← Book details Dahuwar Kaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 81

Sashe 36

Dahuwar Kaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana nan tsaye ta ƙarasa ciki, kunna fitilar wayarta ta yi saboda duhu ta shiga haske cikin gidan.
Ciki da falo ne guda ɗaya, sai fallan ɗaki da banɗaki a ciki. A gefe banɗaki ne da kitchen sai ɗan ƙaramin tsakar gida. Kusan an gama komai, sai daɓe, fulasta, fenti, ƙofafi da winduna su suka yi saura. Farinciki ya sa Sury ta rungume shi tsam, tana faɗin.
"Gaskiya gida ya yi masoyina, amma kana ganin wannan ƙarashen zai iya kai wata nawa baba gama ba?"
Tun da ta rungume shi ya ji duk yanayin jikinsa ya canza, jikinsa a mace ya shiga yawo da hannunsa a jiki sa. Da wata irin murya ya ce, "Kin san samun namu lokaci-lokaci ne, amma dai ina fatan har aurenmy ba zai haure shekara ba."
Ganin saƙon da take aika masa ya fara tasiri a jikinsa ya sa Sury ta cigaba shi ma yana mayar mata da martani. Dogon hijabin jikinta ya zame mata, dama Surayya kafin ta fito sai da ta faki idon mahaifiyarta ta zuro dogon wando da ƙaramar riga a ciki sannan ta zura zumbulelen hijabinta har ƙasa.

Duk zuwan da Kabir yake yi wurin Sury wani abu bai taɓa shiga tsakaninsu ba, bayan rungume-rungume da shafe-shafen da suke yi wa juna. Don haka da ya ji Sury za ta zo ganin gidansa ya ci alwashin saninta a wannan ranar, yana tsaka da yawo da hannunta ya ci karo da abin da bai yi tsammani ba.
"Mene ne wannan?"

Kabir ya faɗa ransa a ɗan ɓace.

"Gabannin magriba period É—ina ya zo!"
Ta furta masa, don dama ta ƙi faɗa masa ne saboda kada ya fasa kawo ta. Domin ta san matuƙar suka zo gidan ta san sai ya nemi koda taɓa wannan ɓangaren ne. Cikin wata irin murya ya raɗa mata a kunne, "Yanzu ya za ki yi da ni?"
Murmushi ta sakar masa ta ce, "Dabarun mu na mata mana, ko ba ka san idan macen aure tana wannan halin akwai dabarin da take yi ba." Ya sani sarai, domin Fauziya duk a halin da take ciki tana ƙoƙarin faranta masa. Amma shi sam ba haka ya so ba, ita ma Sury ta fahimci haka amma ta basar. Babu kunya Surayya ta shiga sarrafa shi, tamkar yadda macen aure take yi wa mijinta. Suna cikin wannan yanayin kiran Fauziya ya shigo cikin wayarsa, kamar ba zai ɗauka ba tuna matsalar da aka samu a daren jiya da ta je shagonsu aka ce ya fita da wuri ya sa ya ɗauka don ya ji abin da ya faru.

"Hello!"

Daga can ɓangaren Fauziya ta ce, "Abi barka da yamma!"
Ya É—an yi gyaran murya don ka da ta fahimci sauyinsa ya ce, "Barka dai Ummu Banat, ya jikin?"
Ta amsa masa tana wurga masa tambaya.
"Amma ba ka shago ko? Na ji ban ji ƙarar ɗinki ba?"
Duk da ya san zai yi wuya Fauziya ta gane a inda yake, amma sai da ya ji gabansa ya faÉ—i.
Ya janye jikinsa daga jikin Surayya yana faɗin, "Na'am eh na je karɓo wa oga kayan ɗinki ne, ina zuwa an zo kaina."
Daga haka ya katse, tun da ya fara waya Surayya take wurga masa harara tana shirin yin magana ya ce.
"Ayi mini afuwa."
Juyar da kai gefe ta yi cikin fushi, ya shiga lallashinta sannan Surayya ta cigaba da sarrafa shi. Sai da suka É—auki lokaci a haka sannan Kabir ya samu nutsuwa, da yake gidan akwai rijiya sai kawai ya ja ruwa da gugura ya yi wanka da ita sannan suka fito daga gida.

