Sashe 64
Dahuwar Kaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ga mamakin Mahmud yana zuwa ya tarar Laraba ba ta nan, a tsorace ya ajiye É—an buhun zabbin ya yi sauri ya faÉ—a motarsa ya fisge ta da gudu ya bar cikin dajin.
Tun da Laraba ta hango shi ya tunkaro ta, take ƙyaƙyata dariya tana da saman bishiyar dalbejiya har Mahmud ya ja motarsa ya yi gaba.
Dirowa ta yi ta buɗe buhun tana dariya har da riƙe ciki, sai kuma ta yi shiru tana tunanin yadda za ta yi da zabi har guda huɗu. Mai daban-daban ne ya faɗo mata a rai, wani mai nama da yake can tsallaken ƙauyensu, wanda ya jima da cewa yana sonta. Da sauri ta suri buhun kamar marar gaskiya ta shiga bi ta cikin gonaki ya har ta isa wurinsa.
"Larabayyo 'yar Larabatuwa! Yanzu Laraba sai ki dinga guduna, saboda Allah mene ne aibuna?"
Mai daban-daban ya furta mata cike da so. Laraba ta maze ta ce, "Mai daban-daban ka san shi so makaho ne, to kwanaki shi ya lulluɓe mini idanu a kan wani mutumi amma yanzu ba ya gabana kai nake so!"
Wani irin daÉ—i ya mamaye shi don haka ya ce.
"Kai amma na ji daɗi Laraba, wallahi yau da ƙyar zan iya yin bacci yanzu faɗi duk abin da kike so a wurin nan a yanka miki."
Laraba ta yatsina fuska ta ce, "Eh wancan balangun za ta yanko mini ko yanka sha biyar ne, amma kafin nan ga zabin Inno nan ta ce a kawo ka gyara ka gasa mata."
Jikin mai daban-daban har karkarwa yake, ya fara yankawa Laraba nama. Ya kalli wani yaronsa ya buga masa tsawa a kan ya karɓi buhun hannun Laraba ya je ya gyara su. Bayan ya miƙa wa Laraba balangun ta ce.
"Na gode sosai masoyina mai daban-daban, yanzu waɗannan zabin idan ka gama gasa su ka ajiye da daddare zan zo na karɓa." Mai daban-daban ya amsa mata yana washe baki. Laraba har ta yi gaba ta waiga ta sake jan kunnensa, a kan kada ya aika zabin gidansu za ta dawo ta karɓa da kanta.
Mahmud bai yi tafiya mai nisa ba, isa bakin wani babban symbol ɗin sabulun wanka da ke gefen titi. Ya ciro waya ya kira abokinsa Muddasir, wanda suka yi da shi za su haɗu a adaidai wurin da ya kwatanto masa. Bugu biyu wayar ta yi ya ɗauka. Daga can ɓangaren ya ce.
"Ga ni nan ina hango ka na kusa ƙarasowa!"
Daga haka Muddasir ya katse. Cikin ƙasa da minti ɗaya mai adaidaita sahu ya sauke shi. Sai da Mudassir ya biya shi kuɗinsa ya ƙarasa wurin motar Mahmud ya ce, "Mutumina ashe ka gane kwatancen!"
Cike da damuwa Mahmud ya ce, "Allah ka yi mana tsari da ƙauye, yanzu saboda Allah a nan za mu yi service?" Mudassir ya yi murmushi yana zama a sit ɗin gaba ya ce.
"Kai kukan daÉ—i kake yi, da muka samu aka canza mana school zuwa ta garin Gangaren dutse? Da ace an bar mu a garin Rafin gurgu fa? Yanzu ba ga su Haidar can ba suna fama."
Mahmud ya saki guntun tsaki ya ce, "Yanzu ina za mu bi mu ƙarasa garin Gangaren dutsen?"
Mudassir ya nuna masa hanyar shiga garinsu Laraba, gabansa ne ya faÉ—i amma sai ya basar don ba ya san ya sanar da Mudassir abin da ya faru da shi ya yi masa dariya.
Ganin sun tunkari hanyar garinsu Laraba ya sa Mahmud ya ce, "Wai ina ne garin? Mun kusa zuwa ko da saura. Mudassir ya ce, "Mun kusa zuwa, da ka miƙe za mu bi ta kan doguwar hanyar can har ƙofar gidan mai gari, ka san dole sai mun gabatar da kanmu a wurinsa tun da zama ne ya kawo mu.
A hargitse Mahmud ya taka burki cikinsa yana kaÉ—awa, Mai garin da ya gama sakawa zawo a wando ne za su je wurinsa su gabatar da kanku?
"Lafiya Mahmud?"
Mahmud da gumi ya gama rufe shi kamar zai yi kuka ya ce.
"Wallahi ba lau ba Mudassir."
Ya ƙarasa maganar yana yin parking ɗin motar a gefen hanya, sai kawai ya kifa kansa a kan sitiyarin motar.
Cike da shauƙi Mai Yasin yake kallon Inno jin amsar da ta ba shi, dangane da sanar da iyalanta a kan maganar aurensu. farinciki fal zuciyarsa ya ce.
"Allah mai haɗa jinin mumini da mumini, Allah kaɗai ya san alkairin da yake ɓoye da silar haɗuwarmu a Saudiyya. Haka kawai na ji kin sake kwanta mini Inno, a gaskiya marigayi ya dace da mace."
