← Book details Dahuwar Kaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 81

Sashe 81

Dahuwar Kaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Fadil ne ya ɗauke su a motarsa ya wuce da su asibitin ƙwararru na Malam Aminu Kano (AKTH). Kasancewar a can yake aiki, kai tsaye ɗakin haihuwa aka wuce da ita domin a duba ta. A gwaje-gwajen likitocin ne suka tabbatar da ba ciki ba ne, sai dai ba sa ganin komai a cikin nata. Hankali a tashe Hansatu ta kira Yaya Inu, a lokacin ya ci babbar rigarsa zai tafi ɗaurin aurensa.

"Mai gida akwai damuwa ciki dai na jikin Salame ashe ba É—a ba ne."

"Mene ne idan ba ɗa ba? Hansatu kada ku janyo mini masifa a farar safiyar nan. Ni fa ba na son damuwa, yanzu haka ɗaurin aurena da Zuly zan tafi." Baƙin ciki ya sa ƙwalla ta zubo wa Hansatu a ƙufule ta ce, "Yanzu abin da za ka ce mini kenan? Mai gida kana nufin Zuly ta fi 'yarka Salame?"

"Hansatu kada ki ɓata mini rai, kin san dai jiya a yadda na kwana. Auran nan da za a ɗaura ne kawai yake ba ni ƙwarin gwiwa, har kika ga ina walwala. Ke bari na wuce kada ki ɓa ta mini lokaci, saboda matashin kai ta ce mini waliyinta wutar ciki gare shi zai iya tafiya idan na makara." Daga haka Yaya Inu ya katse, ya tura waya a aljihu ya rufe ɗakinsa sannan ya fice.
Yana kai kansa zai fita a ƙofar gida ya ci karo da Mai gari shi da su Sanƙira, cike da girmamawa mai gari ya russuna ya ce.
"Barka da fitowa!"
Hannuwa biyu Yaya Inu ya kai ya fara shafa idonsa, a ransa yana ayyana ko dai gizo idonsa ya yi yake nuna masa Mai gari ne yake tsugunna masa.

"Ranka ya daÉ—e ya haka kuma?"
Mai gari ya russuna ya ce, "Duk girmanka ne ai, ga wannan a rage da abincin yara."

Sanƙira shi da Muzammil, suka shiga kiciniyar sauke buhunhunan kayan abincin daga cikin kura sannan suka tafi. Mai gari har zai juya da sauri Yaya Inu ya tsayar da shi.

"Ranka shi daÉ—e ni fa ka saka ni a duhu, waÉ—annan É—in na mene ne?"
Mai gari ya shafa kai ya ce, "A da dai ban yi niyyar sanar da kai yanzu ba, amma na ga kana neman ƙarin bayani ne Baba. Magana ta gaskiya Allah Ya jarabce ni da son Laraba, kuma aurenta nake son yi." Yaya Inu ya bayyana mamakinsa a fili, saboda duk cikin yaransa babu mai baƙin jini da samari ba sa kulawa kamar Laraba. Amma ganin irin rawar ƙafar da Mai gari yake yi masa, da tarin arzikin da zai samu ya sa ya ce.
"Idan ma yanzu a shirye kake, ka wuce mu je masallaci domin yanzu haka ni ma ɗaura mini aure za a yi!" Cike da shauƙi Mai gari ya ce, "A yi haka kuwa?"

Yaya Inu ya washe baki ya ce, "Me ya rage Mai gari? Ni ma ai an sauƙaƙa mini wannan bidi'ar wunin bikin, da mata za su zo su yi ta cinye abinci." Godiya sosai Mai gari ya yi, ya ce zai je ya sauya kayansa sannan ya ƙarasa. Hakan kuwa aka yi, Mai gari yana zuwa masallaci ana gama ɗaurin auren Yaya Inu da Zuly matashin kai. Yana zama ya miƙa wa Malam Liman sadaki ya zama waliyinsa, aka ɗaura aurensa da Laraba a kan sadaki naira dubu ɗari.

Fitar Yaya Inu daga gida babu jimawa Goggo ta ƙarasa, almajirai ne suka shiga da ƙullin kayanta. Inno tana hango ta, ta ƙarasa wurinta cikin farinciki ta rungume ta tana faɗin.
"Lale marhabun yau ga mutanen Jibiya." Goggo ta saki murmushi ta ce, "Ga mu Allah Ya kawo mu, wai ina Laraba ban ji motsinta ba?"

"Idan kika bibiya ta fita ta ɗauko mini magana, yarinya yadda kika san rainon ifiritu." Goggo ta saka dariya cike da zolaya ta ce, "Ni kam wai Inno hala yaron ciki gare ki? Irin wannan ƙyalli da kike yi haka."
Inno ta saki guntun tsaki ta furta, "Wuce mu je ku gaisa da Malam, kafin mu shiga ki fara zuba mini labari."

