Sashe 50
Dahuwar Kaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
GIDAN INNA
Wani irin ɓacin rai ne ya lulluɓe zuciyar Fauziya, rai a ɓace ta miƙe tsaye tana ɓalle maɓallin rigarta. Shi kansa Kabir bai ji daɗi ba, cikin tausasa harshe ya ce. "Don Allah ki yi haƙuri Fauziya." Fuska babu walwala ta ce, "Babu damuwa."
Ya ɗan leƙa fuskarta ya ga har lokacin babu alamar fara'a, duk sai ya ji babu baɗi.
"Kin san iyaye wani abin sai ana haƙuri da su." Ya furta a sanyaye.
"To ni me na ce Kabir? Ka je idan ka gama sai ka ci abincin."
Fauziya ta furta bayan ta zura doguwar rigar bacci, can gefen katifa ta koma ta kwanta. Kamar Kabir zai yi mata magaba sai kuma ya fasa ya nufi ɗakin Inna. A bakin gado ya samu Inna da alama ta gama cika, ya zauna a ƙasa ya ce.
"Gani Inna."
"Kai ma ashe sakarai ne Kabiru ban sani ba? Don Allah kai ba ka ji kunyar kanka ba, a ce tun farkon dare ka naniƙe 'yar mutane a ɗaki? Kai Allah dai ya sawaƙe da wannan jaraba ta 'yan zamani."
Shiru Kabir ya yi, sai ya ji kunya duk ta kama shi. Inna ta taɓe baki ta ce, "To dama kuɗinka na wurina nake son na ranta, idan ba amfani za ka yi da su ba. Na ji an ce barkono ya sauko a ƙauye zan saro na dinga ƙulla wa yaran nan." Da sauri Kabir ya ɗago ya ce, "A'a Inna, dama na ce ki adana mini su ne saboda ban samu ciko ba. Amma zaman da muka yi da Fauziya, yanzu ta ba ni keken ɗinkinta, idan na sayar da shi sai na haɗa kuɗin suka cike dubu ɗari. Idan ya so sai a tura su Yaya su kai kuɗin, don Allah Inna kada ki taɓa ko sisi, wallahi yayan yarinyar nan ne ya ba ni sati biyu. Idan ban tura ba zai iya aura mata wani."
Inna ta wara hannu ta ce, "Ai ka ga matar rufin asiri, wallahi da Sadiya ce sisi ba za ta ba shi ba. To idan an kai kuɗin auren wai a ina za ka saka ta, ban da abin ka ai da bari ka yi ka kammala gidanka tukunna. Ka ga lokacin hidima ta yi maka sauki, don ma kai Allah Ya haɗa ƙashin arzikinka da na matarka"
Tagumi Kabir ya zuba da hannuwa biyu ya ce, "Wallahi ni ma haka na so Inna, to yayanta ya matsa ne. Haka ta kira ni tana kuka wai zai aura mata wani É—an uwansu idan ba ta fitar da miji ba."
A gwasale Inna ta ce, "To dama mene ne ribar yawan zancen idan ba aure za a yi ba? Ai gara a yi wacce za a yi a wuce wurin."
Kabir ya tashi daga wurin da yake zaune, ya hau kan gado gefen Inna ya riƙo hannunta, sannan ya yi ƙasa da murya ya ce.
"Amma wata alfarma nake nema a wurinki Inna, don girman Allah ki cewa su Yaya kada su faÉ—a wa matansu. Don ina gudun kada Fauziya ta ji labari, da so samu ne ma har sai bikin ya matso tukunna."
"Idan ta ji uwarka ce da za ta hana ka aure? Ko kuma ƙanwar uwarka ce ita?"
Kabir ya miƙe tsaye cikin tsoron kada Fauziya ta ji ya ce, "Don Allah Inna ki yi shiru kada ta ji, kin san fa yadda aka yi wurin sayen filin gidan can da kuma ginin. Wallahi idan ta sani tana iya cewa Surayya ba za ta zauna a gidan ba, tun da haɗa su nake son yi.."
"Mtsswww."
Inna ta ja dogon tsaki ta cigaba da cewa, "Amma dai wallahi an yi lusarin namiji, shashasha da bai san ciwon kansa ba. Saboda ta sayar da firjinta ta ba ka ka sayi ƙofofi, sai ta hana ka yin aure? Wai me ya sa kake son zama sakarai hotiho ne Kabiru? Kai ne fa miji ba ita ba, wai dama haka ka lalace a wurin yarinyar nan ban sani ba?"
Kabir ya saka hannu yana kare bakinsa alamar Inna ta yi shiru, ya sake kwantar da murya ya ce.
"Ba fa kuɗin firji nake nufi ba, wannan ai na ƙarshe-ƙarshe ne da ta ba ni. Kin manta na ce miki kuɗin gadon wurin mahaifiyarta ne, ta ba ni muka haɗa da kuɗin wurina muka sayi filin, to a ginin ma akwai kuɗaɗen da ta ara mini sai daga baya ne ta ba ni na firji."
Jin kalaman Kabir ya sa Inna ta taɓe baki ta ce, "To sai me? Kai dai an riga da an shanye ka wallahi."
Kabir da ya lura Inna ta ɗauki zafi kuma tana iya tsula wa kwaɓarsa ruwa, sai ya shiga rarrashinta. Sannan ya nuna mata da ta gargaɗi 'yan'uwansa a kan maganar auren, har ya samu ya shawo kanta.
A lokacin da ya koma ɗaki Fauziya tuni ta yi bacci saboda gajiyar aikin da ta sha, cikin sanɗa ya sake jan ƙafa ya fice daga ɗakin sai ya nufi hanyar fita.
