← Book details Dahuwar Kaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 81

Sashe 37

Dahuwar Kaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ke dai Maman Sabir a kullum maraÉ—inki ba ya kunya, wato yau kuma da haka kika shigo. Sabon salo kiran salla da usur, ai gara haka da ki faÉ—a É—akin da ba na ki ba."
Maman Sabir da tuni ta fahimci zancan ta ce, "Ke kuwa ai dukan da kuka yi mini ban ji da daÉ—i ba. Abin dariyar ma, baban Sabir tunkur yake zama bai yi bacci ba yana jirana."
Sai kuwa suka sake kwashewa da dariya.
Lawisa da take ɗaki take jin su kamar ba za ta tamka musu ba, sai kuma ta yi zaraf ta leƙo ya ce.

"Sai ki yi takatsantsan kuwa, domin babu ruwan Ubangiji. Ba abin mamaki ba ne ki ga Sabir ya gado ki. Ni ina fata da roƙon Ubangiji, tun da har fatan da kike yi wa kanki kenan Ubangiji Ya sa Sabir ya gaji abin da kike yi wa izigili."
Tana faÉ—ar haka ta koma É—aki.

"Wallahi sai dai ki gani a kanki, aniyarki ta biki mai mugun baki."
Maman Sabir ta furta cike da tsoro.

Fauziya suna shiga ɗaki, bayan ta saka shi ya tsallake su Na'ima da ke kwance sai kuwa ta sake shi rai a ɓaci. Daga gefen gadon ya faɗi, kansa ya bugu da katakon gado. Cikin azaba ya runtse ido yana shafa wurin, takaici ya sa Fauziya ta zauna a gefen gadon sai kawai ta fashe da kuka.

Sai da Maimuna ta tura ƙofar ta rufe sannan ta waigo tana bin bayan Maman Nana da harara, ganin za ta waigo ya sa ta saki fuska cikin wayancewa ta ce.

"Uwar gida kuma amarya a gidan Baban Nana, ke kaɗai ki sha kurumki daga ke babu ƙari."

Maman Nana ta saki guntun tsaki ta zauna a kan kujera, sai kuma Maimuna ta sha jinin jikinta duk da Jafar ya tabbatar mata da ba ta gane da wacce yake wayar ba. Amma sai ta ce, "Uwar Nana ko dai kin samo wa Abdul abokin wasa ne? Na gan ki duk a sanyaye."

Maman Nana ta zaunar da Abdul da bai wuce shekara ɗaya ba ta ce, "Ni da wannan ne ai da sauƙi, sai na saka shi ya ɗauko mini mai aiki ta dinga komai kamar lokacin da na yi cikinsa."
Cikin bugar ciki Maimuna ta ce, "To! Me yake damunki?"

"Wallahi ban tabbatar namiji munafiki maci amana ba ne ba sai yau, wai har ni Abban Nana zai munfurta?"
A razane Maimuna ta dube ta, tana shirin yin magana ta cigaba.

"Wai har ni zai dinga yin waya da budurwa a ɗaki? Tsabar wulaƙanci ya saka ni aiki, ina can ina haƙilo ko yaro ya ƙi riƙe mini ashe soyayya zai sha. Wallahi ta ci sa'a ban same ta a waya ba, da sai na ƙare wa kaf danginta zagin rashin mutumci. Sai da na raini mijina yanzu kuma 'yan'iskan mata za su fara kawo mini hari, wallahi duk yarinyar da ta yi gangancin auren mijina sai na lahantata." Ras! Ƙirjin Maimuna ya buga, don ta san halin Maman Nana akwai ta da baƙin kishi. Amma duk baƙin kishinta ba ta ji ko ɗar ɗin za ta iya rabuwa da Jafar ba. Dalilin haka ya sa ta dafa ta ta ce.

"Gaskiya ni Abban Nana ma ya ba ni mamaki, saboda Allah duka shekararku nawa da zai dinga wani kule-kulen 'yan'mata?" Maman Nana ta wara hannu tana taɓe baki alamun kema dai taya ni gani, don Maminuna ta sake zuga ta sai ta ce.

"To ai ko ni me shekara goma da aure Nazir ba shi da budurwa, ina laifin ma ya bari ku shekara ko sha biyar ne kin ga lokacin ke da yaranki kun samu jindadin da kuka samu bakin gwargwado. Amma kina zaman zamanki a kwaso miki gayyar tsiya, gara dai tun wuri ki san abin yi."

Ai kuwa nan take Maman Nana ta sake cika, rai a ɓace ta ce.
"Ai wallahi bari ya dawo, dama ai na faɗa masa sai ya kira mini budurwar idan ba haka ba zai ga ɓacin raina."

Wani irin farinciki ya mamaye zuciyar Maimuna, saboda a yanzu babu abin da yake damunta sama da ta ji Maman Nana ta ce suna cikin daɗi ita da Jafar. Ta sake taɓe baki ta ce, "To ni ban da ma abin namiji, mace har mace kamar ki me zai yi da wata kuma. Dirin nan bakin gwargwado kina da shi, gashin nan kina da na zaman falo. Ke dai a fuska ba za ce miki mummuna ba, to don Allah me namiji yake so da ba ki da shi."
Maman Nana ta yi caraf ta ce, "Jaraba fa irin ta namiji, ki duba ki ga irin magungunan da ke ɗurawa cikina Maman Dija, ke kanki shaida ce saboda Abban Nana na fara shafe-shafen man bilicin, tun da na lura yana leƙe-leƙen fararen 'yanmata."

