Sashe 12
Dahuwar Kaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Hello Abban Sayyid, na ce ka haÉ—o mini da tsiren jiya da ka sayo mini. Amma dai yau kada a cika albasa, sai kuma su Sayyada yogot É—in nan za ka taho musu da shi." Sai Bilkisu ta yi shiru kamar ana ba ta amsa sannan ta sake cewa.
"A'a ba sai ka sayo mini kifi ba, kai dai ka sayo wanda za ka ci taliyar da shi." Ta sake yin shiru sai daga ƙarshe ta ce.
"A'a ai abin da Amina ta yi maka bai kai ka ce za ka ƙauracewa kwanan ɗakinta ba. Ba a yi haka ba, gaskiya kada kasa ta ƙulla ce ni. Sai dai ka shigo kawai." Bilkisu ta lallaɓa ta koma kan kujera tana ƙunshe dariyar ƙeta, saboda ta san babu tantama Hafiz ba zai shigo ba sai da kifi. Ɗabi'arsa ce indai ta yi shinkafa ko taliya fara da mai to ba ya taɓa ci sai ya sayo kifi ya ci da shi, ita da yara kuma sai ya sayo musu balangu ko tsire.
Amina tana daga ɗaki wani irin takaici ya lulluɓe ta, musamman da ta ji wai Hafiz yana faɗa wa Bilkis zai ƙauracewa kwanan ɗakinta. Kiransa ta gani, saboda haushi kawar da kai gefe ta yi ba ta ɗauka ba. Miƙewa ta yi ta shiga uwar ɗaki ta cire kwalliyar atamfar da ta yi, ta ɗauki wasu riga da wando marasa nauyi na bacci ta saka, sannan ta fita ta ɗauro alwalar Isha'i ta gabatar da sallah.
Tana nan zaune ta ji sallamar Hafiz, mamaki bai gama kashe ta ba sai da ta ga Hafiz ya nufi ɗakin Bilkisu. Bai wani jima ba, ta ga ya ɗawo ɗakinta ya zauna, sai dai har lokacin fuskarsa a haɗe take. Kifin da ta ga ya fito da shi ya sake tabbatar mata da wayar da ta ji Bilkisu tana yi, Hafiz bai kalli ɓangaren da take ba ya ce.
"Idan za ki ci ki sauko."
Haushi ya kama ta da jin abin da ya faÉ—a, zuciya ce ta ciwo ta ta ce.
"Na ƙoshi."
Sai a lokacin ya ɗago ya kalle ta, bai tanka mata ba ya cigaba da cin abincinsa. Sai da ya gama ya tura mata ledar wani ƙunshin kifi gabanta ya ce.
"Ga shi nan ki tashi ki ci."
"Na ƙoshi ka cinye."
Amina ta faɗa a karo na biyu, ransa ne ya ɓaci don ya san ba ta ci abinci ba. Cikin faɗa ya ce.
"Wai saboda na yi miki faɗa shi ne za ki hau ɓata rai? Wani sabon hali za ki tsiro mini Amina? Kin san asarar yawan abincin da kika yi mini?" A ɗan zafafe ita ma ta ce.
"To yanzu me nace maka? Kawai don na ce na ƙoshi sai ya zama abin faɗa? Idan ba da son ranka ka dawo za ka kwana a nan ba, ba sai ka koma can."
"Me kike nufi Amina?"
Ya jefa mata tambaya rai a ɓace. Shiru Amina ta yi, cikin hawaye ta miƙe ta shiga ɗaki tana kuka. Kukan da Amina ta yi shi ya sake harzuƙa Hafiz, don gani ya yi bai ga abin fushi da kuka ba saboda kawai ya nuna mata kuskurenta. Hafiz yana gama cin abinci kallo ya kunna, don ba ya son ya sabarwa kansa da zaman majalisa. Yana nan zaune har ya ji bacci don haka ya kashe ya shiga ɗaki, a lokacin da ya shiga Amina ta yi bacci. Rage kayan jikinsa ya yi sannan ya haye gado ya kwanta.