Tun shigar Goggo gidan da Mai Yasin ya ji muryarta, ƙirjinsa ne ya yi wata irin bugawa da ƙarfi. Haka kawai ya ji gabansa yana faɗuwa, jin muryar matar da ko a duniyar mafarki ba zai manta da ita ba.

Da sallama É—auke a bakin Inno suka shiga É—akin, Mai Yasin yana É—aga ido karaf ya sauka a kan Goggo da ta daskare a wurin.

"Malam Jafaru! Dama tsawon shekaru a nan ka laƙe bayan ka halake mini dukiyar marayu? Allah na gode maka, tabbas addu'a ba ta faɗuwa ƙasa banza. Azzalumi maha'inci, ka ci amanata kuma ka tafi ka bar ni da ƙallagaggen aurenka a kaina."

Mai gari ya jima bai yi farincikin da yake ciki a wannan ranar ba, saboda mallakar Laraba da ya yi ji yake kamar ya mallaka faraincikin duniyarsa gabaÉ—aya. Yaya Inu ne ya sanar da shi tariyar Laraba, za ta kama sati mai zuwa saboda 'yan saye-sayen kayan É—aki da za a yi mata.
Bayan sallar Isha'i Zuly matashin kai da wasu fanɗararrun ƙawayenta biyar, suka yi mata rakiya zuwa ɗakin miji. Dama da rana ma tare da ita aka yi jere, don haka da za a kai ta suna tafe suna hira. Zaune take a ɗakin ta, tana jiran shigowar Yaya Inu hayaniyar yaran ta cika mata kunne. Cike da izza ta fita tsakar gidan a gadarance ta ce.

"Ku waɗanne irin dabbobi ne, ku da yaranku da za ki dinga tunɓele da dare?"
Indo da dama zuciyarta take cike da kishi fal ta ce, "Yadda muka zama dabbobi, sannu a hankali ke ma za ki zama dabbar, har ki haifo balami a ciki gaba da yin tamɓelen da shi." A daidai lokacin Yay inu ya shigo, yana shigowa duka yaran suka nustu suna yi masa sannu da zuwa, ko ƙurarsu bai kalla ba ya wuce wurin Zuly ya kamo hannu ta suka wuce ɗakinsa. Sabuwar hira suka dasa suna ƙyalƙayala dariya, zuciyar Indo kamar za ta buga, tun tana tsakar gida tana jin hirarrakinsu har dare ya yi ta shige ɗaki ta kwanta.
Ganin Yaya Inu ya ja filo da abin rufa ya sa Zuly matashin kai ta ce, "Yaya haka ne masoyi? Ban gane ba an yi gabas da kare." Ƙirjin Yaya Inu ya buga amma sai ya basar ya ce, "Na gaji ne kin san fa yau na sha baƙi." Zuly ta ɗan tsuke fuska ta ce, "A'a ai kuwa haka za ka yi haƙuri ka tashi, don ni in saluɓe namiji ba abu ne mai wuya a wurina ba." Tsoro da kunyar Zuly ya mamaye shi, saboda tun da yake aure bai taɓa auro fitsararsiyar mace irinta ba. A ɓangare ɗaya kuma bai san me zai ce mata ba, hasali ma wata irin kunyarta yake ji. Yana cikin nazari, ya ga Zuly ta miƙe tsaye tana warware ɗankwalin kanta ta ce. "Na ka wasa ne Malam Inusa, ai ni ba na sanya. Ba ka ji ma laƙabin sunana ba matashim kai? Bari ma ka gani."
Zuly ta ƙarasa maganar tana fisgo siraran ƙafafuwan Yaya Inu.

Ya auren Yaya Inu da matashin kai zai kasance? Shin Yaya Inu yana warkewa ko ya tafi kenan? Wacce badaƙalar za a yi a gidan Mai gari da Laraba? Shin za ta so Maigari ko shi yake wahalarsa? Ina matsayin auren Inno da Mai Yasin? Yaya Mai Yasin zai yi tun da asirinsa ya tonu? Zai zauna da Goggo da Inno ko yaya? Mene ne a cikin Salame idan ba ɗa ba? Ya matsayin gwajin da za a yi wa su Ɗan Bishir? Yar gwal da Ɗanladi zaman su zai ɗore?
Duka waÉ—annan tambayoyin da ma waÉ—ansu, amsarsu tana cikin cigaban littafin GIDAN LIKITOCI.

AlhamduLillah, a nan na kawo ƙarshen free pages ga me son ci gaba za ta biya ta 500 Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank shaidar biya ta wannan no 07062062624

Ummou Aslam Bint Adam🌚
Chapter 81 · 0% Book details