← Book details Dahuwar Kaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 81

Sashe 55

Dahuwar Kaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baba Ibrahim ya sauke ajiyar zuciya cikin takaici ya cigaba da cewa.
"Yaya da ace kuɗaɗen nan da kake kashewa a sayen magungunan tara su kake, da ko nauyin karatun yara ka rage da su. Amma ka bar yara haka, hatta makarantar allo ba duka ne suke zuwa ba. Kuma saboda Allah ga shi nan, kullum wasu ƙananan ƙwayayan ake sake ƙyanƙyashe maka."
Baba Inu ya É—ago fuska a haÉ—e ya ce, "Ka gama ubana? Idan ba ka gama ba na yi shiru ka cigaba."
Baba Ibrahim ya furzar da iska mai zafi ya ce.
"Na gama."

"To shige ciki ka ba ni wuri, ashe shi ya sa ka kwaso fuska kamar akwatin zaɓe ka zo ka tsaya mini a ka. Wallahi Iro ka fara ba ni tsoro, da ace kana da iko na tabbata da sai ka yi duk yadda za ka yi domin ka turmushe mini ƙwaiƙwayen haihuwa. Amma ka don kanka, na lura baƙinciki da hassadar ne fal ranka. Allah bai hore maka irin ƙwaiƙwayen haihuwa masu yawa da albarka kamar ni ba."

Bab Ibrahim a fusace ya ce, "Wallahi gaskiya ka faɗa, yadda kake sakin jiki kai da matan da kake aura kana saki da ina da iko sai na farke ka na ƙone maka su kowa ya huta. Tun da haihuwar kawai ka sani ba ka san jidalinsu ba."
A ɗan tsorace Baba Inu ya dafe ƙirji, yana bin Baba Ibrahim da wani irin kallo ya ce.

"Kai dai Iro an yi mai mugun hali, mugun bakinka ya faɗa kanka. Sai ja je ka yi ta fama da 'ya'ya huɗu, ni kam haihuwa yanzu na fara tun da ban san mai jin ƙaina ba."

Ganin Baba Inu bai É—auki zugar Baba Ibrahim ba ya sa Mai maganin ya zuro kai ya ce.
"Ai mai gida shi ya sa a kullum idan za mu fito, muke addu'ar neman tsari miyagu irinsu masu hana a yiwa bayin Allah ciniki." Takaici ya sa Baba Ibrahim ya shige cikin gida ba tare da ya tanka musu ba. Saboda halin yayan nasa ba ƙaramin ɓata masa rai yake ba.

Baba Iro yana shirin yin magana daga soron gidan ya ji, gijif! Kwacakwar! Alamar ana jan kaya a buhu. Baba Saleh ne ya fito da ƙaton buhun magungunansa, ganin motar mai magani a ƙofar gidan ya sa ya murtuke fuska yana harare-harare cikin habaici ya fara waƙa.

Komai baƙin cikin tsololon ƙato.
Wallahi sai dai ya yi ƙototo.
Na zama kainuwa a wannan loto.
Ƙaryar mai baƙinciki ya ga bayana, har masu ƙin sayan maganina.

Yana gama faɗar haka ya fizgo ƙaton buhunsa da yake ja da ƙyar, sai ga shi bisa tsautsayi ya fiszo da ƙafar bencin da Baba Inu yake kai. Bencin ya yi gaba shi kuma Baba Inu ya hantsila ta baya ji kake darr ya yi zaman 'yan bori a ƙasa.
Kamar bai san da shi a wurin ba Baba Saleh ya saki buhun hannunsa yana rafka salati sannan ya ce.

"Wai Yaya dama kana nan ƙofar gida? Ikon Allah sannu!"
Ya ƙarasa maganar yana ƙoƙarin riƙo hannun Baba Inu, da sauri ya bige hannunsa rai a ɓace ya ce.

