wa ya taɓa zuwa gidan nan ya nuna miki yana farinciki da auren da zan yi, duk suna yi ne don su yi miki kara ba wai don ba sa so ba ne.
Wallahi tun wuri ki dawo hayyacinki, ina faɗa miki haka ne tun ba ki ƙure yarinyar nan ba. Idan kika buɗe mata ido nan gaba ba za ki ji daɗin zama da ita ba."Hafiz yana gama magana ya fice daga ɗakin rai a ɓace.
Wannan faɗan da Hafiz ya yi wa Bilkisu da yaransa su Sayyada, shi ya sa Amina ta samu 'yanci sakata ta wala a ɗakinta. Don idan Hafiz yana nan, tana samun damar saka ƙananan kayanta masu jan hankali da rigunan bacci. Saɓanin a baya da take saka manyan kaya, gudun kada yaran su shiga su ga shigar da ba ta dace a jikinta ba.
A ranar da Hafiz zai koma ɗakin Bilkisu tun safe take cikin annshuwa tana walwala. Hatta Amina da ba wata hirar suke yi ba, ta fahimci walwlarta. Tana zaune bayan la'asar ta ji sallamar Aunty Murja da Na'ima, duk da Amina ba ta sansu ba amma fuska a sake ta amsa sallamarsu tana yi musu sannu da zuwa. Fuska a sake su Aunty Murja suka amsa mata, suna cikin gaisawa Bilkisu ta leƙo a fusace ta ce.
"To tsaiwar me kuke yi Aunty Murja ku shigo mana." Ƙarasawa suka yi ɗakinta, sai da suka gaisa Aunty Murja ta ce.
"Oh ashe kuma haka abu ya faru Bilkisu, ni ai ina zaune rannan katsam Abban Sajida yake faɗa mini wai Hafiz zai yi aure. To daga baya kuma na ji an ce ba za ki yi wuni ba, don dama cewa na yi zan zo ƙafa da ƙafa. Da muka ji ba wuni sai kawai na cewa Auntyn yara ta bari ma zo daga baya." Taɓe baki Bilkisu ta yi ta ce.
"Tsinanniya gata can ai, an kawo ta baƙar daga. Sai ta zo ta ci uwar da nake ci." Aunty Murja murmushi ta yi, ta tuna irin habaici da cin kashin da suka dinga yi mata. Sai kawai ta ce.
"Allah Ya haÉ—a kanku, ya sa zuwanta alheri ne."
"Haba Aunty Murja, kin taɓa ganin zuwan kishiya ya zama alheri?" Bilkisu ta faɗa cikin sauri, sunkuyar da kai Na'ima ta yi. Aunty Murja ko kaɗan ba ta ji daɗi ba saboda Na'ima tana wurin, don haka ta miƙe ta ce.
"Mu bari mu wuce yawon namu da yawa, za mu leƙa barka matar yayan Auntyn yara ce ta haihu."
Mamaki ne ya kama Bilkisu ganin yadda Aunty Murja ta ɗauki kishiya kamar wata ƙanwarta. Har soro ta raka su, Na'ima ce ta fara fita. Cikin sauri Bilkisu ta kamo hannun Aunty Murja ta ce.
"Aunty Murja wai kishiya kike yi wa wannan haba-habar? Salon kina zaune ta zo ta raba ki da mijin? Ai wallahi ni da kishiya sai dai kallon banza." Murmushi Aunty Murja ta yi ta ce.
"Ya danganta da irin kishiyar da kike da ita Bilkisu, ita kishiya kana karantar yanayin yadda ta zo ne. Idan ta zo da arziki ku yi shi, idan kuma da tsiya ne sai ki kama kanki. Ni ba abin da zan cewa Na'ima, saboda zuciya É—aya take tare da ni da yarana. Yanzu haka zancan da nake yi miki Nimrah ta koma hannunta, kema ki karanci taki kada ki cuce ta. Ki zauna ke da ita zuciya É—aya, sai ki ga zamanku ya yi daÉ—i."
Ajiyar zuciya Bilkisu ta sauke, tana jin magnar Aunty Murja kamar busar sarewa. Daga ɗan waje Na'ima ce ta leƙo ta ce.
"Aunty kin san dai halin Abban Sajida, wallahi idan muka yi dare ke zan É—orawa laifi. Ko kuma na kama hanya na yi gaba sai kin taho." A gaggauce Aunty Murja ta yi wa Bilkisu sallama tana dariya ta ce, "Wallahi ki É—ora mini laifi, ni ma sai na faÉ—a masa laifin jiya da na rufa miki asiri." Na'ima ta yi dariya suka tafi.
