Sashe 31
Dahuwar Kaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Baiwar Allah wannan yarinyar da take kuka daga ina?"
Mai É—an sahun ya tirke ta da tambaya, yana wurga mata kallon tuhuma.
"Yata ce, shagon Babanta zan je kunama ce ta harbe ta zan kai ta kemis."
Fauziya ta furta a gajiya, kallon da yake yi mata na rashin yarda ya sa ta É—an waiga ta ce.
"Fatima ki faɗa masa me ya samu ƙafarki."
Fatima ta sake sakin ihu cikin kuka ta ce, "Cinnaka mai allura ne ya harbe ni, wayyo Mami ƙafata. Don Allah ki cire mini allurar cinnaka."
Sai da mutumin ya haska Fatima, sannan ya ga zallar kamar da suke yi da mahaifiyarta. Ya ce Fauziya ta shiga, bayan ta zauna ya wuce da su.
Ba su yi wata tafiya mai mugun nisa ba suka ƙarasa, ta miƙa wa mai adaidaita sahu ɗari biyun don ya ɗauki kuɗinsa. Ya ce mata ta je kawai, bayan ta yi masa godiya ta nufi layin da shagon ɗinkin su Kabir yake. Tana gab da ƙarasawa shagon, ta ga wani ya fito daga ciki da mukulli yana shirin rifewa.
"Assalamu alaikum."
Fauziya ta yi masa sallama, mutumin ya amsa mata yana saka mukullin ƙofar.
"Don Allah Kabir fa?"
Kallon tsaf ya yi mata, yanayinta ya ga ba ta yi kama da masu karɓar ɗinki ba. Kuma koda ɗinkin za ta karɓa, tana mace har sha biyu saura yana ganin dare ya yi.
"Hajiya lafiya?"
Fauziya ta dafa bango a gajiye ta ce, "Matarsa ce."
Sai a lokacin mutumin ya É—an faÉ—aÉ—a fara'arsa.
"Ah Allah sarki, ai ban gane ki ba. Wallahi Kabir ya fita tun bayan sallar isha'i, ni kaÉ—ai na rage a shagon ni ma yanzu zan tashi."
Wani abu ya tsaya a zuciyar Fauziya, amma don kar ya fahimci wani abu sai ta saki fuska ta ce, "To shi kenan na gode."
Kamar ta karɓi aron kuɗi a wurin mutumin, sai kuma ta haƙura. Don ba ta san duk wani abu da zai taɓa mutumci, da martabar Kabir. Kemis ɗin da ta hango a farkon shigowarta layin ta nufa, ta sake zaro ƙaramar wayarta ta latsa lambar Kabir ko Allah zai sa ta shiga.
Bugun farko ta ji an É—auka, don haka ta yi saurin faÉ—in. "Hello."
Ita ma sai ta ji an ce hello da muryar mace, amma sai ta yi tunanin ko network ne ya maimaita abin da ta faÉ—a.
"Abban Na'ima kana jina?"
Daga can ɓangaren ta ji an ja dogon tsaki an kashe. Dam! Gabanta ya yi wani mummunan bugawa, wanda ya sa juya ta fara zabarin ƙafafuwanta har take yunƙurin wurgar da ita.
Da sauri ta sake latsa lambar amma sai ta ji ta a kashe, haka kawai ta ji zuciyarta tana yi mata wasu-wasin ko kuskuren lamba ta kira. Kamar wacce take bitar hadda, haka ta fara karanta lambar Kabir a fili tana saka wa a cikin wayarta. Ta sake latsa lambar ta kira saboda ta fita daga kokonton da take yi, amma sai ta ga duk lamba É—aya ce da wacce ta kira da farko.
Wani irin abu ta ji ya tokare mata maƙoshi da ƙirji, ta haɗiyi yawu mai ɗaci har ta ƙarasa shagon mai Kemis ɗin da yake ƙoƙarin rufewa. Da sauri ta ƙarasa ƙofar shagon tana faɗin.
