← Book details Dahuwar Kaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 81

Sashe 40

Dahuwar Kaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ear pices ta ɗauko ta saka a kunne, ta shiga bidiyan ta kunna shi. Jikinta ya ɗauki karkarwa gabanta yana wani irin bugu da ƙarfi, lokaci ɗaya hawaye ya wanke fuskarta domin bidiyon ya matuƙar ƙazanta. Da sauri ta shiga whatsapp ɗinsa, ta ga yawanci masu saƙon duk maza ne don haka take mamaki a inda Kabir ya samu wannan bidiyom. Har za ta fita ta ga an saka costomer Hafsa lace bubu, tana shiga ta karo da emojin heart ta turowa Kabir. Can sama ta haura ta fara cin karo da saƴonnin batsar da suka tattauna, a nan ta gado wannan bidiyon na Hafsa ne tun da ga muryar ta nan ta kunna voice ɗinta ta ji."
Jikinta yana rawa ta kifa wayar, sai ta jingina da bango tana jim wata irin tsanar Kabir ta mamaye ta.

Ummou Aslam Bint Adam
+2347062062624
[11/02, 19:29] Ameera Adam: *NAUSHIN WUTA*

©®AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

GARGAÆŠI: Ban amince a sarrafa mini littafi da kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.

SADAUKARWA
Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da mata da gidan Aljanna Amin.

SHAFI NA SHIDA

Tun tana zubar da hawayen zuci don kada yaranta da ke zaune su fahimci halin da take ciki har ta gagara sarrafa zuciyarta saboda wani irin zafi da ɗacin da take yi mata. Hawaye taka sosai tana shassheka tamkar za ta shiɗe, saboda wani irin kakkarwa da jikinta yake yi ƙirjinta ya shiga bugawa da sauri-sauri. Ganin halin da mahaifiyarsu take ciki ya sa suka ƙarasa wurinta suna tambayarsu, ba ta iya tanka musu ba sai ma wani irin kallo da ta dinga bin su da shi kamar ta ga sababbin hallita. A ranta ta ayyana ƙila yarinyar da suke musayar munanan kalamai da Kabir ko kaɗan iyayenta ba su san abin da take aikatawa ba. Sai kawai ta rungumo su jikinta ta sake fashewa da wani irin kuka mai cin zuciya, ganin haka ya sa su Fatima su ma suka rairai kukan su ma.
Duk da ya san ba hali ko ɗabi'ar Fauziya ba ne binciken wayarsa, haka kawai yana wanka da ya tuna ya bar wayar a kan gado ya ji gabansa ya faɗi. Nan take ya yi sauri ya kwakkwara ruwa ya fito, don ba ya so Fauziya ta fahimci irin alaƙar da ke tsakaninsa da su Hafsee. Kamar wanda aka kifa haka Kabir ya faɗa cikin ɗakin har yana tuntume, Fauziya ta ɗago tana kallonsa ta ƙura masa ido. Ganin yanayin da ya same ta ita da yaran da kuma mummunan kallon da take wurga masa, ya sa ƙirjinsa ya buga da wani irin ƙarfi. Da gudu yaran suka tafi wurinsa cikin haɗin baki suka ce, "Abi Mami ce take kuka."

Yanayin yadda ya ga hankalin yaran ya tashi ya sa ya kalli wurin da ya ajiye wayarsa, rashin ganinta a wurin ya sa shi tabbatar da tabbas mai afkuwa ta riga da ta afku. Ya san duk irin saɓanin da za sh samu da Fauziya ba ta iya zubar da hawayenta a gaban yaran, duk abin da za su yi ko wata tattaunawa ce sai ta bari sun tafi makaranta ko kuma idan sun yi bacci amma gudun kada ya bada kai bori ya hau sai ya yi kamar bai san dalilin ɓacin ranta ba ya ce.

"Ummu banat lafiya kike hawaye a gaban yara?"