Kwana biyu gidan Hafiz lafiya ƙalau ake zaune, saboda a ɗakin Bilkisu yake. Koda Hafiz ya koma ɗakinta, babu wani canji da ya nuna mata. Hasali ma duk don ya faranta mata, haka ya dinga santin girkinta da duk wani abu da ta yi masa. Shi kansa ya ji daɗi sosai ganin yadda ta watsar da komai, duk da ba wata doguwar mu'amala suke yi da Amina ba. Amma babu wani abin faɗa ko baƙar maganar da take haɗa su, haka daga ɓangaren Amina ta ji kewar Hafiz da zai bar ɗakinta. Amma hakan bai sa ta yi wata muguwar kissa ko ɓacin rai ba, hasali ma ta rungumi su Sayyada hannu bibbiyu. Don haka take jan su ɗaki su yi ta wasansu a cen.
Tun a safiyar ranar da Hafiz zai koma ɗakin Amina Bilkisu take haɗe rai, da Magariba ta yi Amina tana gama girki bayan ta shiga wanka Bilkisu ta saci jiki ta shiga ɗakin Amina. Cikin sauri ta buɗe galan ɗin fetir ɗin da Hafiz yake sayan mai da shi, ta ɗebi kaɗan ta yaryaɗa a cikin kular abincin. Da sauri ta fito ta koma ɗaki zuciyarta fes, bayan wani lokaci ta ji ƙarar mashin ɗin Hafiz ya shigo cikin gidan. Dariya ta fara ƙyaƙyatawa har riƙe ciki, ta jikin labule ta hango Amina ta fito cikin tsaleliyar atamfa. Ta ƙafa ɗaurin ɗankwali ba ƙaramin kyau ya yi mata ba. Yana saukowa daga kan mashin Amina ta rungume shi, fake ta sakarwa kumtunsa. Ya saka hannu ya riƙo ƙungunta ya ce.
"Wannan wankan zai sumar da ni."
Murmushi ta yi tana fari da ido ta ce, "To ni kuma na yi yaya kenan?"
"Sai ki farfaɗo da ni." Ya faɗa yana murmushi, ledar hannunsa ta riƙe suka shiga ɗaki. Yana shiga ɗakin, ya cire hula ya ajiye sannan ya fito ya shiga ɗakin Bilkisu.
Gaisawa suka yi ya tambayi yaran, babu yabo babi fallasa ta ba shi amsa sannan ya fita. Yana fita ta sake sakin dariyar ƙeta, tana jiran sakamakon abin da ta aikata.
GIDAN ALHAJI UMAR
Jin abin da Ahaji ya faɗa ya sa Shukura ta sake kwaɓe baki ta ce.
"Gaskiya ni dai tsoro nake ji baby, wallahi ba zan iya kwana a É—akin nan ba kada a sake shigowa."
Shiru Daddy ya yi, sai ya nufi É—akin su Haidar ya ce.
"Kai Haidar a cikinku akwai wanda ya fito waje ne?" Sun fahimci sarai inda maganarsa ta dosa, amma gudun ɓacin ransa ya sa suka ce masa a'a. Komawa ya yi wurin da ya bar su Shukura, ya dubi Hajiya Karima ya ce.
"Ke ki je ɗaki Hajiya, zan zauna da ita zuwa nan da sallar asuba." Da ido Hajiya Karima ta bi shi, saboda ɓacin rai ko tanka masa ba ta yi ba ta nufi ɗaki zuciyarta tana suya. Cikin ɗaki Shukura ta shiga, Daddy ya rufe mata baya. Suna shiga ta shige jikinsa, tana runtse ido alamun tsoro take ji. Sannu a hankali yanayin salon zaman da suke yi ya sauya. Shukura ta shiga aika masa da saƙonni masu birkitarwa, ko kaɗan Daddy bai yi niyyar biye mata ba. Amma yanayin saƙon da take aika masa ya sa shi yi wa zuciyarsa biyayya, ya shiga mayar mata da martani. Jin Shukura tana ƙoƙarin kai shi matsayar da bai yi niyya ba, ya sa shi ɗagowa cikin wani irin yanayi ya ce.
"Baby mu bari sai na dawo nan ko?" Cikin kissa Shukura ta fashe masa da kuka tana narkewa a jikinsa ta ce.
"Amma ai ni ba haramun ba ce a wurinka, wai dama haka za ka dinga wulaƙanta ni ban sani ba." Yadda ta ƙarasa maganar tana haɗe jikinsa da nata ya sa jin wani abu yana fisgarsa a kanta, ya sunkuya ya laso hawayenta cike da so ya ce.
"Ba na son kukanki baby."
"To ni idan ba ka so ka daina hana ni." Ta furta tana sake aika hannunta cikin jikinsa. Cikin kissa da kisisina Shukura ta cigaba da sarrafa Alhaji har sai da suka biyawa juna buƙata, sai daga baya duk ya ji bai ji daɗi ba. Ko babu komai ya san wannan lokacin na Mommyn Mami ne. Shukura da gayya ta fita ta ɗora ruwa a tukunya, tamkar rana haka ta dinga buga tukunyar lokacin da za ta ɗebi ruwa. Sai da ta ɗora musu sannan ta koma ɗaki ta narke a jikin Daddy.