Sashe 28
Dahuwar Kaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
BABA MALAM
Da mamaki Baba malam ya dubi Shukura ya ce.
"Lafiya dai na ga kina hawaye? Hajiya ko wani abin ne ya faru?" Ya tambaya yana kallon Mama da ke zaune a gefe, girgiza kai ta yi ta ce.
"Babu abin da ya faru Alhaji, na ji dai ta ce Daddyn Mami yana asibiti babu lafiya. Ban sani ba ko jikin nasa ne, amma dai tun da ta shigo take hawaye."
Baba malam zai yi magana Shukura cikin kuka ta ce.
"Don Allah Yaya ku gafarce ni, ku yafe mini ku yafe wa Daddyn Mami. Wallahi yanzu haka yana can a asibiti rai a hannun Allah. Don Allah ka yafe mini Yaya, na san gabaÉ—aya kowa ya tsane ni saboda abin da ya faru."
Jin rashin lafiyar Daddy ya sa gaban Baba malam ya faÉ—i, amma gudun kada ya nuna wa Shukura damuwarsa sai ya ce.
"Tun daga haihuwar mutum dama ai ransa yana hannun Allah Shukura, Allah Ya ba shi lafiya. Batun tsana kuma da kika yi, duk cikinmu babu wanda ya tsane ki. Ƙarƙari dai abin da muka yi, mun dai tsani halinki ne."
Shukura a cikin ranta ta ce, 'Ko ni ɗin kuka tsana kun yi ta banza, yanzu ma so nake na yi amfani da ku kafin buƙatata ta biya.' Amma a fili sai ta ce.
"Dama na zo ne na nemi yafiyar Hajiyan Mami, wallahi na yi nadamar duk abubuwna da na aikata a baya. Don Allah Yaya ku yafe mana, wallahi sharrin shaiɗan da ruɗin ƙawaye ne." Shiru Baba malam ya yi ya ce, "Allah Ya yafe mana gabaɗaya, amma wannan ba magana ce da za a yi ta a taƙaitaccan lokaci ba. Muna buƙatar isasshen lokaci tukunna, idan ya so sai a tattauna abin da ya dace." Kamar mutuniyar kirki haka Shukura ta sunkuyar da kai ƙasa ta ce.
"Na gode Yaya, Allah Ya ƙara girma." Ganin ya yi shiru ta sake cewa.
"Yaya don Allah ku taimaka ku leƙa a sibitin nan, Dadyn Mami yana jin jiki sosai." Karɓar adireshin asibitin ya yi, sannan ya ce ta wuce zai taho.
Bayan tafiyar Shukura Mama ta dubi Baba malam ta ce, "Alhaji wallahi ban yarda da makirar yarinyar nan ba. Haka kawai nake ji a jikina ba da zuciya ɗaya ta yi wannan zuwan ba." Miƙewa tsaye Baba malam ya yi ya ce.
"To ai kowa ya yi na gari kansa, idan ma da wata manufa ta zo Allah ya mayar mata da mugun nufinta kanta. Ki cewa su Mu'alim su shirya za mu je duba shi yanzu."
Mama ta amsa masa sannan Baba malam ya wuce ciki don ya shirya. Sai da ya kira 'yan uwansa ya sanar da su, sannan ya fito shi da su Haidar da 'ya'yansa suka wuce asibiti. Kusan lokaci ɗaya motar Shukura da ta su Baba malam ta shiga harabar asibitin, saboda Shukura ta biya ta store ta yi musu sayayyar abubuwan da za a buƙata. Ganin ta taho hannuwanta ɗauke da manyan ledoji, ya sa Baba malam ya ce su Haidar da Mu'allim su karɓa, babu yadda Haidar zai yi don dai ya san ba shi da damar musawa. Amma da babu yadda za a yi ya karɓi kayan hannun Shukura, suna shiga reception suka hango Inna tana zaune jigum. Shukura tana ganinta har za ta mata magana, cikin zafin nama Inna ta tsinke da mari. Ɗgowar da za ta yi ta sake tsinke ta da mari, da sauri Baba malam ya matsa ya ce.