A bayan layinsu ya tsaya ya zaro wayarsa ya latsa lambar Surayya, bugu É—aya wayar ta yi ya ji ta É—auka muryarta da alamun bacci.
"Baaabyyy."
Jin yanayin muryarta ya sa jin wani irin yanayi, ya kwantar da murya yana raɓewa a jikin bango ya ce.
"Baby wannan muryar tana azabtar da ni."
Surry ta saki murmushin ƙeta ta ce, "Kamar yadda taka take hargitsa ni ba."
"Albishirinki zumata."
Cikin sauri Suryy ta ce, "Goro My."
"In Shaa Allahu a satin nan su Yaya za su kawo kuÉ—in aurena gidanku."
Farinciki kwance a saman harshenta ta ce, "Don Allah da gaske?"
"Zan yi miki wasa ne?"
Kamar tana gabansa ta girgiza masa kai, Kabir ya cigaba da cewa.
"Ina tunanin har da rana za a saka, kafin nan da shekara guda In Shaa Allahu na gama haɗa lefe." Surry ta sake kanne murya ta ce, "Na ji daɗi sosai sadaukina, ina ƙaunarka masoyi."
Shi ma Kabir ya kwantar da murya ya ce, "Na yi kewar komai naki."
"Surayya da komai mallakinka ce Kbna."
Wata sabuwar soyayyarta ce ta sake mamaye shi, ya gyara tsayuwarsa haɗe da sakarwa wayar kiss kamar yana tare da Surayyan. Sun jima suna musayar daɗaɗan kalamai, sai da dare yayi sosai sannan suka yi sallama Kabir ya koma gida. Yanayin da Surayya ta jefa shi a ciki ne ya sa bayan ya gama cin abinci, ya lallaɓe jikin Fauziya domin ya rage zafi. Duk da ya so a ce Surayya ce a maƙale a gefensa, amma a haka ya samu da ƙyar Fauziya ta ba shi haɗin kai. Domin gani take ko yaya suka yi motsi Inna za ta iya gane halin da suke ciki.
Washegari tun da farar safiya ta fara jiyo hayaniyar Sadiya da mijinta, tun suna yin faÉ—an da cacar baki a cikin É—aki har suka fito tsakar gida. Kamar Fauziya ta danne kada ta fita, sai ta ji kamar dukanta Sadiya Yaya Nura yake yi.
"Wallahi ba zan taɓa yafe maka ba, Allah sai ya saka mana."
"Kada ki yafe mana, ai wallahi na yi nadamar aurenki."
Cikin kuka ta ji Sadiya ta ce, "Ni zan faÉ—i haka don wallahi na gama zama da kai har abada."
Da sauri ta fita tsakar gidan tana faÉ—in, "Subhanallah me yake faruwa haka?"
Wurin Sadiya ta ƙarasa da ke yashe a ƙasa tana kuka, a daidai lokacin Yaya Nura ya fito yana faɗin.
"Ki tarkata komatsanki ki koma can baƙin garinku, na ƙarashe ragowar igiyar aurenki a kaina. Na saki, yau zan yi bacci da saleɓa."
Sadiya ta fisge hannunta daga jikin Fauziya ta ce, "Sai me? Ai wallahi da wannan ƙaddararran auren na ka gara na ƙarasa rayuwata a haka."
A wannan lokacin Kabir ya fito daga banÉ—aki ya ce, "Haba Yaya, a gaskiya abin da ka yi sam bai dace ba. Aunty Sadiya ba ta cancanci haka daga wurinka ba, ga duka ga saki abin ya yi yawa."
"Æarauniyar za ka ce na cigaba da zama da ita? Me ake da mace É“arauniya ana zaune Æ™alau, ni wallahi da na san haka zuri'arsu take ta É“arayi; wallahi da ban auro ta ba. Haka kawai ta zo ta gurÉ“ata mini zuri'a da mugun hali."
Inna da tun farko take ɗaki tana sauraronsu, sai a lokacin ta leƙo ta ce.
"Ai wallahi ya yi mini daidai, saboda Allah Sadiya duk ta raina yaron nan. Miji wasa ne? Abin ya kai har da sata, yara gasu nan su uku ne Allah ya raya su."
Mamaki ne ƙarara ya lulluɓe Fauziya, don son zuciyar Inna a bayyane yake ƙarara. Duk wanda ya ga Sadiya ya ga halin da take ciki ya san ba ta jin daɗin gidan aure. Cikin tsantsar tsana Sadiya ta miƙe ta isa gaban Inna zuciya tana suya ta ce, "Ai dama 'ya'yanki ba sa laifi, amma ki sani ki bar ganin 'ya'ya maza duk gare ki. In Shaa Allahu sai kin ga sakayyar son zuciyar da kika nuna mini, shi kuma yadda ya azabtar da ni da yunwa haƙƙinmu ba zai bar shi ba. Sata kuma da ake iƙirari ko gaban malamai na je hukuncin sata ba zai hau kaina ba. Saboda abinci ya hana mu, ni kuma na shiga rumbunsa na ɗiba zan girka mana shi ne ya rufe ni da duka. Allah Ya ba ni wanda ya fi ka, domin kai ba mijin aure ba ne."
Yaya Nura ya saki dariyar izgilanci ya ce, "Kina fama da gajartar ne za ki samu wanda ya fi ni, ai ni ma tsautsayi ne ya taɗe ƙafafuwana har na faɗo kanki. Ki tashi ki fice mana daga gida, kuma kada ki sake ki ɗaukar mini 'ya'ya."
Tuni hawaye ya wanke Fuskar Fauziya ta ce, "Sadiya wai mene ne haka kuke yi a gaban yara ne?" Ta kalli yaran Sadiya da su Na'ima da suka yi carko-carko, wasu daga cikinsu suna hawaye.