← Book details Dahuwar Kaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 81

Sashe 19

Dahuwar Kaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yanzu shi kenan sun daki banza da wofi ko? Wallahi ba zan sake kwana a gidan nan ba, kuma wallahi idan ban rama ba sai ka sake ni" Da sauri Daddy ya janyo Shukura jikinsa ya ce, "Babu inda za ki je, kuma mari kamar kin rama kin gama." Shukura da ke gaban Mommy ta É—aga hannu ta zabga mata mari a fuska, ko sauke hannu ba ta yi ba Haidar ya É—auke fuskarta da mari. A zafafe Daddy shi ma ya sauke wa Haidar mari sannan ya ce.

"Ni za ka wulaƙanta ka tozarta Haidar? Ashe kai ma ba ka da mutumci?" Rai a ɓace Haidar ya ce, "Daddy ba ka ga abin da ta yi ba ne? Ni fa dama na jima ina tara yarinyar nan. Wallahi tuntuni darajarka take ci, da tuni na ɓarar da ita." A zafafe Daddy ya ce.
"Za ka gane ba ka da hankali kuwa, idan hauka ne a kanka zan sa a sauke maka shi." Yana gama faÉ—a ya zaro waya ya nemo wata lamba, yana jin an É—auka ya ce.

"Hello officer, ina son ganinka yanzu. Please ka taho da yaranka." Daga haka ya katse wayar, da mamaki Mommy take kallonsa kamar za ta tanka masa sai kuma ta haƙura. Suna nan tsaye suka ga ya ja hannun Shukura yana lallashi suka fita. Daga Haidar har Ruƙayya rungume Mommy suka yi, Mommy da Mami sai kuka suke yi. Haidar ne ma yake iya lallashinsu, ba su ɗauki lokaci ba suka haɗa kaya a cikin akwatunansu. Gabaɗaya kallo ɗaya za ka yi musu ka fahimci suna cikin matsananciyar damuwa. Suna gab da fitowa suka ji ƙarar motar 'yan sanda, babu jimawa suka ji muryar Daddy yana cewa.

"Ku shigo ga yaron nan, ku zo ku tafi da shi. Ba shi tarbiyya ko kaɗan yaron nan, duk wanda ya zo belinsa kada a bada shi sai saka hannuna. Ku hora shi yadda ya kamata." Mommy da su Haidar suna tsaye, suka ga 'yansanda biyu sun shiga falon Mommy. Nan take suka saka masa hangoff a hannu, Daddy ya ba su umarnin su tafi da shi. Mommy tana kuka tana riƙe shi haka suka tasa ƙeyarsa suka tafi da shi, da ƙyar Ruƙayya ta lallashi Mami ta tsagaita da hawaye. Sannan suka ɗauki jakunkunansu suka fito harabar gidan.

GIDAN HAFIZ

Wani dogon tsaki Bilkisu ta saki cikin jin haushi ta ce.
"Da ka san ba kai kaÉ—ai ba ne ai da sai ka sanar da ni." Ajiye akwatin Amina ya yi ya rungumo ta jikinsa ya ce.

"Kafin a fara faɗan ya kamata a yi mini oyoyo ɗin tukunna." Ajiyar zuciya Bilkisu take saukewa akai-akai, saboda yadda ta ji zuciyarta tana harbawa kamar ta faɗo daga ƙirjinta. Amina ta taɓe baki ta ce.

"Sannu da gida Aunty."

A sheke Bilkisu ta dube ta, ta ce. "Ke zan yi wa sannu, ni da nake gidan mijna sannun me za ki yi mini." Amina ta fahimci maganarta, don haka ta ce.
"Ai da yake tare muke da Habibi, na san kuma kin sha aikin gida shi ya sa na miki sannu. Ga shi sai da na ce ya kira ki kafin mu ƙaraso amma ya ƙi."
Bilkisu ji ta yi kamar an zuba mata borkon, Hafiz da ke tsaye mamaki ya kama shi, don shi dai ya san bai yi haka da Amina ba. Yana shirin yin magana Amina ta yi gaba tana faÉ—in.