"Subhanallah! Haba Hajiya ya da haka? Ba ki ga a yanayin da take ciki ba ne?" Inna ta fashe da kuka ta ce.
"Alhaji ka bar ni na kashe yarinyar nan na huta da ta kaicin da ta ƙunsa mini, ashe dama kishiyarta Hajiya ba ta gidan? Sai ɗazu da ta kira ni take sanar da ni abin da ya faru. Wallahi Shukura ke dai ba ki da mutumci, albasa ba ta yi halin ruwa ba." Inna ta ƙarasa maganar tana sake kai wa Shukura duka, da sauri Shukura ta yi bayan Baba malama tana kuka saboda marin da Inna ta yi mata ba ƙaramin shigarta ya yi ba. Baba malam ne ya kare ta cikin lallashi ya ce.
"Don Allah ki yi haƙuri hajiya, idan ka ce za ka biye ta halin yara sai ka nakasa su a banza."
Inna ta fyace majiya haÉ—e da rushewa da kuka sannan ta ce.
"Alhaji yarinyar nan so take ta ɓata mini suna? Me ta aikata haka? Wallahi kin ci sa'a da Alhaji Ya ƙwace ki, amma wallahi idan ba ki saka Alhaji ya mayar da matarsa ba babu ni babu ke. Mara mutumci ina zaman-zamana za ki ja wa zuri'ata zagi, ke dai ba ki ji daɗin halinki ba." Inna ta furta tana sake kai wa Shukura duka.
Da ƙyar Baba malam ya samu ya shawo kan Inna ta daina barazanar kai wa Shukura duka, haka a gaban kowa ta dinga jaddada idan Shukura ba tayi bakin ƙoƙari, ta saka Daddy ya mayar da Hajiya Karima ba za ta tsine mata. Wannan abin da ta yi ya sa mutane suka dinga yabonta, a ɓangare ɗaya suka dinga kallon Shukura a matsayin wacce take da uwa tagari amma ba ta yi koyi da ita ba.
Lokacin da suka shiga ɗakin Daddy yana kwance ya ƙurawa saman silin ido, har suka ƙarasa wurin bai sani ba. Baba malam ne ya dafa hannunsa ya ce.
"Sannu Umaru."
A hargitse Daddy ya É—ago ya ce, "Yaya kai ne? Don Allah tare kuke da Karima?" Shukura da ke gefe ta ji wani abu ya daki zuciyarta, don ko mai irin sunan Mommy ba ta son ta ji an ambata.
Baba malam ya ce, "Umaru ka nutsu don Allah, ba mu kaɗai ba ne a wurin nan. Ga yara ma sun zo duba ka." Sai a lokacin ya ɗago ya dubi su Haidar cike sa so. Su kansu ba ƙaramin kewar mahaifinsu suka yi ba, ganin ya rame sosai ya sa Haidar ya matsa kusa da shi jiki a sanyaye ya ce.
"Sannu Daddy ya jikin?"
Daddy da idonsa ya fara zubar da ƙwalla ya ce.
"Haidar! Haidar ina Mommynku ko ba ta zo duba ni ba?" GyaÉ—a masa kai Haidar ya yi ya ce.
"Ta ce a duba ka, Mami ma ta ce gobe za ta zo duba ka."
"Ai na warke Haidar, Yaya don Allah ka taimaka ka ce Karima ta dawo. Wallahi ban san lokacin da na sake ta ba, wallahi sharr..."
Inna ta katse maganar Daddy sakamakon jifan Shukura da ta yi da takalmi ta ce.