A yi haƙuri da error ban yi editing ba🫠

Ummou Aslam Bint Adam🌚
+2347062062624
[09/02, 20:22] Ameera Adam: *NAUSHIN WUTA*

©®AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

GARGAÆŠI: Ban amince a sarrafa mini littafi da kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.

SADAUKARWA
Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da mata da gidan Aljanna Amin.

SHAFI NA HUÆŠU

Fauziya tana gama waya da Kabir ta tashi da sauri ta faɗa banɗaki ta sheƙa wanka, bayan ta fito ta ciro wata doguwar riga ta saka. Jikin rigar roba ce, ba ta da tsayi har ƙasa. Daga iya gwiwarta ta tsaya, ta ɗauko kum ta fara gyara gashinta. Fauziya irin dogayen matan nan ne, sai dai tana da ɗan kauri. Tana da ƙira sosai sai dai ba fara bace tas, tana dai da haske da kuma yalwar gashi. Faka gashinta ta yi jelar ta sauka har gadon bayanta, ta ɗebi turarruka masu ɗaɗin ƙamshi ta feshe jikinta da su. A gaban mudubi ta tsaya tana ƙarewa kanta kallo, su Na'ima sai zagaye ta suke yi suna cewa ta yi kyau. Ita kanta ta san ta yi kyau, don haka take ta ɗokin Kabir ya dawo ya ga kwalliyarta. Dafa tsohon cikin jikinta ta yi ta saki murmushi, domin ta san Kabir mutum ne mai san ƙananan kaya. Jin kiran sallar Isha'i ya sa ta saka zumbulelen hijabinta har ƙasa, ta tasa su Na'ima suka gudanar da sallar Isha'i. Bayan sun idar sai da ta yi wa yaran tilawar Alƙur'ani, sannan ta zuba musu abinci suka ci. Da suka gama suka ɗan yi wasa sannan ta yi musu shimfiɗa a tsakar ɗaki, don ta ci alwashin duk zafi ta daina fitar da su waje.

Kabir da Sury tare suka tafi har unguwar su Surayya. Ita ta sauka ta wuce gida, shi kuma ya wuce shagonsu. A lokacin da ya koma Ogansu ba ya nan, don haka shi ma bai zauna ba ya fice daga shagon. A madadin ya wuce gida yana fitowa sai kiran abokinsa Abbati ya shigo masa.
"Ya Abbati kana iya?"
Kabir ya furta bayan ya ɗauki wayar, daga can ɓangaren cikin muryar maye Abbati ya ce, "Ga mu a majalisa, kai fa muke jira kwana biyu nan ba ma gane maka sai wani eh yane kake yi wa mutane."

"Don Allah mijina ka daina wannan shaye-shayen, a yanzu matsayinka na uba ne. Idan za ka yi sara, ka dinga lura da bakin gatari kana wasa shi. A yanzu da muke rayuwa, kamata ya yi ka duƙufa a neman ciyar da mu halali ba shaye-shaye ba. Allah Ya yi mana arzikin 'ya'ya mata, ina gudun kada watarana idan suka girma a dinga goranta musu. Ka yi mini alƙawarin ba za ka sake shan komai ba Kbna."

Kabir ya tuna kalaman da Fauziya ta yi masa, bayan ya dawo hayyacinsa a ranar da ya faɗa ɗakin A'ilo yana cikin maye. Murya a can ƙasa ya ce. "Ku sha kawai Abbati, Fauziya ba ta san shaye-shayen da nake yi."