Inno ta saki murmushin jin daɗi kanta a ƙasa, ita dai nutsuwar Malam da daɗaɗan kalamansa waɗand ta rasa a baya suna birge ta. Har a cikin zuciyarta tana jin ina ma tun tana budurwa, Allah Ya aiko mata shi cikin rayuwarta, da babu yadda za a yi ta yi rayuwa da tsohon mijinta da ko kaɗan bai iya soyayya da tarairaiyar mace ba. Mai Yasin ya saci kallonta da gefen ido ya ce. "Innota ko ba kya jin daɗin yabon da nake yi miki? Ko da za ki ji babu daɗi sai dai ki ji, amma Allah Ya sani ƙaunarki ta jima da ɗamfaruwa a cikin zuciyata."
Inno ta É—ago ta dube shi ta ce. "Haba Malam, ai duk macen da ta yi dace da kai a matsayi mace ta more a gidan duniya da Lahira."
'An zo wurin, dama nan nake ta jiran mu ƙaraso.'
Malam ya raya a cikin ransa, yana murmushi mai ɗauke da manufa a ransa. Ya ƙanƙance murya cikin yaudara da karuwanci ya ce.
"Wallahi tun da na wayi gari jikin nan yake son dawo mini Inno, ga bakina salam babu daÉ—i kamar yawun mage. Nace ko zan samu koda kaza ko naman kasuwa?"
Inno ta sauke ajiyar zuciya, tana mamakin yadda Mai Yasin ba ya gajiya da murƙushe cinyoyin kaza, amma da ta tuna a kullum ya ci kazar ya kuma sharɓi romonta ƙara samun lafiya yake sai ta ce.
"To Malam ka ga dai yaran nan ɗazu kusan baram-baram muka rabu da su dutse a hannun riga, kuma dama mai ƙoƙarin sayo maka Iro ne. Yanzu dai ban san cikinsu wa zan tunkara ba, tun da kazar jiya ma shi ya taho da ita."
Mai Yasin yana gama jin haka sai kawai ya fashe da kuka, ya fara jan magina yana matsar ƙwallah. Sororo Inno ta yi jiki a sanyaye ta ce.
"Lafiya malam?"
Mai Yasin ya ja majina ya ce, "Kaico rashin haihuwa, kaicona Allah ka cigaba da ba ni dangana. Da 'ya'yan da na haifa ne ai duk tsiya za su kawo mini duk kuwa yadda muka yi da su, yanzu kamar dai garken wannan yaron Inu har sai na tambaye shi idan na yi niyyar ɗiban kaji ko zabi? Amma tun da ban haifa ba dole na yi haƙuri da rayuwa."
Shiru Inno ta yi tana nazari don ta san mammaƙo irin na Yaya Inu, amma don ta kawar da damuwar Malam sai ta ce.
"Daga yau kada ka sake faÉ—in yaran nan ba kai ka haife su ba, kai tamkar mahaifinsu ne kuma duk abin da kake muradi, ka yi kanka tsaye ko ka tambaye ni idan kana jin nauyi."
Malam ya hau gyaɗa mata kai, Inno ta miƙe tsaye har ta je bakin ƙofa ta juyo ta ce.
"Kaji kake so ko zabi?"
Malam ya sake narkewa a katifa yana sakin murya a dole shi marar lafiya ya ce, "Idan da so samu ne a samo matasan samarin zakaru masu jini a jika, tun da ai muma a wannan satin ne tariyarmu!" Inno ta saka mayafin ta rufe fuska ta fice tana dariya, tana fita Mai Yasin ya buga tsalle a kan katifa yana rawar oya shake body.
Kai tsaye sashen Yaya Inu Inno ta nufa, a lokacin da ta je ba ya nan sai matansa. Cikin girmamawa suka gaishe ta, bayan ta amsa ta ce su buɗe mata garken awaki da shanunsa. Kusan lokaci ɗaya suka kalli juna, Larai ta yi ƙarfin halin faɗin.
"Inno amma bai ce za ki zo É—aukar..."
Cikin tsawa Inno ta katse ta.
"Dama ban ce miki na faɗa masa ba, Malam ne ya ce mini yana sha'awar matasan samarin zakaru ni kuma na zo zan bincika masa, idan ya zo ki sanar da shi abin da na sanar da ku." Daga haka Inno ta nufi garken ta hankaɗa ƙofar zagayen da ƙafarta. Safare da Dubu 'ya'yan Yaya Inu ne suka taya Inno ɗiban zakarun guda uku ta fice da su, ta yi wa Malam magana da kansa ya fito zuwa bakin rariya ya yanka su. Inno ta ɗora ruwa ta shiga gyaran kaji, sai ga shi babu jimawa ƙamshin farfesun kaji ya cika gidan, ta zuba a babban food flask wanda ta saba zuba wa Malam ta kai masa. Ta ɗebi ɗan madaidaici ta ragewa Laraba a kai, ƙafa da wuya a cikin tukunya.
Cikin sauri Yaya Inu yake tafe, hannunsa riƙe da baƙar leda wacce take cike da sababbin magunguna da ya taho da su daga bakin kasuwa. Saurin da yake yi La'asar ta ƙarato, ga shi mai maganin sanyin da ya saya ya sanar da shi ba a wuce ƙarfe huɗu na yamma ba tare da an dafa an sha shi ba, saboda ƙa'idarsa kenan. Shi kuma a ranar yake son yin amfani da shi kuma ba ya fatan lokaci ya ƙure, shawo kwanar da zai yi ne ya ci karo da Hajara tsohuwar matarsa wacce ya ji labarin mijin da take aure ya mutu. Dama tun da ya saki Abu zuciyarsa ta shiga wasu-wasi a kan ya dawo da ita.
"Ranki shi daÉ—e, yau Hajara ce a gari?"
Yaya Inu ya faÉ—a yana washe baki, Hajara ya É—an yatsina fuska ta ce.
"Eh ni ce sai aka yi yaya Inusa?"