Tamabayar da ya wurga mata ta ji ta yi tamkar ya zuba mata ruwan dalma, ta dube shi cike da mamakin wai ita Kabir zai raina wa hankali. Murmushin takaici ta saki sannan ta miƙa masa wayar ta ce, "Ungo wayarka, cikina ne yake ciwo." Ya san ta faɗi haka ne saboda gudun yaran su fahimci shi ya yi mata wani abin, Na'ima ta ɗauko kwalmar maganin tarinsu ta miƙa mata ta ce.

"Ammi riƙe ki sha magani ba na son na ga kika kuka!"
Ƙuri ta yi wa yarinyar tana kallo, murya a dashe ta ce.

"Wannan maganin yara ne Na'ima, cikin nawa ya sarara idan na tashi zan É—auko maganina a cikin jaka."

"Amma za ki daina kuka?"

Na'ima ta sake wurga mata tambaya, gyaɗa mata kai Fauziya ta yi. Dai kuma ta ƙarasa gaban Kabir ta ce, "Abu ni dai ka kai Ammi asibiti, ba na son ta dinga kuka ni ma zan yi." Ta ƙarasa maganar tana janyo hannunsa. Tamkar wanda aka liƙewa ƙafa da super glue, haka ya ji ƙafarsa ta manne ta ƙasa wata irin shakkar Fauziya ta kama shi.

"Ko... ko... za mu... wuce asibiti..."

Ya furta bakinsa yana rawa, sai dai tun bai fire kalamansa ba Fauziya ta wurga masa mugun kallon fa ya sa shi haÉ—iye kalamansa.

"Ai jikin mamanku da sauƙi Na'ima, ba sai mun je asibiti ba. Yanzu dai bari na yi muku shinfiɗa kun ga gobe kuna da school."

Tana gee har lokacin idonta yana kan Kabir, da take yi masa kallo kamar tana som gano wani ɓoyayyan abu daga jikinsa. Shafa jikinta take yi don ta tabbatar ba mafarki take yi ba, ta saka hannu ta mintsini cinyarta jin zafin ya ratsa wurin ya sa ta tabbatar da zahiri ne. Tana kallo Kabir ya kashe wayar gabaɗaya, jikinsa gar rawa yake ya ɗebo kayan shimfiɗa ya yi wa yaran. Yana gama shimfiɗar ta ga ya ɗauki wayarsa ya fice daga ɗakin alamar fita ma zai yi daga gidan gabaɗaya.

Tun da ya fice Fauziya take saƙa da warwarar hukuncin da za ta yanke, ban da kai wa da kawowa babu agim da take yi. Hat yanzu zuciyarta rawa take yi a kan ko dai idanu da kunnuwanta ba su jiyo mata daidai ba. Babban abin da ya sake ɓata mata rai, yadda ta ga ya ɗauki wayar ya fice daga gidan wato duk ma abin da za ta yi ta je ta ƙarata. Ta jima tana ƙoƙarin dakatar da hawayen idonta, amma ta kowanne ɓangare ya gagara ba ta haɗin kai.
Shinshina jikinta ta fara yi tana son gano ta inda ta gaza, ta ɗaga rigarta tana kallon mamanta ko za ta ga hango aibun na jikinta. Domin Allah ya yi mata baiwa duk da haihuwarta uku ga ta huɗu za ta yi amma mamanta bai lalace, ballantana ta ce ko nata ne suka zube har yake hangen na wasu. Kuma idan ma lalacewa suka yi a tsawom shekaru bakwai da aurensu bai ci ace ya ɓoye mata ba. Har gara ya faɗa mata domin ta san matakin gyaran da za ta ɗauka. Ta matsa gaban madubi tana bin kanta da kallo, sai dai har ta gaji da tsaiwa ba ta gano makusar da za ta sa Kabir ya dinga musayar munanan kalamau da hotuna da 'yanmata.
Gajiya ta yi da tsaiwar ta zauna a gefen gado, sai ta shiga tausayin kanta da 'ya'ya matan da ta haifa.