"Ɗan abin rage zafin shi ne za ka ce Fauziya ba ta so? Kai yanzu kana namiji mace ce za ta zauna tana yi maka ƙabali da ba'adi? Haba bros kada ka bayar da maza mana, don Allah ka taho muna jiranka."
Daga haka Abbati ya kashe, har zuciya ta ce masa ya yi tafiyarsa gida, sai kuma wata ta ce ya je ya sha ko kaɗan ce. Saboda shi kansa kwana biyun da ya yi bai sha ba, har jin sa yake yi wani iri. Don haka daga nan bakin ƙofar shagon ɗinkinsu ya wuce bayan wata makarantar firamare, wacce iren-irensa suka laɓewa a lungunta suke shaye-shaye. Kabir yana zama T-boy ya miƙa masa wata 'yar roba haɗe da da wata baƙar leda, nan take Kabir ya fara shaƙa yana ɗaɗɗakar ruwan robar kafin wani lokaci tuni ya yi wa kansa caji.

Jin shiru har ƙarfe goma da rabi Kabir bai shigo ya sa Fauziya ta ɗauki wayarta ta latsa lambarsa. Sai dai wayar ta ƙari ringing har ta katse bai ɗauka ba, haka kawai ta ji gabanta ya faɗi. Zuciya ta shiga raya mata ko dai Kabir yana wurin shaye-shayen da ta hana shi, girgiza kanta ta yi cike da ƙwarin gwiwa ta ce.
"In Shaa Allah a wannan karon ba zai sake ba..."

Maganarta ce ta katse sakamakon jin mummunan bugun ƙofar da ake yi, wanda ya gigitata saboda tsoro, firgici da tashin hankali.

"Fauziyataaaaaa! Fauzeeeee, zooo ga ni na zo."

Kalaman Kabir cikin maye suka doka sallama cikin dodon kunnenta, ba yau ta saba jin haka daga gare shi ba. Amma a wannan ranar sai ta ji wani irin ɗaci, ɓacin rai da baƙinciki ya mamaye ta. Ta kalli su Na'ima da ke kwance a ƙasa, haka kawai ta ji tausayinsu a ya kamata. Hawaye ne bibbiyu suka fara zuba daga kwarmin idonta, tana nan zaune ta sake jin ya buga ƙofar da ƙarfi yana cewa.

"Don Allah... kar ki min faÉ—a... ni babu abin da na shaaaa..."

Sanin halin mutanen gidansu ya sa ta yunƙura da ƙyar ta fita, inuwa ta gani a bakin ƙofar Maman Sabir da alama a tsaye take tana leƙen ganin abin da zai faru.

"Ni fa... ba na shan... komai, Fauziyaaaaaa ko kin sha kin bugu ne... kika yi bacci... ki zo ki buÉ—eeee."

Ta sake jin muryarsa a daidai lokacin da ta tura ƙofar gidan, tana buɗewa ya faɗo jikinta da yake ya saki jikinsa a kan ƙofar. Hannu ta saka ta kare cikinta, tana shaƙar ƙamshinsa ta ji yana wani irin warin hayaƙi.

"Fauzinaaaa."

Ya furta yana shafa fuskarta, takaici ne ya gama maƙure ta. Ta haɗiyi yawu mai ɗaci ta dube shi tana jin kamar ta rufe shi da duka, a wannan ranar ji ta yi da ace su kaɗai ne a gidan tana buɗe masa za ta bar shi a wurin. Idan ya ga dama ya shiga ko ya kwana a nan, amma gudun kada ya shiga ɗakin matan aure ya sa ta kamo shi. Suna tafe yana layi tana dafa bango, tana shiga tsakar gida ta hangi A'ilo da Maman Sabir suna magana ƙasa-ƙasa. Duk da ba ta ji me suka faɗa ba, amma jikinta ya ba ta maganarta da Kabir suke yi. Ta girgiza kanta cike da tausayin irin rayuwar da take ciki, sannan suka shiga ɗaki. Suna ganin Fauziya ta shiga ɗaki suka saki shewa haɗe da tafi A'ilo ta ce.
Chapter 36 · 0% Book details