← Book details Dahuwar Kaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 81

Sashe 66

Dahuwar Kaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ɗan Bishiririna! Ɗan Bishiri ka yi haƙuri ban kyauta maka ba ko? Yanzu me kake so na sayo maka?"
Ɗan Bishir ya kalli gabas da yamma, ya kalli mahaifiyarsa da ke gefe a zaune kalli mahaifinsa. Sai ya sake ɓarke baki ya saki kuka.
Ƙirjin Baba Sale ya buga da ƙarfi ya jikinsa yana rawa, ya rungume Ɗan Bishir ya dubi Uwale fuska shaɓe-shaɓe ya ce.

"Uwale tsoro nake ji, wallahi ina cikin tashin hankali."
Uwale ta sauke ajiyar zuciya, saboda ta san za a yi haka ko ma fiye da haka.
"Me ya faru mai gida?"
Baba Sale ya ja gefen É—an kwalinta ya share hawaye ya ce. "Ina tsoron ko dai an guntule ÆŠan Bishir gabaÉ—aya, Uwale kada fa Bala wanzan ya nakashe mini É—an É—aya-É—ayana..."
Kuka ya ci ƙarfinsa.

"Yanzu mai gida duk yaran da ka dinga yi wa shayi, iyayensu ba su ce za ka nakasa musu 'ya'ya ba sai da abin ya zo kanka? Kamar ba ka san yadda Bala yake da ƙware a harkar wanzanci ba? Kar ka manta shi fa ɗan gado ne."
A hassale Baba Sale ya ce.

"Kowa ai nasa ya sani, ni gudan jinina kuma magajina na sani don haka a kansa zan yi magana..."
Ita ma Uwale ta katse shi.

"To ai ɗa na kowa ne, shi ya sa ɗa da dukiya ba a yi musu mugunta. Kuma hausawa suka ka ƙi naka duniya ta so shi, ka kuma so naka duniya ta ƙi shi. Wallahi wannan zazzafar soyayyar da kake yi wa Ɗan Bishir ba za ta kai ka ba. Don ba zan ɓoye maka ba a cikin gidan kowa haushinsa yake ji, ko kaɗan ba shi da farin jini a wurin yara da manya."
Wani irin kallo ya shiga wurga mata, yana jin a ransa yadda ta caɓa wa Ɗan Bishir baƙaƙen maganganu da ace ba a yi masa kaciya ba, babu abin da zai hana bai kora ta gidansu ba. To don dai ya san idan ta tafi babu mai jinyarsa.

"Baaabaaaa!"
Ɗan Bishir ya furta a shagwaɓe, da sauri Baba Sale ya amsa masa sai ya ce.

"Zan ci abincin Rahina, daÉ—i gare shi. Ni ba zan ci komai ba sai abinci ko shayinta."
Zumbur Baba Sale ya miƙe ya ce, "Ai kuwa yanzu zan karɓo maka, zauna Ɗan Bishiririna ga ni nan zuwa." Ya ƙarasa maganar yana zuwa bakin ƙofa, ya waigo yana jifan Uwale da harara ya ce.

"Shi Ɗan Bishir dai ya zama kabewar kan kabari baƙincikin mai taushe, duk wani mahassadi sai dai ya gan shi ya ƙyale."
Daga haka ya fice daga É—akin.

Kai tsaye sashen Labaran ya wuce, daga bakin ƙofa ya tsaya yana sallama. A lokacin Rahina ta tsakar gida a zaune tana shan iska, Labaran yana wanka a ta bayan kitchen ɗinsu don ya ce kafin ya samu kuɗin da zai rufa musu banɗakin sashensu, a nan za su dinga wanka saboda abin da ya faru da Rahina.

"Wa alaikassalam."
Rahina ta amsa sallamar tana yunƙurin miƙewa domin ta saka hijabinta, daga can gefe ta ji Labaran ya ce.

"Kada ki sake ki ƙara magana."
Shiru ta yi saboda ta san zafin kishinsa, shi kuma Baba Sale jin an amsa ya saki murya ya ce.

"Amarya mai daÉ—in tuwo da miya, angon na ki yana ciki?"

Wannan yabon da Labaran ya ji ana yi wa Rahina ya sake ɓata ransa, don haka ya zura gajeren wandonsa ko kunfar jinsa bai wanke ba ya fita fururu ƙofar gida.

"Lafiya Labaran me yake faruwa?" Baba Sale ya furta fuska É—auke da mamaki.
Labaran ya yarfe kumfar fuskarsa ya ce, "Ita ta kawo haka! Ka san dai abin da ka aikata haramci ne ko? Ka zo ƙofar gida ka zage muryarka kana magana iyalina tana sauraronka, ba ka tsammanin ta ji muryarka ta yi mata daɗi?" Ran Baba Sale ne ya ɓaci, amma da ya tuna Ɗan Bishir ya zo nemarwa abinci sai ya wayance.

"Labaran kenan, yanzu dai duk ba wannan ba. Wallahi Ɗan Bishir ne yake son cin abincin Rahina, saboda zaƙin girkinta kasan na daban ne."
Tun Baba Sale bai gama magana ba Labaran ya hau huci, rai a ɓace ya ce.
"Allah Ya isa, wallahi ba zan yafe maka ba, da wannan yabon. Yanzu saboda Allah abincin Rahina ne wani zindiƙin sankacecen ƙato yake yabawa haka?"
Zuciya ta fara ciwo Baba Sale ya ce, "Kai Labaran kada ka faÉ—a mini maganar banza da wofi, ban da aska da tasha jinin ÆŠan Bishir ka isa na tako wurinka neman abinci ne? Ka faÉ—a mini ko nawa ne zan biya ka, ka sayar mini abincin nata."

