Sashe 2
Dahuwar Kaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
WASHEGARI
Tun da gari ya waye Bilkisu ta lura da sauyin Hafiz, sai wani nannan yake yana haba-haba da ita. Sai da yaran suka tafi makaranta gabaÉ—aya sannan ya cewa Bilkisu.
"Ummu Sayyid, don Allah magana nake so mu yi da ke ta fahimta. Kuma ki kwantar da hankalinki wannan ba wani abu ba ne, ni dai kin san ina sonki kuma ina matuƙar ƙaunarki Bilkisu." Gabanta ne ya faɗi, da sauri ta haɗe fuska ta ce.
"Ka ga ni ba na son wannan kewaye-kewayen, duk me ya kawo waÉ—annan maganganun?" Murmushi ya yi ya ce.
"Haka ne, to kin san komai da kika sani a rayuwa muƙaddari ne daga Ubangiji. Kuma kin san akwai abin da yake ƙaddara a cikin rayuwar mutum, ko ba ya so babu yadda zai yi da shi."
Hafiz ya É—an yi jim sai ya cigaba da cewa.
"Dama tun kwanaki nake son sanar da ke, akwai wata yarinya da na yaba da hankalinta. Ko kaÉ—an ba ta da hayaniya, shi ya sa nake son aurenta. Don ba zan kawo wacce za ta tarwatsa mini gida ba..."
"Dakata don Allah Hafiz, wannan wacce irin maganar banza kake faɗa mini? Yanzu dama akwai ranar da za ka munafurce ni? Ni za ka ƙara wa kishiya Hafiz?"
Bilkisu ta furta cikin fusata. Hafiz ya sake kwantar da murya ya ce.
"Wallahi na so sanar da ke tun rannan, sai kuma na ga za ku shiga bikin Yaya Salis don haka na bari sai an gama. To jiya bayan kin fita su Baba Ƙarami suka je kai kuɗin aurena wurin iyayen Amina."
A wannan karon ma É—agowa Hafiz ya yi yana satar kallonta sannan ya ce.
"Wallahi ana zuwa, mahaifinta ya ce a ɗaura aure idan har da gaske nake yi. Idan ya so ko daga ba ya a yi duk bidi'o'in da ake yi na al'ada, wai saboda wasu samarin suna amfani da kai kuɗin aure don su ɓata ya..."
"Kutumar..."
Uban ashar É—in da Bilkisu ta lailayo ta maka ya katse maganar Hafiza, nan take jikinta ya É—auki karkarwa cikin tsananin zafin kishi ta cikumo wuyansa ta ce.
"Wallahi duk shegiyar da ka aura sai ka sake ta, ni za ka wulaƙanta ka tozarta? Wallahi ko ka sake ta ko na kashe ka, kuma na kashe kaina yanzun nan." Bilkisu ta ƙarasa maganar tana fisgo sharɓeɓiyar wuƙa a kwandon wanke-wanke.
GIDAN ALHAJI UMAR
Hajiya Karima wayarta ta ɗauko ta latsa layin lambar mai gidanta, ba a ɗauki lokaci ba ta ji ya ɗauka. Don haka cike da ƙosawa ta ce, "Alhaji ko na wuce ɗaki ne? Tsawon minti goma sha biyar fa kenan da ka ce na fito kuma na ji ku shiru."
"A'a ga mu nan zuwa." Daga can ɓangaren Alhaji Umar ya ba ta amsa. Tana nan zaune babu jimawa ta ji ya shigo falon baki ɗauke da sallama. Ɗago da kai ta yi ta amsa masa, ta hangi hannunsa a maƙale da na Shukura da take biye da shi. Zama ya yi a kujerar da ke kallonta, Shukura ta matsa jikinsa tana lafe kanta a gefen kafaɗarsa. A ɗan duburburce Alhaji Umar ya ce.
"Wallahi... kin san akwai gajiyar biki. Duk ta gaji ne."
