← Book details Dahuwar Kaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 81

Sashe 39

Dahuwar Kaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ai dama ku ba na ganinku sai idan uwarku za ta zo, ko ban isa a turo mini ku ba ne oho." Sadiya da Fauziya suka haɗa ido suka saki murmushi, Inna ta sake leƙen hannun Fauziya ta ga ba ta ga komai ba sai kuwa ta sake cewa.
"Kabirun ma kusan sati guda kenan ban gan shi ba, tun ranar da ya kawo mini garin tuwo da taliya. To dai nan É—in da ba kwa son zuwa, nan ne dai gidanku tun da ubanku ma a nan ya tashi. Kuma ni na haifi Kabiru babu yadda kuka isa ku yi da ni."
Shiru su Na'ima suka yi, saboda dama babban dalilim da ya sa ba sa son zuwa wurin Inna yawan faÉ—anta. Sau tari Fauziya za ta shirya su musamman ranar Juma'a ta cw su zo su gaida Inna amma suna zuwa ko zaman minti talatain ba sa yi suke tafiya. Wani lokacin ne ma suke zama su yi wasa da yaran Sadiya.

"Ke Salim ku zo ku É—auki tsintsiyoyin nan, ke kuma Zainabu ga mafitai ki É—auka. Yau idan kika sake ki yar munnda kuÉ—i wallahi sai ubanki ya biya ni kuÉ—ina."
Inna ta furta wa 'ya'yan Sadiya tana tura musu farantan da aka jera tsintsiya da mahutan. Sadiya ko kaÉ—an ba ta jin daÉ—in tallan da Inna take É—ora mu, don dai babu yadda za ta yi ne amma ba ta son tallar musamman ga Zainab da ta kasance 'ya mace.

"Inna ga wannan a yi wanki da shi babu yawa."
Fauziya ta zaro ledar daga kan cinyarta. Ina sai da ta ɗora wa su Salim farantin tsintsiya sannan ta waiga wurin Fauziya riƙe da baki ta ce, "Oh ke dai Fauziya ba kya gajiya, to an gode madalla. Ai kuwa kin ce na sha wanki, dama kayan sawata duka sun ƙare sai masu datti. Ai ka ga masu abin kirki, amma wasu kuya ko ƙullin gishiri ba su san su ba ni ba. Ke dai Allah Ya yi miki albarka, wannan ciki da kike ɗauke da shi Allah ya sauke ki lafiya ya sa ki haifo wa Kabiru magaji." Fauziya ba ta amsa ba, suna nan zaune suka ɗan taɓa hira. Fauziya tana son su keɓe da Sadiya amma tana tsoron fassarar da Inna za ta yi musu. Sun ɗan jima suna hira Inna ta ce, "To yanzu ni dai ragowar Taliya ɗaya gare ni ballantana na dafa mana abinci, ko da wuri za ku wuce ne Fauziya."
Girgiza kai Fauziya ta yi tana mamakin rayuwar Inna, Fauziya ta miƙe ta ce. "Yanzu za mu wuce Inna, dana zan je gaida Baba ne na ce bari na zo na gaishe ki." Nan take kuwa Inna ta hau washe baki ta ce, "To shi kenan ku gaida gida, shi kuma Kabiru ki ce masa ina son ganinsa." Fauziya ta amsa sannan ta nufi hanyar fita, da sauri Sadiya ta bi ta tana faɗin.
"Wai har za ku tafi, bari mu fita tare dama zan miƙa wa Mariya kayan wankin da na yi mata."

Da biyu Sadiya ta bi Fauziya suka fita, suna fita Fauziya ta ce. "Wai dama har yanzu su Salim ba su daina tallar muhucin nan ba?"
Sadiya ta haɗiyi yawu mai ɗaci ta ce, "Ai na kusa barin gidan nan Fauziya, wallahi na gaji haƙurina ya kusa ƙarewa."