Duk abin da ya faru tsakanin Amina da Hafiz, Bilkisu tana laɓe tana jin su. Daɗi ne ya cika ta, cikin farinciki ta koma ɗaki ta buɗe ledar kifin da Hafiz ya ajiya mata. Sai da ta cinye shi tas, sannan ta ɗauki ruwa ta sha ta haye gado ta kwanta hankali kwance.
WASHEGARI
Washegari koda Amina ta tashi yanayinta babu yabo babi fallasa, haka shi ma daga wurin Hafiz. Sai da ta zo yin wanke-wanke ta juye shinkafar a leda, saboda ko akuyoyi ba za su iya ci ba. Bilkisu ce ta sharo ɗakinta a lokacin tuni Hafiz ya jima da fita, da gayya ta sharo wata ƙatuwar takardar tsire wacce take sharkaf da mai, ƙuli da albasa. A yatsine ta sharo takardar da ta yi fakaka a saman makwashin shara ta ce.
"Shi ma Abban Sayyada na faɗa masa ya cewa mai tsiren nan ya rage zabga mana albasa, amma kullum sai ya manta." Ta gefen ido Bilkisu ta kalli Amina da ke wanke-wanke, sai da ta je wucewa ta gabanta sannan ta saki takardar ta faɗi ƙasa da gayya don ta gani. Tsugunnawa Bilkisu ta yi ta share ta saka a shara, sannan ta wuce ɗaki tana murmushin mugunta. Wunin ranar haka Amina ta yi shi cikin damuwa, zuciya ta raya mata munafurcin da Hafiz zai tsiro mata. Har take ji a ranta da ya san ba zai yi musu adalci ba, da ba ta aure shi ba. A yammacin ranar sai da ta yi wanka sannan ta ɗora girki, bayan ta gama ta ɗebi nata ita da Hafiz sannan ta ba wa Bilkisu da yaranta. Kuma a wannan ranar lafiya ƙalau suka ci abinci, har Hafiz yana janta da hira saboda girkin da ta yi ba ƙaramin daɗi ya yi masa ba. Hakan ne ya sanyaya zuciyar Amina har ta sauko daga fushin da take yi, ta so ta yi masa magana a kan rashin adalcin da ya fara yi amma sai ta ƙyale shi don kada ya ga kamar ta cika ƙorafi.
Sannu a hankali rayuwar gidan Hafiz ta cigaba da tafiya, da daɗi babu daɗi haka suke rayuwa. Saboda kusan kullum da abin da Bilkisu take tsiro da shi, musamman idan Hafiz yana ɗakin Amina. Sautari idan yana ɗakin Amina sai dare ya yi za ta buga masa ƙofa ta ce ɗaya daga cikin yaran babu lafiya, ko kuma ta ce ya fito ya duba mata ɗakinta ta ji motsin wani abin. Tun Hafiz bai fahimta ba, yana biye mata. Har ya fahimci kamar da makirci a cikin lamarinta, saboda idan yana ɗakinta lafiya ƙalau suke kwanciya su yi bacci.
Ana cikin haka sai Bilkisu ta tsiri idan Hafiz yana ɗakinta sai ta fice ta koma cikin yaran ta kwanta, a ranar farko da ta yi da ya tambaye ta sai ta ce ita ta fi jin daɗin kwanciya a cikinsu. Da ya nemi kasancewa da ita nan ma sai ta ce ba ta buƙata, daga haka sai ta koma idan ya dawo ɗakinta sai dai ta zauna ta yi ta rusa kuka ko ta ce ya sake ta. Hakan ba ƙaramin ɗaga hankalinsa ya yi ba, da ya tambaye ta sai ta ce masa idan yana ɗakinta ji take kamar ta kashe shi. Kuma sai jikinta ya ɗauki zafi kamar ana dafa namanta ko ana tsira mata allura. Wannan lamarin ne ya ɗaga hankalin Hafiz, ya shiga nema mata maganin aljanu a tsammaninsa ko su suka fara shafarta. Watarana da safe Hafiz yana shan shayi, ta fara shara, da gayya Bilkisu ta sharo ƙarƙashin kujera sai ga wata ƙatuwar laya ta fito. Da mamaki ta ɗauki layar ta ce.
