Sashe 78
Dahuwar Kaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Lokacin da su Uwale suka samu labarin abin da ya faru ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba, abin sai ya haɗe mata goma da ashirin ga halin da Ɗan Bishir yake ciki, da zargin da ake yi ya kwashi cuta mai karya garkuwar jiki ga kuma halin da mijinta yake ciki. Da yake dawowar Baba Ibrahim kenan daga wurin aiki, ko gidan bai shiga ba ya ce wa Uwale ta koma shi zai je ya ji abin da yake faruwa. Kai tsaye ƙaramin asibitin gwamnati ƙauyen nasu ya wuce, a can ya samu Baba Sale ana yi masa ƙarin ruwa . Da yake an yi masa allurar bacci sai ya zauna a gefensa yana jiran tashinsa. Kusan zaman awa guda Baba Ibrahim ya yi, sannan Baba Sale ya buɗe idonsa.
"Sannu Sale, ya jikin naka?"
Baba Sale ya tashi zaune yana dafe kansa da ya yi masa nauyi, ya dubi Baba Ibrahim murya tana rawa ya ce. "Yaya ka ji abin da ya faru ko?"
Ya gyaɗa masa kai ya ce, "Sale ina son ka saurare ni da kyau don Allah. Na farko dai kai musulmi ne, ka yarda da ƙaddara mai kyau da akasinta. Sannan ka san Ubangiji ne ya ba ka Ɗan Bishir, a lokacin da ba ka yi tsammani ba. Don haka kenan ko a yau Allah Ya yi niyyar ɗauke abinsa zai iya. To me zai sa ka kashe kanka a banza da wofi, ko ka janyo wa kanka ciwo ya kwantar da kai. Lokacin da na zo likitoci sun tabbatar mini ko a asibitin nan ka yi suma ya fi bakwai, don Allah ka kwantar da hankalinka. Yanzu ina son daga nan zan wuce na je na samu Bala Wanzan, da shi Idi Naira na ji yadda aka haihu a ragaya. Idan na ji ta bakinsu sai mu wuce asibiti ɗungurungum a yi haihuwa da hanji, amma babu yadda za a yi a dinga faɗar cuta da fatar baki ba tare da an tabbatar ba."
Da sauri Baba Sale ya riƙo hannunsa ya furta. "Yaya zan bi ka, gara a yi komai a kan idona."
Baba Ibrahim ya sake haÉ—ai rai ya ce, "Idan ka san za ka yi mini hayaniya ko ka je kana sume-sume gara ka yi zamanka a nan."
Cikin sauri Baba Sale ya girgiza kai, Baba Ibrahim ya yi wa lokitocin bayani sannan ya biya su kuÉ—in ruwa da alluran da ake yi masa; suka wuce Police station.
Bayan sun gaisa Baba Ibrahim ya gabatar da kansa sannan ya É—ora da cewa.
"Yallaɓai zuwa na yi domin na ji kan zancen abin da ya faru, idan da yuwuwar zuwa asibiti a yanzu sai mu wuce gabaɗaya."
Sergent ɗin da ke tsaye ya buɗe wani file ya zaro takarda ya ce, "Alhaji wani mutum mai suna Malam Shehu mai doya shi ya kawo ƙarar Bala wanzan, yana tuhumarsa da cin zarafinsa bayan ya je ƙofar gidansa. Sannan laifin da Bala ya yi har da zagin ɗaya daga cikin ma'aikatanmu, abin da kuma ya sake dagula case ɗin zargin cutar HIV da ake yi wa Alhaji Idi Naira. Yanzu haka shi ma Idi ya kawo Malam Shehu wurinmu, a kan zargin yana ɓa ta masa suna da wannan cutar." Ajiyar zuciya Baba Ibrahim ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Yanzu za mu iya ganin Bala Wanzan ɗin?"
"Gaskiya sai dai zuwa gobe idan Allah Ya kai mu." ÆŠansandan ya furta.
Babu yadda suka iya haka suka wuce gida, sai dai kaso talatin a cikin ɗari na damuwar Baba Sale ta ragu, saboda ya ji an ce Alhaji Idi Naira ya yi ƙarar Malam Shehu zai ɓata masa suna.
Mai Yasin tun da ya saka 'Yar gwal a idonsa soyayyarta ta dawo masa sabuwa fil a ransa, haka a ɓangare ɗaya kishinta ya mamaye shi, yana jin tsanar Ɗanladi a ransa don dai kawai yana shakkarsa ne. Yana daga ɗakinsa ya hango ta, ta nufi banɗaki da buta a hannu shi ma ya yi zaraf ya ɗauki buta ya rufa mata baya. Tana shiga banɗaki za ta turo ƙofa ta ji mutum yana ƙoƙarin turowa, suna haɗa ido ta saki murmushi irin na 'yan bariki ta ce.
"Mai Yasin namu, ashe a wannan lungun ka lafe?"
Mai Yasin ya riƙo hannunta ya ce, "Ga ni kuwa kin gani, wai dama 'Yar gwal za ki iya auren wani namijin ba ni ba?"
'Lallai wannan gafalallan tsohon naka wasa ne.' Ta raya a ranta, amma a fili sai ta ce.
"Ka da ka sake kallona a matsayin matar aure, saboda wannan auren nawa shi da babu duk ɗaya. 'Yar gwal ta auri Ɗanladi ne domin ta yi masa tatsar mai, idan ta kwashe albarkar aljihunsa sai ta ƙara gaba."
"Sai da ke 'Yar kunama!"
Mai Yasin ya yi maganar yana dariya, sannan ya yi ƙasa da murya ya ce. "Yanzu ni ya za ki yi da ni?"