Murmushi Hajiya Karima ta yi, duk da tana jin zafi a ranta amma sai ta danne ta ce, "Ai dama gajiya sai a hankali za ta warware."
A hankali Shukra ta gyara mayafinta cikin dabara ta fara ƙarewa Hajiya Karima kallo.
Hajiya Karima babbar mace ce da za ta kai shekara talatin da bakwai zuwa arba'in, ita da Alhaji Umar aure suka yi tun na saurayi da budurwa. Alhaji Umar zai yi shekara arba'in da bakwai zuwa hamsin, tun da suke tare da Hajiya Karima bai taɓa ƙara aure ba, sai a wannan lokacin da ya auro Shukura mai shekara goma sha takwas a duniya.
Ta cikin mayafi Shukura ta yamutsa fuska a cikin ranta ta ce.
'Gaskiya baby ya yi haƙurin zama da wannan abar, don Allah dubi yadda duk naman fuskarta ya saki. Aba ta yi shirim da uwar ƙiɓa babu fasali.'
Gyran muryar da Alhaji Umar ya yi ne ya katse gajeren tunanin da Shukura ta faÉ—a.
"AlhamduLillah! Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Ubangiji (S.W.A), Hajiya ke da Shukura na haɗa ku a nan ne domin na yi muku 'yar nasiha. Gabaɗayanku matana ne, ke Hajiya ke ce babba. Idan kika kama girmanki za ku zauna lafiya babu rashin kunya ko tashin hankali, haka kema Shukura. Wannan uwargidana ce, ba ta da matsala da kowa tun zamana da ita. Ban auro ki don ki raina ta ba, haka ita ma daga ɓangarenta."
Alhaji Umar ya furta cikin tausasan lafuza. Ya jima yana yi musu nasiha sannan kowa ya wuce É—akinsa.
Tun da Hajiya Karima ta shiga ɗaki ta ji zuciyarta duk babu daɗi, duk yadda ta kai ga danne kishinta sai da ta ji ƙwalla ta zubo mata. Saboda rana ta farko kenan, da suka raba makwamci da Alhaji tun tsawon shekara ashirin da biyar da aurensu. Alwala ta ɗauro ya fara gabatar da sallolin nafila, ta shiga kwararo addu'o'i sannan ta ji zuciyarta ta yi mata sanyi.
WASHEGARI
Asubar fari ta ji ana buga mata ƙofa, a hankali ta yunƙura ta zage sakatar ɗakin. Alhaji ta gani sanye ta doguwar rigar, ta ɗan murza idanunta ta ce.
"An kira sallar Asuba ko?"
Murmushi Alhaji ya yi yana É—an sosa kai ya ce, "A'a tukunna dai."
Shiru ta yi tana jiran abin da ya kawo shi a lokacin, Alhaji ya sunne kai ƙasa ya ce.
"Wallahi dama ashe gas É—inta ne ba a haÉ—a mata ba. Shi ne na ce za ki É—an É—ora mana ruwa."
Ƙirjinta ne ya yi wani irin bugu da ƙarfi, nan take ta ji zuciyarta ta ɗauki tururi. Da wani irin kallon mamaki ta kalle shi, don ta yi tsammanin ko babu komai zai ji nauyin yi mata wannan maganar. Tun da kawaici mai sunan kawaici ta yi a lokacin shirye-shiryen aurensa.
"Amm... dama... saboda ta ce ba za ta iya amfani da ruwan sanyi ba ne..."
Alhaji Umar ya furta a rarrabe cikin jin nauyi, musamman da ya lura da irin kallon da take jefa masa.
Ummou Aslam Bint Adam🌚
07062062624
[17/06, 18:06] Ameera Adam: *DAHUWAR ƘAHO*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
GargaÉ—i: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ko É—orawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.
Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne.
SHAFI NA BIYU
Haɗiye yawu mai ɗaci Hajiya Karima ta yi, ta shanye abin da yake ƙunshe a saman ƙirjinta ta ce.
"Babu damuwa."