"Idan kin tafi yaran kuma fa Sadiya?"
Cikin halin ko'inkula ta ce, "Allah zai raya su, wasu ma suna tasowa babu iyayen kuma su yi rayuwa kamar kowa."
Fauziya ta tsaya tana bin Sadiya da kallo, duk ta lalace saboda rashin kwanciyar hankali.
"Don Allah ki daina wannan maganar, addu'a za ki cigaba da yi har Allah Ya hore muku ku bar wa Inna gidanta. Kin san zama wuri É—aya dama yana kawo haka, ki cigaba da addu'a sai ki ga watarana sai labari."

"Hmmm ba za ki gane ba Fauziya, ni na san takaici da baƙincikin da nake ci a gidan."
Cikin ƙarfafa gwiwa Fauziya ta ce, "Babu abim da ya fi ƙarfin addu'a."

Fauziya da Sadiya sun jima suna tattaunawa sannan suka yi sallama, Fauziya ta wuce ta tari adaidaita sahu suka wuce gidan mahaifinta.A tsakar gida ta samu mahaifinta yana ta bambamin faɗa a kan 'yan nefa sun zo karɓar kuɗin wuta. Har ƙasa ta tsugunna ta gaida shi, sannan ta miƙa masa saƙonsa, nan take Baba ya shiga washe baki yana saka mata albarka. Ɗakin Inna Sakina ta shiga da yake a nan ɗakin aka raini Fauziya, bayan sun gaisa ta fara bin ƙannenta da alawoyi tana danƙa musu. Su Nai'ima kuwa dana tun a tsakar gida suka fara wasa da ƙannen mahaifiyarsu.

Kabir yana fita daga gida kai tsaye wurin masu sayar da ƙofa ya nufa, ƙofofin ba ƙaramin tsada ya ji sun yi masa ba. Ya cika da ragowar kuɗin wurinsa ya sayi guda ƙofofin guda uku, ƙofar farko ta ƙofar gida. Sai ɗakin da yake a tsakar gida, da kuma ƙofar falon gidan. Daga nan wurin can gidan nasa ya nufa, ya kira masu saka ƙofofi suka fara aiki. Ba su suka gama ba sai yamma liƙi, gabanin zai fito daga gidan kiran Hafsa ya shigo masa, zama ya yi a bakim dandamalin rijiyar sannan ya ɗauka.

"Gimbiyar mata!"

Ya furta cike da kashe murya, daga can ɓangaren Hafsa ta ce.
"An ya kana jin abin da nake ji kuwa?" Kabir ya sake kwantar da murya ya ce, "Haba Hafsyna, don Allah ki daina faÉ—in haka."
Hafsa ta ce, "Ka duba whatsapp É—inka na turo maka da hotuna."

Jikin Kabir har rawa yake ya katse wayar, sannan ya yi saurin buɗe datarsa. Yana shiga whatsapp ya fara cin karo da saƙonninta, buɗe hotunan ya yi ya ga ta ɗauko masa hoton ƙirjinta da ƙasanta kamar yadda ya buƙata. Cikin wani irin yanayi ya sake kiranta, a kunyace Hafsa ta ɗauka sai ta ji duk muryarsa ta sauya.

"Baby kin yi kyau sosai, amma don Allah ki yo mini bidiyo mana."
Hafsa da duk ta ji nauyinsa ua kama ta ta ce, "Baby gaskiya ka yi haƙuri, wallahi wannan ma da ƙyar na iya turo maka."

"Guda É—ai-É—ai fa kawai za ki yi mini, kuma kin san ai aurenki zan yi ko ba ki yarda ba?"

Shiru ya ji Hafsa ta yi, ya ɗora da cewa. "Akwai kuɗin da nake saka ran za su shigo mini nan da kwana uku. In Shaa Allah a satin naa za a kawo kuɗin aurenmu." Daɗi ya lulluɓe Hafsa, jikin yana rawa ta ce.

"Zan turo maka amma don Allah kana gani ka goge."