Labaran ya buga tsalle kamar mai shirin tashi sama, saboda yadda kishi ya tirniƙe shi ya ce.
"Ba askar kaciya ba Allah Ya sa abba-tuwa ce a kansa, wallahi ba zai ci abincin Rahina ba. Yanzu ni kake kallo ka ce na sayar maka da abincin Rahina? Ko kasan sayar maka da abincin nan daidai yake da na sayar maka da wani tsagi na daga baiwar da Allah ya ba ta?"
Haush ya sake mamaye Baba Sale sai kawai ya zuciya zai faɗa gidan, da sauri Labaran ya suri wani ƙaton itace. Ganin haka ya sa Baba Sale ya fice, shi kuma ya rufa masa baya yana faɗin.

"Jama'a ku tare ga baƙin kwarto mai lasisi nan."
Baba Sale yana faɗawa cikin gida ya danno ƙofar ya saka sakata, Labaran ya yi bugun duniya bai buɗe masa ba.

Ganin yadda Mahmud ya yi zuru yana nazari ya sa Mudassir ya taɓo shi ya ce.
"Wai me yake faruwa ne?"
Mahmud ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Wallahi Mudassir na haɗu da wani iftila'i a cikin wannan ƙauyen, ina cikin damuwa kuwa matuƙar Mai gari ya gano ni."
Mudassir ya bi shi da kallon mamaki don a iya saninsa da Mahmud, wannan ne zuwansa garin na farko, saboda har yana kan hanya shi ya dinga yi masa kwatance. A tsorace Mahmud ya kwashe duk abin da ya faru tsakaninsa da Laraba ya ba shi labari, tun bai rufe baki ba Mudassir ya dinga sheƙa masa dariyar ƙeta. Haushi ne ya kama shi, ya dube shi rai a ɓace ya ce.

"Ka ma mayar da ni É—an iska wato ga mahaukaci ko?"
Cikin dariya Mudassir ya girgiza masa kai ya ce, "Wallahi a garin wannan tsoron naka watarana sai ka halaka kanka. Yanzu kai Mahmud aljanu ne za su kai ka su baro? An ma kuwa aljanar gaske ce? Ace aljanu su nemi ya yanka musu zabi su tafi da su? Gaskiya akwai ayar tambaya."
Jiki a sanyaye Mahmud ya ce.

"Wallahi a wannan dajin ba na jin za a samu bil'adama a cikinsa, kai ganin idona na fahimci ba mutum ba ce. Yanzu tun da ka ce dole mu gabatar da kanmu wurin mai gari sai dai ka wakilce mu."

"Kai ka san yadda mutanen ƙauye suka ɗauki mai gari kuwa? Ai dole sai mun haɗu mun gabatar da kanmu ya san da zamanmu a garinsa, wallahi yadda ka ci ubansa shi ma haka zai ci na ka idan ya gano ka."
Mudassir ya furta yana gimtse dariyarsa.
Wata dabara ce ta faÉ—o wa Mahmud ya saki murmushi a fili ya ce. "Mu je gidan da ka ce za mu sauka, na san yadda zan yi da su."
Mudassir ya shiga kwatanta masa hanyar, suka sauya akalar hanyar zuwa wani É—an madaidaicin gida mai É—aki biyu wanda babu kowa a cikinsa.
Mudassir ne ya ɗauko mukulli ya buɗe musu ƙofar suka shiga da kayansu, a kan wani ɗan ƙanƙanin gas da Mahmud ya taho musu da shi suka ɗora ruwan wanka. Sai da suka yi wanka suka sha ruwan tea da Mudassir ya dafa musu, sannan ya ce su shirya zuwa wurin mai gari.
Mahmud shadda ya saka fara ƙal, ya ɗauko hula ya saka. Sai kuma ya saka face mask a fuskarsa idonsa yana sanye da glass. Mudassir kuwa ya saka ƙananan kaya sun yi kyau sosai, duk hanyar da suka bi sai abi su da kallo ana ganin 'yan birni sun shigo garin. Lokacin da suka ƙarasa ƙofar gidan mai gari shiru suka ji shi kamar babu mutane, a ƙofar gidan suka tsaya duk da Mahmud ya rufe fuskarsa amma gabansa faɗuwa yake kada Mai gari ya gano shi.

"Salamu alaikum!"
Mudassir ya yi sallama yana zura kai soron mai gari. Shiru suka ji ba a amsa ba, da yake É—akin Mai gari a soro yake yana jin duk abin da suke faÉ—a.

"Na yi mamaki da na ji ba a amsa sallamar ba, É—azu fa da na zo a kan idona ya shiga gida."
Mahmud ya furta a hankali, shi kuma Mai gari jin haka ya sa cikinsa ya sake kaɗawa, don ya yi tunanin hukumar kare haƙƙin aljanun ce ta sake turo wakilanta. Yana daga cikin ɗakinsa gumi ya shiga keto masa, wani ɗan matsakaicin matashi da ya zo wucewa ganin su Mahmud a tsaye ya ce.

"Wai Mai gari kuke nema?"
Mudassir ya gyaÉ—a masa kai, don yaron ya yi musu magana da biyu ne saboda ya birge abokansa da ke can labe suna kallonsu. Ko babu komai dai ya san ya yi wa 'yan birni magana.
"Idan kuka yi magana bai amsa ba, yana nan cikin ɗakinsa ku ƙwanƙwasa masa."
Yaron ya furta yana niyyar wucewa, Mudassir ya ce masa.
Chapter 66 · 0% Book details