"Abban Sayyid kai ne ka ajiye ta." Yamutsa fuska ya yi ya ce
"Ni kuwa me zai haɗa ni da laya Bilkisu? Miƙo mini na gani." Ƙin ɗauka ta yi ta janye gannu gefe ta ce.
"Cab wallahi ba zan taɓa ba, haka kawai ban san ta mece ce ba zan taɓa ina zaune ƙalau." Miƙewa ya yi ya ƙarasa wurin ya yi bismillah ya ɗauka. Ya shiga warwarewa yana buɗewa sai ga wani busasshen ɗanyan nama, da ƙananan allurai a ciki. Wata takarda ya gani ya buɗe ta, a ciki ya ga an rubuta sunansa da na Bilkisu na farraƙu. Daga ƙasa kuma an saka sunansa da na Amina an yi rubutun mallaka." A firgice ya ɗago yana bin Bilkisu da kallon tausayi, sai a lokacin ya fahimci irin abin da ta ce masa tana ji a cikin jikinta. Kamar Bilkisu ba ta san da komai ba, ta matsa kusa da shi ta ce.
"Me aka rubuta a ciki, ba ni mu gani." NaÉ—e takardar ya yi, don ba ya son ta gani ya cusa a aljihu ya ce.
"Ƙarasa shararki babu damuwa." Haɗe fuska Bilkisu ta yi ta ce.
"Kamar ya babu damuwa Abban Sayyid? Ya za a yi a ga laya a ɗakina kuma a ce ba zan gani ba, salon haka kawai a ce asiri na yi tun da dama yanzu ni ce mai lefi." Rasa abin da zai faɗa mata zai yi, sai kawai ya fice daga ɗakin ya shiga ɗakin Amina. A lokacin da ya shiga tana kwance, saboda a kwana biyun gabaɗaya ba ta jin daɗin jikinta. Kullum cikin tashin zuciya da kasala take, tana ganinsa ta tashi zaune a hankali. Cikin zafin rai Hafiz ya miƙa mata ya ce.
"Mene ne wannan? Me kika aikata haka Amina?"
Ita warin busasshen naman ma tayar mata da zuciya ya yi, ta É—an yamutsa fuska ta ce.
"Kamar ya ya? Mene ne wannan kuma" Takaici ne ya kama shi, rai a matuƙar ɓace ya shaƙo wuyanta yana jin kamar ya zabga mata mari ya ce.
"Ina tambayarki mene ne wannan kina tambayata? Baƙar munafuka algunguma, ashe dama haka kike ban sani ba?" Hankali Amina ba ƙaramin tashi ya yi ba, duk sai ta birkice jikinta ya fara rawa saboda Hafiz bai taɓa birkice mata irin haka ba.
GIDAN ALHAJI UMAR
Alhaji yana fita Shukura ta yi shiru, don ba ƙaramin mamaki ya ba ta ba. Bata taɓa tsammanin har kawo wannan shekarun yana son Hajiya Karima haka ba, ta shi ta yi ta buɗe drowerta ta kwaso kayanta da duk wani abu da za ta buƙata ta saka a akwati. Tana shirin saka mayafi ya dawo ɗakin. Da mamaki yake bin ta da kallo, har lokacin fuska babu walwala ya ce.
"Ina za ki?"
Kuka Shukara ta saka, ta ce.
"Wurin mahaifiyata zan tafi, gara na je can tun kai da matarka ba ku kashe ni ba. Idan na haife maka ɗanka sai ka je ka ɗauka ka kawo mata." Hankalin Alhaji ne ya tashi, cikin sauri ya riƙo hannunta ya ce.