"Baby ka shigo mini da akwatin, kuma ni yau kwana za ka yi kana matsa mini ƙafa don ciwo take yi mini."
Bilkisu jin haka ya sake hargitsa ta, rai a ɓace ta saki hannun Hafiz ta wuce ɗaki fuuuu kamar za ta tashi sama. Amina tana ganin haka ta saki murmushi, a ranta ta ayyana.
'Ashe dama matar nan sakarya ta mayar da ni, shi ne take kunna ni ban sani ba. Ai kuwa da ni take zancen.'

Tana shiga É—aki Hafiz ya shigar mata da akwatin, sannan ya fito ya nufi É—akin Bilkisu. A kan kujera ya same ta, ya faÉ—aÉ—a fara'arsa ya ce.
"Baby kin yi kyau sosai." A madadin ta ba shi amsa sai ta ce.

"Wato Hafiz ni ka so tozartawa ko? Saboda za ka dawo da matarka shi ne ba za ka sanar da ni ba. Na gode, ai yanzu amfanina ya ƙare tun da ta dawo." Zama Hafiz ya yi a gefenta ya ce.
"Haba Bilkisu, me ya sa za ki ce haka? Ina kasuwa mahaifinta ya kira ni, amma don Allah ki yi haƙurin rashin kiranki." Yana rufe baki sai kawai Bilkisu ta fashe da kuka, janyo ta jikinsa ya yi ya shiga lallashinta. Sai da ta tsagaita da hawayen sannan ya ce.

"Ina abincina?"

"Yana kicin." Ta ba shi amsa a daƙile.

Har ya miƙe zai fita ya waigo ya ce.
"Am dama tun da Amina ta dawo, a É—akinta zan kwana yau."

"To mene ne na faÉ—a mini Abban Sayyid, ai duk abin da ka yi ka isa ne. Da za ka dawo da ita ka faÉ—a mini? Sai don za ka je ka kwana a wurinta za ka yi mini 'yar murya, duk abin da mutum dai ya yi Allah Yana kallo." Murmushi kawai Hafiz ya yi ya fita, don ya fahimci rikici Bilkisu take ji, idan ya ce zai tanka mata sai ta mayar da abin ya zama babba.

A ranar kwanan farinciki suka yi tsakanin Hafiz da Amina, duk wani tabon da take kallon Hafiz da shi ya goge. Kuma tun daga wannan lokacin Amina ta sauya taku, duk wani motsi da furucin Bilkisu tana ganewa. Don haka koda ta yi wani abin Amina ba ta nuna mata ta damu, wannan dalilin ne ya sa Amina ta cigaba da zaman aurenta cikin kwanciyar hankali. Sai laulayin cikin da yake danunta, shi ma a lokacin da ya shiga wata huɗu sai laulayi ya yi mata sauƙi sosai. Don babu abin da ba ta ci sai wanda ba a rasa ba, haka kuna ta ɓangaren ciwo zazzaɓin dare da yawan ciwon kan da take yi duk ta daina.

Ana cikin haka sai Bilkisu ta tsiri duk ranar da Hafiz yake ɗakinta, a ɓoye za ta aiki yaranta gidan wata ƙawarta Maman Siyama, da yake yaran Maman Siyama sun girmi su Sayyada sai su sayo mata Nama ko kifi a ɓoye. Sai ta yi girki da shi, ko kuma da safe ta sayo ƙwai tun da dare ta soya musu ita da yara. Haka wunin ranar Amina za ta yi ta cika tana batsewa, kuma sai abin ya haɗe mata ga saurin fushi irin na mai ciki ga kuma abin da Bilkisu take yi. A irin haka har faɗa suka taɓa yi da ita da Hafiz, ya yi mata rantsuwar duniya a kan ba shi yake saya wa Bilkisu ba ta ƙi yarda. Tun yana lallashinta har ya yi watsi da ita, sai watarana da ta jin sallamar yaro bayan ya shiga ɗakin Bilkisu har zai fita ta bi shi soro da sauri. Murmushi ta yi masa cikin bugar ciki ta ce.