"Wannan wacce irin rayuwa, aai yaushe zan sanu kwanciyar hankali? Sai yaushe zan samu nutsuwa kamar kowa? Sai yaushe..."

Wani sabon kukan ya sake ƙwace mata, a wannan ranar da take jin kamar zuciyarta za ta yi fiffike ta ɓullo daga ƙirjinta, ba ta shayi ko kunyar bayyana kukanta a sarari domin gurin ɗabi'u da halayen Kabir ba a ranar suka fara yi mata ba. Kamar kuwa Fauziya ta sani, su Ai'lo da ke ɗaki duk sun kasa kunne suna son gano dalilin kukan nata. Don sun san fa wuri ya dawo gida ba a buge ba, ballantana su ce takaicin rashin dawowarsa ne ya saka ta kuka.
Lawisa da ke ɗaki har sun kwanta ita da mijinta ta gagara haƙuri, ta fito zuwa ƙofar ɗakin Fauziya.

"Maman Na'ima! Maman Na'ima ke jaÉ—ai ce zan iya shigowa?"
Fauziya da muryarta ta gana dacewa ta ce, "Shigo ni É—aya ce."

Tana shiga ɗakin ta ɗan ƙasa fa murya ta ce, "Me yake faruwa MamAn Na'ima? Tun ɗazu nake jiyo kukanki lafita kuwa?"
Ta san Lawisa tana ƙaunarta tana ba ta kulawa, amma wannan wani gingimemen sirrin mijinta ne da ba za ta iya furta mata ba.

"Mahaifiyata na tuna Lawisa, mahaifiyata cw ta faɗo mini. Akwai abubuwa da dama da nake ganin iyaye mata suna yi wa 'ya'yansu Lawisa na rasa wannan gatan. Ban san wa zan raɓa na ji danshi da sanyin mahaifiyata."
Jikin Lawisa ya yi sanyi, da jin kalaman Fauziya. Domin ta taɓa ba ta tsakure kaɗan daga cikin labarinta, da irin baƙar wahalar da ta sha a hannun matan babanta. Sai ta yi tsammanin ko wani abin suka yi mata bayan ta je gidan, don haka ta dafa kafaɗarta ta ce.
"Ba kuka za ki yi mata ba Mamam Na'ima, addu'a ya dace ki yi mata. Ki yi haƙuri watarana sai labaru."Fauziya ta gyaɗa kai sannan ta yi mata godiya Lawisa ta koma ɗakinta. Tana nan zaune kimanin sha biyu da rabi na dare Kabir ya shiga gidan, a ɗarare ya zauna ya san Fauziya sarai da zafin kishi. Duk sai ya ji haushin kansa da tun yana gama gani bai goge ba. A tsammaninsa Fauziya za ta kula shi amma ga mamakinsa sai ga ko ƙurarsa ba ta kalla ba.

"Fauziya don Allah..."

"Ba na buƙatar jin komai daga gare ka." Ta furta a kausashe tana ɗaga masa hannu. Shiru ya yi ya kasa cewa uffan, Fauziya ta miƙa ta koma gefen yaranta ta kwanta ta shiga nazari da lissafin takaicin da mummunan ganin da ta yi.

Bayan Maman Nana ta koma gida haka ta sake cika fam, don tana aiki amma zuciya tana raya mata abubuwa da dama har aka yi sallar Magriba Jafar ya dawo. Yana zura ƙafarsa cikin gidan ya bi ta da wani kallon cike da ƙyama, ya saki guntun tsaki sannan ya wuce ɗaki. Yanayin fuskar Maman Nana ce ta sa ya tuna abin da ya faru kafin ya fita, don haka shi ma ya yi watsi da ita. Kaskon turaren wuta ta ɗauka har za ta fita Jafar ya ƙwala mata kira, fuska a haɗe ta ƙarasa ƙofar ɗakin ta ce.
"Ga ni."
Chapter 40 · 0% Book details