"A'a ka ji da tsohuwar da ka samu, idan fa muka bari suka san alaƙarmu na rantse da Allah ni da kai sai dai mu yi biyu-babu. Kawai mu cigaba da sabgarmu, kowa ya wawuri abin da ya wawura ko a fakaice ma dinga haɗuwa."
Guntun tsaki Mai Yasin ya ja, ya ce. "Wa yake ta wata tsohuwa? Ƙila dai a rashinki yau na waiwayi haƙƙina a wurinta."
'Yar gwal ta saki dariya, sannan ta ce ya yi maza ya tafi don kada wani ya gansu.
Bayan 'Yar gwal ta koma a tsakar gida ta ci karo da Laraba tana 'yar carafke, tana shiga ta É—ebo wankin rigunan mama da É—an kamfai ta wurga mata a fuska. Tsaminsu haÉ—e da warin man bilicin É—in da 'Yar gwal take shafawa ya bigi Laraba, ta ture su tana yamutsa fuska.
"Ke! Wanke mini su yanzu, ina son su fita sosai." Da mamki Laraba take kallon ta.
"Ko ba za ki wanke ba? Kika zubo mini ido irin na marasa tarbiyya kina kallo."
Laraba ta tashi ta ɗaga wani wargajejen ɗan kamfai, sai kawai ta tuntsire da dariya. Tun tana dariya a tsaye har ta tsugunna, ta janyo wata warɓeɓiyar rigar mama ta ɗago ta ta sake kwanciya tana dariya.
"Don uwarki dariya ma za ki yi mini? Wato ni za ki mayar 'yar iska?"
Laraba ta tsagaita da dariya tana ɗan tsuke fuska ta furta. "Kambu... Kada ki sake zagin uwata tana ƙasa, ki zagi kowa nawa ban ta uwata wallahi. Ehe, ba dole mutum ya yi dariya ba wannan ai ya isa na yi hijabi da shi."
"Rashin kunya za ki yi mini?" 'Yar gwal ta ƙarasa gaban Laraba a fusace. Laraba ta juya mata baya tana ɗago ɗankwalinta gaba ta ce.
"Faɗa wa ƙeya ɗankwali ya ba ki amsa 'yan mata."
Laraba tana juyowa 'Yar gwal ta wanke ta da mari, a hargitse Laraba ta ɗago za ta yi magana Ɗanladi ya ƙarasa yana faɗin.
"Kin yi mini daidai sanyin zuciyata, wato har yanzu kina nan da iskancinki ko Laraba? Maza wuce ki kwashe su ki wanke kada ranki ya ɓaci." Idon Laraba ya yi ja saboda ɓacin rai, ta harari 'Yar gwal a hankali ta ce.
"Allah Ya isa ban yafe..."
Tun ba ta gama magana ba, kamar haÉ—in baki ÆŠanladi da 'Yar gwal suka make bakinta, nan take bakin ya fashe amma a dole ta kwashe kayan, ta fara wanki saboda yadda ÆŠanladi ya ciro belt zai zane ta da shi. Sai da ta yi wa kayan ruwa kusan huÉ—u kowanne 'Yar gwal tana cewa bai wanku ba, sai a na biyar sannan suka bar Laraba ta fara shanya a lokacin har an fara kiran sallar isha'i.
Jin shirun Laraba ya yi yawa ya sa Inno ta fito daga sashenta, tana zuwa harabar ta ci karo da ita tana shanyar kaya su ÆŠanladi suna tsaye a kanta.
"Laraba me kike yi haka da daren nan?"
Murya tana rawa Laraba ta ce, "Wanki."
Inno ta ƙanƙance ido ta ce, "Mene ne wannan kamar ɗan diras? Ke wuce ciki mu je."
Da sauri Laraba ta saki na hannunta ta wuce ciki, Inno ta dubi Ɗanladi rai a ɓace ta ce.
"Ba baiwa aka sayo muku ba, tun da ba ka da mutumci haka matarka ma ba ta gaji arziki ba wallahi ba za ku mori Laraba. Mun kwana a gida É—aya, amma ban da mutumci da za ku zo ku gaishe ni." Inno ta wuce sashenta a zafafe.
Ran Laraba ya ɓaci sosai, ita kanta ta san a banza ma tana dafa mutum da ruwan jikinsa har ya nuna, ballantana sun taɓo ta da kansu. Don haka ta ci alwashin yadda suka azabtar da ita sai ta rama.
Tun da dare ya fara yi Laraba ta fara zarya, tana saka da warwarar abin da za ta aikata, tana wucewa ta ga 'Yar gwal a ƙofar ɗaki tana dama kunun gyaɗa. Da sauri ta faɗa ɗakin Inno, a can drower madubi ta buɗe ta ciro wani maganin hawan jinin Inno, mai saka bacci ta ɓallo guda takwas. A ƙa'ida Inno ɗaya take sha a wuni guda, kuma a hakan ma bacci yake saka ta sosai. Bayan jininta ya sauka ne aka sauya mata wani, don haka ta daina shansa. A cikin ƙaramar farar leda ta zuba su ta ɗebi ruwa kaɗan ta zuba, sai da ya narke sannan ta fita cikin sa'a kuwa ta ga 'Yar gwal ta shiga ɗaki. Da sauri ta matse maganin a cikin jug ɗin kunun, ta juya cikin sauri ta bar wurin. Tana laɓe a bakin ƙofar Inno tana leƙe ta ƙofa, ta ji lokacin da 'Yar gwal ta ɗauka ta shiga ɗaki. Zuciyar Laraba ƙal da haye katifa ta kwanta, tana shirya irin muguntar da za ta yi musu. A fili ta saki dariya, Inno ta wurga mata harara sannan ta ɗauki furar Mai Yasin ta nufi ɗakinsa.