"Wallahi duk baƙincikin mutum bai isa ya ga bayana ni Inusa don uban mutum! Haka zan daɗe na yi ƙarko shekaru irin na dabino, sai na ga bayan maƙiyana. Kai mai magani, ungo dubu biyar ka yi mini haɗin komai da ruwanka."
Baba Inu bai yi niyyar sayen maganin dubu biyar ba, amma don ya ɓa ta wa Baba Saleh rai ya yi haka. Baba Saleh ya buga tsaki yana wurgawa mai maganin harara, ya nufi wata tsohuwar motarsa da yake tallan magungunansa, ya buɗe ya tura buhun maganin da ke cike da jarkokin magani sannan ya rufe.

Inna ce ta fito daga gida a fusace hannunta riƙe da Laraba, ta dubi Baba Inu bayan sun yi sallama da mai maganin ta ce.

"Inu na gaji da cin kashin da ake yi mini a cikin garin nan."
Da mamaki Baba Inu ya dube ta ya ce, "Me aka yi miki Inno?"

"Ba ni aka yi ba Laraba aka yi wa, kuma duk wanda ya yi wa Laraba ni ya yi wa. Mai gari ne yake son ganina da ita, wai Laraba ta tare ÆŠahe É—an gidan Sa'a mai ragadada ta cinye masa. Saboda Allah ina Laraba za ta kai ragadada cikin É—an bokiti ban da son zuciya?"
Jin haka ya sa Laraba ta juya gefe a fakaice ta sake suÉ—e hannunta da ya yi shanana da miyar ragadada.
Baba Inu ya zuba mata ido ya ce, "Wallahi duk abin da aka ce mini wannan hatsabibiyar yarinyar ta yi ba zan musa ba, shi ya sa tun da satin nan ya kama nake jiran shigowar Uwar marayi garin nan. Wallahi babu abin da zai hana Laraba zuwa birni, ta je can ta yi aikatau ko na huta da takaicinta. Ni duk cikin 'ya'yana babu sai siffar 'ya'yan aljanu irinta."
Wani irin haushin Baba Inu ya kama Inno, sai kawai ta ja hannunta suka wuce wurin mai gari.

Tun daga nesa da aka hango Inno tafe da Laraba ƙananan maganganu suka fara tashi a fadar mai gari. Sanƙira ne ya yi magana sannan kowa ya yi shiru. Da sallama Inno ta zauna a kan tabarmar fuska a haɗe ta ce.

"Allah Ya taimake ka, na ji wai kana nemanmu ni da Laraba!"
Mai gari da tun da Laraba ta zauna yake bin ta da mugun kallo ya ce, "Wai ne ma Inno?"
Ya mayar da kallonsa wurin Laraba ya ce.

"Ke Laraba waye wannan?"
Laraba ta yi kicin-kicin da fuska tana duban ÆŠahe kamar ba ta gane shi ba ta ce, "Ban san shi ba, amma na ga yana yi mini kama da 'ya'yan Baraka mai hancin salansa."
Haushi ya sake cika Mai gari ganin irin rainin hankalin da Laraba ta yi masa. Ya sake nuna Huwaila wacce ta kai ƙarar Laraba, a kan ta jefa mata bokiti da guga a cikin rijiya. Laraba ta sake ƙanƙance ido ta ce.

"Wannan kam Lado ƙeya ne!"
Sai kuma Laraba ta washe baki ta ce, "Lado ƙeya dama ka dawo daga Legas?"
Haushi ne ya lulluɓe mai gari, mutanen wurin wasu suka fara dariya yayin da wasu kuma haushin Laraba ya cika su, don kusan duka mutanen garin babu wanda ba shi da tabon ɓacin ranta.
Tsam mai gari ya taso ya zo gaban Laraba, a tunaninta tambayarta zai yi sai ji ta yi ya zabga mata gigitaccan mari, har sai da ta ga waɗansu taurari sun gilma mata. A razane Laraba ta dafe kunci saboda marin ba ƙaramin zafi ya yi mata, amma sai ta basar don ba ta san ta kunyata kanta a gaban mutanen garin. Ta sake basarwa ta sake ba shi irin amsar da ta ba shi da farko. A wannan karon ma haushi ya sa Mai gari ya sake ɗauke fuskarta da mari, abinka da farar fata lokaci ɗaya fuskarta ta yi jajir. Ganin haka ya sa ran Inno ya ɓaci ta dube shi a fusace ta ce.