Cikin sauri Kabir ya ce, "Wallahi ina gani zan goge." Kashe wayar Hafsa ta yi ta shige É—akinta ta yi masa bidiyo ta tura masa. Kabir yana ganin bidiyon a ruÉ—e ya shiga yi mata replay da kalaman batsa, tun tana jin nauyinsa har ta fara biye shi.

Yamma liƙis Fauziya ta koma gida ta ɗora musu girki, a wannan karom ma ana yin magrina ta kira Kabir ta sake tuna masa maganar da suka yi game da alƙawarin da ya ɗaukar mata ba zai sake shan komai ba. Sannan ya ce ta yi tsala masa kwalliyar domin a cike yake da kewarta. Zuciyar Fauziya fes ta tsala wanka cikin wata doguwar riga marar nauyu, ta raba gashinta gida biyu kamar wata 'yar baby ba ƙaramin kyau ta yi ba. Suna nan zaune ita da yara kimanin ƙarfe tara suka ji sallamarsa. Kusan lokaci ɗaya ita da yaran suka rungume shi har ita suna faɗin.

"Abi oyoyo."

Rungume su ya yi gabaɗaya, sai Fauziya ta saci kallon yadda suke nishaɗi ita da yaran saboda dawowarsa da wuri kuma a cikin nutsuwarsa, sai ta ji ƙwalla tana shirin zubo mata. Ɗaya bayan ɗaya ya tsugunna yana sumbatar yaran a goshi, sai ya ɗago ya dube ta suka haɗa ido. Rungumo ta ya yi jikinsa yana kashe mata ido ɗaya, irin kallon da take bin sa da shi ya sa shi hura mata iska a fuska.

"Wannan kwalliyar zan biya tukwicinta an jima."

Ya furta matana hankali, ta sakar masa murmushi ta ce.
"Na fa tsufa da yawa."
Kafaɗa ya maƙale mata cikin kwaikwayon muryarta ya ce, "Ni ban yarda ba." Duk da yaran ba su fahimci me suka tattaunawa ba, jin yadda mahaifinsu ya maƙale murya ya sa suka fata ɗariya.

Hula, agogo da wayarsa ya ajiye a gefen gado ya ɗauki bokiti ua zuba ruwa ya tayi yin wanka. Kabir ya manya shaf da abin da Hafsa ta turo masa bai goge ba har ya iya ajiye wayarsa, kuma ya bar hotunan ne saboda udan ya keɓe ya dinga kalla yana jindaɗi.

Fatima ce ta É—auki wayar ta shi, da yake wani lokacin idan yana gida ya kan kunna musu game ko cartoon su kalla. Shige-shige suka fara yi masa har suka shiga cikin gallery É—insa, Na'ima tana ta zura kanta ta danna É—aya daga cikin bidiyon da Hafsa ta tura masa. Fauziya da ke tsugunne tana jera masa kayan abin ci ta ji muryar mace raÉ—au a kunnenta tana faÉ—in.

"Baby kana gani, wannan bidiyon..."

A giguice Fauziya ta fisge wayar daga hannunsu jikinta yana karkarwa, sakamakon ji irin bayanin batsar da buduwar take yi. Domin a bidiyon hafsa tana yi masa tana bayanin komai dalla-dalla.

"Lah Mami mene ne wannan?"

Na'ima da ta fi su wayo ta tambaya, sai da Fauziya ta saita nutsuwarta ta ce, "Bidiyin wata marar lafiya ne da take neman taimako, za a haɗa mata kuɗi a yi mata magani. Na sha faɗa muku idan mutum ya ajiye abu sai an tambaye shi ake taɓawa ko?"
Gabaɗaya suka gyaɗa mata kai, Fauziya fa take jin wani abu yana taso mata a ƙirji ta yi ƙarfin halin faɗin.

"To daga yau, ko da wasa ka da na sake na ƙara ganin ku taɓa wa mutum wayarsa. Idan ba haka ba ranku zai ɓaci." Su Fatima suka amsa mata.
Chapter 39 · 0% Book details