"Don Allah ka taimaka ka duba yarinyata kafin ka rufe, wallahi kunama ce ta harbe ta."
Tausayinta ne ya kama shi, ya zare kwaɗon ƙofar ya koma ciki. Saboda tsabar gajiya, da ƙyar ta iya sauko Fatima ta miƙa masa. Bayanin abin da ya faru ta yi masa, sannan ya yi wa Fatima allurai. Ya ɗebo magunguna ya yi mata bayanin yadda za a ta dinga ba ta, jiki a sanyaye Fauziya ta ce.
"To nawa ne kuÉ—in?"
Sai da ya sake duba magungunan ya ce, "Hajiya gabaÉ—aya kuÉ—inki dubu huÉ—u da É—ari biyar." Kirjin Fauziya ya buga, ta dubi wayarta da ko dubu huÉ—u ba za a saye ta ba ta ce.
"Don girman Allah ka yi mini wata alfarma, don Allah ka yi mini haƙuri zuwa gobe da safe. Yanzu haka shagon mahaifinta na zo ba ya nan, wallahi ɗari biyu ce kawai a hannuna."
Cike da takaici yake wurga mata wani kallo, ya furta.
"Haba Hajiya, yanzu ni kin yi mini adalci kenan? Tun farko ai da sai ki ce mini ba ki da kuÉ—i, ni ma fa ba shagona ba ne. Yanzu idan Oga ya zo me zan ce masa? Kin san dai gari ba gaskiya, magana ta Allah ba zan iya ba ki kayan dubu huÉ—u da wani abu ki tafi da su ba."
Wayar hannunta ta miƙa masa ta ce, "Na san ban kyauta ba, amma don Allah ka yi haƙuri. Ga wayata ka riƙe, zuwa gobe In Shaa Allahu zan kawo maka cikon kuɗin..."
"A'a gaskiya, ba zan karɓi wayarki ba. Zan dai karɓi magungunan, ki je gobe da safen sai ki kawo kuɗin. Idan ma ba ki dawo ba, ni a aljihuna na biya kuɗin allurar da na yi mata."
Mai kemis ɗin ya katse ta yana kwashe magungunansa, sannan ya miƙe mata wayarta ya ƙoƙarin fitowa daga ciki. Duk yadda Fauziya ta kai ga roƙonsa fir ya ƙi amincewa, saboda ya jaddada mata shi ma ba shagonsa ba ne. Idan aka samu matsala a aljihunsa yake ciko.
A wannan karon ma haka ta dinga tafiya a ƙafa, sai dai wannan lokacin har ta ƙarasa gida ba ta samu adaidaita sahu ba. Sai tsirarun motocin gida da suke kai kawo a titi. Ta ci sa'a kamar yadda ta janyo ƙofar haka ta same ta, ta yi mamaki sosai da har sha biyu da kusan rabi amma Kabir bai dawo ba. Ba yau Kabir ya saba kai dare da sunan yana shago ba, amma bai taɓa haure sha biyun da rabi na dare a waje ba. Wannan ne ya sake tabbatar mata da zarginta.
"An ya Kabir É—ina zai iya zuwa wurin wata mace a tsohon daren nan?" Ta furta tana sake tuna muryar wacce ta É—auki wayar.
"Kabir É—ina babu macen da take gabansa."
Fauziya ta faɗa tana girgiza kanta. Da haka ta miƙe ta sake yi wa su Na'ima shimfiɗa a tsakar ɗaki, ta kwantar da su don ta samu Fatima ta tsagaita da kukan.
Bugun ƙofarsa ta ji, ta ji wani ɓacin rai ya lulluɓe ta. Kamar ba za ta tashi ba, tuna gidan ba su kaɗai ba ne ya sa ta yunƙura ta fita ta buɗe masa. Saboda haushinsa da take ji, ko kallonsa ba ta yi ba ta wuce ciki.