"Munafuka kin ji abin da mijinki yake faÉ—a ko? An ya Shukura zuciyar musulunci gare ki, wallahi tun wuri ki je ki nemi yafiyar mijinki, kuma ki bi duk yadda za ki yi ki sa ya dawo da matarsa idan ba haka ba wallahi kada ki sake takowa inda nake."
Daddy har cikin ransa ya ji daÉ—in abin da Inna ta yi, Baba malam ya ce.
"Don Allah ki yi haƙuri haka, ba na jin daɗin furucin da kike mata."
"Alhaji haushin yarinyar nan da nake ji, wallahi ji nake kamar na maƙure mata wuya ta mutu. Ace ki zo ki samu mace da mijinta sama da shekara ashirin, ki ƙulla makircin da za ki sa mijinta ya sake ta. Alhaji ta kyauta kenan?" Inna ta furta tana kumfar baki.
Baba malam ya jinjina kai ya ce, "Ba ta kyauta ba, kin san ɗa ne ka haife shi ba ka haifi halinsa ba. Yanzu dai ki je gida ki huta Hajiya." Inna ta ƙarasa bakin gadon ta duba Daddy sannan ta yi musu sallama ta fita.
Su Haidar ne suka fita waje, Shukura ta maƙure a bango ban da hawaye babu abin take yi. Daddy ya sauko daga gadon, ya russuna a gaban Baba malam ya ce.
"Don girman Allah yaya ka taimaka ka dawo mini da Karima, wallahi tallahi ban san yadda aka yi na rabu da ita ba. Na yi rashinta a kusa da ni Yaya, don Allah ka tausaya mini."
Daddy ya ƙarasa maganar yana hawaye, jikin Baba malam ne ya yi sanyi, zai yi magana Shukura ta matsa ita ma tana sake ƙwaƙulo hawayen munafurci ta ce.
"Don Allah yaya ka taimaka mini, hankalina a tashe yake da jin furucin mahaifiyata a kaina. Don Allah yaya ka taimaka ka ba wa Mommyn su Mami haƙuri." Baba malam ne ya ce ta tashi ta zauna a kujera, saboda yanayin da take ciki tun da cikinta ya tsufa.
Daga Daddy har Shukura zama suka yi dirshen suna ba shi haƙuri, sai da ya gama sauraronsu sannan ya ce.
"Duk na ji maganganunku, to amma ku sani. Ba ni zan zauna da kai ba Umaru, Karima ce mai zama da kai, ita ta san irin zaman da ta yi da ku. Don haka sai da amincewar Karima sannan za a mayar muku da aurenku, idam ta yarda shi kenan idan kuma ba ta amince ba dole ku yi haƙuri." Bakin Daddy har rawa yake ya ce.
"Zama ma ta amince In Shaa Allahu."
"Allah Ya sa."
Baba malam ya furta.
A ranar Daddy ya matsa sai an sallame shi, sai da suka gwada shi suka ga jininsa ya ɗan daidaita sannan suka rubuta masa magunguna suka sallame shi. A daren ranar Daddy ya sheƙa wanka ya nufi gidan Baba malam da nufin ya samu ya shawo kanta. Tun da Baba malam ya ji zuwan Daddy ya sa aka aika kiran Mommy, sai da ta shiga wurinsa sannan ya ce.
"Karima na san kin san duk abin da yake faruwa, a yanzu haka Umaru yana cikin gidan nan. Ya zo domin ya ba ki haƙuri a game da abin da ya faru, to ni yanzu a tsakiya nake. Ba zan goyi bayan Umaru ba don na tilasta miki ki komai gidansa, haka kuma idan kina son komawa ɗakinki ba zan hana ki ba. Umaru shi ne mijinki tun kuna saurayi da budurwa, ke kika san halinsa da irin zamantakewarku. Kada ki cuci kanki, idan kin ga za ki koma fani'ima, idan ba za ki koma ba shi kenan babu mai yi miki dole." Mommy ta jinjina kai sannan ta ce.