'Ba dai leƙe ba, sai da faɗawa. Jafar ai ya yi nisan kiwo a kan alkyabbar mata.'
Maimuna ta raya a ranta, amma a fili sai ta ce.

"A toh ga shi kina ƙoƙari a turaka ma na ji kin ce ba kya sanya, to wai da ba kin ce har zauce miki yake ba?"

Maman Nana ta yi ƙwafa ta ce, "Yaushe rabo? Ni yanzu rabona ma da shi ai mun kusa sati, Abban Nana da yake da jaraba wai shi ne har yake sha mini ƙamshi jiya. Ƙiri-ƙiri mutumin nan ya ce mini ba shi da lafiya..."

"Sati fa Maman Nana? Ke kuwa kina me? A gaskiya ki dawo nutsuwarki, ni fa ba don kar na faÉ—a ki ji haushi ba da na ce wani abu."
A zabure Maman Nana ta dafa Maimuna ta ce, "FaÉ—i mana, ni da ke ai kin san ba ma haka."

"Astagafirullah ba wai zargi nake ba, sai na ga ko dai budurwar tashi ce ta É—auke masa hankali? Kin san fa 'yan'matan yanzu wallahi idonsu a buÉ—e yake, ba abin da ba sa yi wa sauraye ke kina can yashe a baki suna harkarsu."

"Bantan uba! Ai kuwa sai yanzu kika kamo mini bakin zaren."
Maman Nana ta furta jikinta yana karkarwa, sannan ta cigaba.
"Ai kuwa zan saka ido a kansa, wallahi idan na gano wani abu a tsakaninsu sai an maimaita yaƙin dunuya na biyu."
Maimuna ta cigaba da zuga ta, sai ta gama yi mata famfo sannan ta yi mata sallama ta tafi. Tana fita Maimuna ta saki shewa, cike da ƙeta ta ce. "Sakarya wawiya marar lissafi, in dai ni ce wallahi baƙinciki yanzu kika fara ƙunsa. Sai na raba ki da jin daɗin, da kike hura wa 'yan unguwa hanci kina faɗar ke mowar miji ce."

Ummou Aslam Bint Adam
+2347062062624
[11/02, 14:13] Ameera Adam: *NAUSHIN WUTA*

©®AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

GARGAÆŠI: Ban amince a sarrafa mini littafi da kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.

SADAUKARWA
Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da mata da gidan Aljanna Amin.

SHAFI NA BIYAR

Maman Nana ta fita babu jimawa yaran Maimuna suka dawo daga makaranta, hankalinta yana kan wayarta saboda so take Jafar yaa turo mata kuɗin ta goge alert ɗin. Sai da su Asiya suka ci abinci suka wuce Islamiya sannan Maimuna ta sake lalubar wayarta. Kamar ya san wayar tana hannunta nan take ta ga alert na dubu ashirin, wani irin tsalle ta buga tana riƙe baki. Jikinta har rawa yake ta shiga ɗaki ta ɗauko ƙaramar wayarta ta saka batirin ta kunnata, a gaggauce ta shiga kiransa sai dai bai ɗauka ba don dama ta san ba lallai ya ɗauka ba sai dai ya kira ta.

"Baby yanzu na ga kulin ya shigo."

Maimuna ta furta muryarta har rawa take yi, jin sautin murmushin da yake yi har cikin zuciyarta ta yi. Ta ya ce, "Yanzu saboda dubu ashirin kika kira? Haba my Moon, don Allah kada ki sake yi mini haka." Maimuna ta saki murmushi, tana shirin magana ta ji ya shagwaɓe murya ya ce.

"Ni fa na gagar haƙuri gaskiya, na biya ta kasuwar waya na saya miki sabuwar babbar waya wacce za mu dinga ganin hotuna da bidiyon juna."
Maimuna ta ji daÉ—i sosai, amma tana tsoron kada asirinta ya tonu Nazir ya gano ta.
"To ya za a yi ta zo hannuna? Kuma ni ina jin tsoron kada Nazir..."

"Idan muna magana ba na son ki dinga ce mini kina tsoron Naziru, wai wanne irin zama yake yi da ke da kike mugun jin tsoronsa."
Jafar katse ta cikin sauri, shiru Maimuna ta yi sai ya cigaba da cewa.
"A gaskiya alamu sun nuna ba kya jin daɗin zama da shi, a haka ka gan shi kamat na gari yana sunkuyar da kai ƙasa. Amma ya zo a jiye kyakkyawar mace, yana azabtar da ita." Sai kuma Jafar ya ɗan kwantar da murya ya ce.

"Haba my Moon, ki duba irin kulle da takunkumin da yake yi miki? Wai a haka kika iya zama da shi har tsawon shekara goma? A gaskiya an ci amanar kyau wallahi."

Jin maganganun Jafar sai suka soso mata mikin da yake É—amfare cikin zuciyarta, kalamasa suka yamutsa zuciyarta tana jin É—acin yaudarar da Naziri ya yi mata a shakarun baya.

"Hmmm ai Nazir ya dasa mini mikin da zai jima a zuciyata bai goge ba, lokaci kawai nake jira my baby."

"Kada ki jira lokaci Moon, kamata ya yi lokaci ya jira ki. Saboda yara uku rak ba za su hana ki rawar gaban hantsi ba. Wai ma kina kallon kanki a mudubi kuwa?"
Chapter 37 · 0% Book details