"Wallahi Sama'ila ka kiyaye ni, jikata fa ba jaka ba ce..."

"Ai dama duk wani iskanci da yarinyar nan take yi ke ce kike É—aure mata, wallahi mai gari sisina ba zai yi ciwon kai ba sai an biya ni ragadadata. Har kayan miya da mahaÉ—i kusan dubu biyar na kashe."
Sa'a mai ragadada ta faɗa a ƙufule.
Cikin tsoratarwa da burgagi Mai magari ya miƙe tsaye yana buɗa kafaɗu ya ce, "Inno tun da haka kika ce, bari na aika ku birni wurin hukuma ta yanke mata hukunci. Kin ga idan aiƙali ya ji irin tuhume-tuhumen da ake yi mata ƙila ma ya aikata gidan yari."
Jin haka ya kaÉ—a hantar cikin Inno, hankali a tashe ta zungoro Laraba ta ce.
"Ke Laraba ki yi magana."

Laraba ta yi wa Mai gari ƙuri tana yi masa kallon ba ka daki banza ba, har sai da cikinsa ya kaɗa amma sai ya basar ya ce.

"Laraba kin tare Ɗahe kin cinye masa ragadada kin tula masa ƙasa a ciki, ita kuma Huwaila kin jefa mata guga da bokita a rijiya yanzu da kin jefa ta ciki me za ki ce?"
Laraba ta wurga wa Huwaila harara ta ce, "Kai Lado ƙeya tun da ka dawo garin nan yaushe muka haɗu da kai!"
Huwaila ta fashe da kuka cike da takaici ta ce, "Mai gari kana ji tana mayar da ni Lado, yanzu Laraba ta rasa da wa za ta haɗa ni sai Lado ƙeya?"

Mai gari ya kalli Sanƙira yace ya tsinko masa itacen dalbejiya ya zuge masa ganyenta. Jikin Sanƙira har rawa yake ya haye bishiyar da ke gefensu, ya fisgo manyan reshe ya zuge ya miƙa wa mai gari. Kafiya da taurin kan Laraba ya sa ko gezau ba ta yi ba, duk da gabanta sai faɗuwa yake yi.

Rai a ɓace Mai gari ya shiga rafta mata ta ko ina, mutanen wurin suka marmatsa don kar a same su. Tun Laraba tana daurewa har dauriyarta ta ƙare ta fashe da kuka tana mutsu-mutsu. Inno ban da kuka da kururwar neman taimako babu abin da take yi.

Yaran da suke zagaye da su ne suka fara tafi suna tsalle da waƙa, saboda tun da suke ba su taɓa ganin abin da ya saka Laraba kuka ba.

Laraba mai kuka ye ye.
Ga majina da yawu ahayye.
Gobe ma ta ƙara ye ye.
Ku zo mu yi mata ɓarɓaɗan tusa a tsakar ka.

Idan suka kai baitin waƙar sai su ƙarasa su dunguro kan Laraba da ke shasshekar kuka.
Mai gari sai da ya gaji don kansa sannan ya koma kujerarsa cike da son nuna birgewa ya ce.
"Duk wanda ya sake aikata makamancin abin da Laraba ta yi, hukuncin da za mu yi masa kenan. Ina Inno take?"

Cike da jin haushi a daƙile Inno ta ce, "Ga ni."

"Za ki biya Huwaila da Sa'a kuɗin ɓarnar da Laraba ta yi musu." Inno ta yi tsagal ta ce.
Chapter 55 · 0% Book details