Suna shiga É—aki ta É—ebo kayan abincinsa ta ajiye ba tare da ta tanka masa ba.
"Ummu banat lafiya kuwa? Na ga kamar ba yadda na saba ganinki ba."
Kamar tana jira a ƙule ta ce, "Ta ya za ga gan ni dama? Bayan kana can wurin 'yanmatanka, yanzu Abban Na'ima cin mutumcin da wulaƙancin har ya kai ka tafi wurin wata har na kira ka ba ta waya." Idanunta suka ciko da hawaye tana jin wani maƙaƙi a cikin zuciyarta.
"Ai duk wulaƙancin da za ka yi mini ban cancanci haka daga gare ka ba, amma babu komai akwai Allah." Ta ƙarasa maganar cikin shasshekar kuka.
"Innalillah wa inna'ilaihir raji'un! Yanzu ni kike zargi Fauziya? Ni Kabir É—inki kike zargi da yawon gidan 'yanmata? Yanzu ko wani ne ya jefe ni da waÉ—annan kalaman, ashe ba za ki iya wanke ni ta hanyar shaidata ba?"
Shiru Fauziya ta yi tana mamakin kalamansa, tana kallon rainin hankalin da yake shirin yi mata. Ita kanta da wani ne ya sanar da ita abin da ta ji a lokacin, ba za ta taɓa yarda ba.
"Kana nufin wacce ta yi mini tsaki É—azu ba ka santa ba? Ko kana nufin ba wayarka ba ce? Don Allah Abban Na'ima kada ka mayar da ni wacce ba ta san me take yi ba."
Kabir ya sake marairaice murya ya ce, "Haba Fauziya, mene ne nawa ba ki sani ba? Kina tsammanin akwai wata mace da zan ɓata lokacina a kanta? Wallahi abin da kike faɗa ban san shi ba. Haba Fauzeena, yau fa da farinciki na ƙaraso gida saboda 'yan canjin da na samo."
Ya yi maganar yana sakin murmushi ya cigaba da cewa.
"Wallahi yau aiki ne ya sha mini kai, mun jima ba mu yi É—inki irin na yau ba."
Girgiza kai Fauziya ta yi tana jin ɗaci a ranta, a ɓangare ɗaya tsoron Kabir ya fara kama ta saboda ita da Kabir ba sa ɓoyewa junansu komai.
"Abban Na'ima yaushe ka fara ɓoye mini halin da kake ciki? Yaushe ka fara yi mini ƙarya?"
Ƙirjin Kabir ya buga da ƙarfi yana shirin yin magana ta katse shi.
"Ko minti talatin ban yi da baro shagonku ba, kuma an tabbatar mini da tun bayan sallar Isha'i ka bar shagon. Ashe kullum ninke ni kake yi? Ina nan yashe da baki ban sani ba."
"To ai fitar da na yi daga shagon gidan Alhaji Musa na je, kaya na kai wa iyalinsa kin san duk cikin shagonmu ya fi yarda da ƙwarewa ta. To lokacin da na je ƙofar gidan na kira wayarsa a kashe. Da na ce a yi mini sallama da shi, sai yaran gidan suka ce yana ganawa da wasu abokan kasuwancinsa, sai dai da na jira su kammala. Ganin zaman ya yi yawa ya sa na bayar da wayata aka jona mini caji a gidan, lokacin da Alhaji ya sallame ni har na kusa zuwa gida, na tuna na bar wayata a gidan shi ya sa na koma na karɓo." Kabir ya janyo ledojin da ya shiga da su ya ce.
"Ki dubi wannan sayayyar da na yi, duk da kuɗin da Alhaji ya biya ni ne. Wannan shinkafar kwano ɗaya ce, ga taliya da makaroni guda bibbiyu sai wake kwata da na ƙaro mana." Ya sake buɗe ɗayar ledar ya ce.