"Ni kam kifin da kake sayo wa Maman Sayyada yana da arha kuwa? Naman da kifin wanne ya fi sauƙi ne?"
Yaron ya yi jim sannan ya ce. "Gaskiya kifin ya fi arha don Ummanmu ma shi take saya, amma na ga ita Maman su Sayyid ta fi son na sayo mata nama." Jinjijna kai ta yi ta ce.

"To je ka, na gode ka ji."
Ya amsa mata ya tafi.

ÆŠaki ta koma tana nazari, sai kuwa ta É—auko waya ta kira Hafiz sai da ta ji ya É—auka sannan ta fita tsakar gida ta ce.

"Hello Habibi, ba na jinka ko network ne?" Bilkisu tana tsakar gida tana koyawa su Sayyada aikin makaranta, ta ji muryar Hafiz raÉ—au a kunnenta. Amina da ta tabbatar da Bilkisu ta ji, sai ta fakaici idonta ta katse kiran ta ce.

"Yawwa dama na ce, don Allah idan za ka taho ka biya gidan Aunty Nana ka ba ta kuɗin naman kai ƙafa, don gobe farfesunsu nake so kuma ba na son na yi wahalar dafa su." Sai ta shige ɗaki ta ce.

"Eh network ɗin ya dawo, to shi kenan Hubby Allah Ya bar mini kai." Amina ta leƙa ta windo ta ga Bilkisu ta yi kasaƙe har da sakin ƙwafa.
Tun a daren ranar ta kira yayarta Aunty Nana ta tura mata kuÉ—i, ta ce da safe ta aika yara a sayo naman kai ta yi mata farfesu, idan ya so da rana idan Hafiz ba ya gida sai ta aiko a kawo mata.

Kamar yadda suka tsara Amina tana zauna a tsakar gida washegari da rana, tana sai ga Usaina 'yar yayarta ta yi sallama. Da yake budurwa ce, kuma Amina ta kitsa mata komai tana shiga cikin É—an É—aga murya ta ce.

"Aunty ga farfesun naman kan, wai Umma ta ce ga canjin dubu ɗaya da ɗari biyar na Yaya Hafiz." Amina ta karɓa ta buɗe, take ƙamshin ya mamaye gidan har ta ji yana shirin saka ta amai. Gani suka yi Bilkisu ta fito, Amina ta ɗan yamutsa fuska saboda dama can naman kai bai wani dame ta ba ta ce.

"To ku kunci ne?" Yarinyar ta girgiza kai, sai ta ɗauko wata ƙaramar roba ta ɗauki ƙafa ɗaya ta ɗora a kai da romo ta ce a miƙa wa Bilkisu. Tun Usaina ba ta rife baki daga sallamar da ta yi wa Bilkisu ba, ta buga mata tsawa da cewar ba ta ci. Dariya Amina ta yi a ranta, ta dubi Usaina ta ce.

"Ungo canjin nan nasa je ki kanti ki sayo mini multina guda biyu, don wannan naman kan ba lallai na iya cinye shi ba sai dai ki tafi da shi."

Babu jimawa Usaina ta sayowa Amina, sai da suka shiga ɗaki sannan Amina ta yi ƙasa da murya ta ce.
"Maza ki mayarwa da Aunty naman kan nan, don wallahi daurewa kawai nake yi ji nake kamar zan yi amai." Dariya Usaina ta yi, ta yi saurin fita daga gidan ba tare da Bilkisu ta ganta ba.
Chapter 19 · 0% Book details