Fitowa ta yi ta za ta nufi ƙofar kicin ɗinta jiki a sanyaye Alhaji Umar ya ce.
"Na ce ko na zo na É—ora, na ga kamar na katse miki bacci."
Kallon tsaf ta yi masa, kamar za ta yi shiru sai kuma ta ce.
"Da ka san za ka iya É—orawa kuma ka taso ni?"
Shiru ya yi mata baice komai ba, Hajiya Karima ta É—auki tukunya ta É—ora musu ruwan. Kan kujerar falo ta ga ya je ya zauna, har ta juya za ta shiga É—aki daga can É—akin Shukura ta ji an ce.
"Babyyyyy!"
A zabure ta ga Alhaji ya miƙe ya nufi ɗakin ta girgiza kai ta shige ɗakinta, tana tuna yadda ta ji ana cewa zama da kishiya sai an daure. Ashe dama haka matan da aka yi wa kishiya suke ji a cikin zuciyoyinsu? Ashe dama duk tsawon shekarun da ka ɗauka da miji idan ya yi aure sai ka ji zafi a ranka? Ashe gaskiya ne da ake cewa ba a tsufa da kishi haka ne? Ayarin tambayoyin da ta dinga jefa wa zuciyarta kenan, bayan ta shiga ɗaki. Sai da ta tabbatar da ruwan ya yi zafi sannan ta fito ta kashe gas ɗin ta koma ɗakinta, don ba ta son duk wani abu da zai kai kunnenta har ya ɓata mata rai. Alwala ta ɗauro saboda lokacin an fara kiran sallar Asuba, jin za a shiga masallaci ya sa ta nufi ɗakunan yaran gidan ta tashe su yin sallah.
Da gari ya waye kamar kullum ita da Ruƙayya suka haɗa abin karyawa, bayan sun kammala ta zuba na su Shukura a cooler ta ajiye musu. Ita da yara kuma, suka baje a babban falo kamar yadda suka saba idan babu makaranta. Suna nan zaune suka ga Alhaji da Shukura sun ƙaraso ɗakin sai yatsina take yi, a ɗan kunyace yake son zame hannunsa daga cikin naya saboda ganin yaransa a wurin. Sake riƙe hannunsa ta yi gam, sai kawai ya wayance da cewa.
"Mamana yau ko tayi babu? Amma dai ke kika yi girki don na ji gidan sai ƙamshi yake yi."
"Ummm!"
Ruƙayya ta furta a daƙile, saboda har lokacin ba ta daina fushin auren mahaifinsu ba.
"Hajiya barka da safiya." Alhaji ya furta yana ƙoƙarin kawar da idonsa daga cikin nata, don haka kawai yake jin nauyinta.
"Barka dai Daddyn yara ya kwanan amarya?"
Alhaji ya washe baki ya ce, "AlhamduLillah."
"Daddy ina kwana." Yaran suka haÉ—a baki suka gaida shi, amsa musu ya yi sai ya ce.
"Ba ku gaida Auntynku ba."
"Mazan ne kawai suka gaishe ta, amma Ruƙayya ko ƙurarta ba ta kalla ba." Zama Alhaji ya yi a ƙasa, ita ma Shukra ta zauna a kusa da shi tana ta yarfe hannu alamun ba ta jin daɗin jikinta.
"Ina kwana."
Shukra ta furta wa Hajiya tana sake yamutsa fuska, Hajiya ta luwa sarai da yanayin Shukra sai ta yi kamar ba ta gane ba ta ce.
"Lafiya ƙalau, ya kwanan baƙunta."
"AlhamduLillah." Shukra ta furta tana lafewa a jikin Alhaji. Miƙewa Ruƙayya ta yi za ta bar falon, mahaifiyarta ta ce.
"Mami ɗauko abincin Auntynku a kicin." Wani baƙinciki ne ya mamaye ta, ta wurga mata harara karaf idonta ya haɗu wuri ɗaya da na Shukura. Wani siririn murmushi Shukura ta yi a cikin zuciyarta ta ce.