Sashe 73
Dahuwar Kaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abin duniya goma da ashirin ya haÉ—e wa Yaya Inu, ya haÉ—iyi yawu mai É—aci kamar zai yi kuka ya ce.
"Billahillazi la'ilaha'ilahuwa ban taɓa aikata wannan ɗanyan aikin ba. Ni fa shi ya sa nake tantama, magana ta Allah a ce duk dangina babu zabiya sai yanzu zan haife ta. Wallahi tun ban kai ku wurin hukuma ba, Abu ki ɗauke yarinyar nan ki kai ta wurin ubanta. Da ma ni da ke babu kare bin damo." Hankalin Abu ya tashi, saboda babu abin da yake ɗaga mata hankali irin ta yi ido biyu da ɗansanda. Duk da tana da gaskiya, amma haka gumi ya shiga karyo mata, ta ƙarasa ta ɗauki jaririyar cikin ƙarfin hali da barazana ta ce.
"Au haka ka ce ko? To kafin ka kai mu wurin hukuma, ni da kai na zan fara kai ƙararka. Ka san dai ko lokacin 'yan matancin na kai ne mutumin da nake kulawa. Don haka babu wani uban yarinyar nan, idan ba kai ba. Ai na sha faɗa maka ka daina satar kwana kana kirana turakarka amma sai ka ce ba haka ba. Ka dinga koɗa ni kana ce mini matar so, ni kuma ina jin daɗi domin na ɓa ta ran su Indo nake biye maka. Sai yanzu za ka ce ba ka san zancen ba, za ka yi bayani a gaban ƙuliya." Tana gama faɗar haka ta yi waje fuu! A fusace.
Hansatu ta gyaran É—aurin É—an kwalinta, irin É—aurin ture ka ga tsiya ta ce.
"Kai yau Allah na gode maka da ka nuna mini wannan rana. Ayyiriri! Shagali wan dina. Ai gara da ta tafi da 'yarta don wallahi ba zan riƙe gayyar tsinuwa ba, yarinya an same ta a tsine ta rayu a ciki cikin tsinuwa sannan a ce za a dire mana ita. Haka kawai muna zaune a kawo mana annoba cikin zuri'a ta kwashe mana albarkatun cikin gida."
Daga haka ta wuce cikin ɗakinta, su Indo ma haka. Yaya Inu jiki a sanyaye ya nufi ɗakinsa yana nazarin baƙin cikin da Zainab ta dasa masa. A ɓangare ɗaya yana fargabar abin da zai je ya dawo, saboda shi dai ya san bai taɓa kusantar mace tana jini ba, satar kwana dai kam ya san yana yi babu adadi musamman idan mace ta ɓata masa rai. Don ya rama abin da ta yu masa sai ya kira wata macen da ba girkinta ba, musamman Abu ta kwana a ɗakin. Babban tashin hankalinsa, ya yi mata barazana da hukuma kamar yanda ya san tana tsoron 'yansanda amma ya lura ko a jikinta.
Zaune yake ya yi shiru yana kallon ÆŠan Bishir da jijiyoyin jikinsa suka gama yin laushi, ya ja riga ya share hawayensa. Yana jin ina ma yana da ikon dawo da ciwon shalelensa kansa, da tuni ya dawo da shi.
"Mai gida zaman nan naka fa ba zai kai mu ba, a ce yanzu tun da aka yi wa yaron nan shayi ba za ka fita kasuwa ba. Ita zara fa ba ta barin dami, don Allah ka tashi ga magungunanka can na haɗa maka su." Baba Sale ya ja majina ya ce, "Haka ne Uwale, amma gani nake idan na fita kamar wani abu zai faru da shi. Ban taɓa ganin kaciyar da ta lalace haka ba, ki duba fa ki ga yadda take yin ruwa. Yaron nan duk kuzarinsa ga shi nan ba shi da kataɓus."
Ita kanta Uwale ƙarfin hali take yi, don tana nuna rauninta ta san abin da mijin na ta zai yi sai ya fi haka, don haka ta shanye hawayen idonta ta ce. "Haka ne, amma ko ka zauna ɗin ma abin da Allah Ya ƙaddara shi zai faru. Shi kuma idan mun ga ba ta daina ruwa ba, sai mu sake kiran wanzan mu yi masa bayani. Tun da maganin wurinka ma bai sa ta ƙame ba."
A sanyaye Baba Sale ya miƙe ya shiga ɗaki, ya ɗauko wani ƙaton buhu da ke cike da magunguna. Ya ƙarasa gaban Ɗan Bishir ya ce, "Ɗan Bishiriri ni zan fita nema."
Ɗan Bishiri da ya yi lugub, saboda yadda yake jin jiki ya kalle shi da shanyayyun idanunsa ba tare da ya amsa masa ba. Da ƙyar Baba Sale ya iya ɗaga ƙafarsa ya fita Uwale tana biye da shi. Suna fita Fadil yana fitowa bayan sun gaisa ya wuce ya shiga motarsa da ke gefensu.
"Au Mai gida na manta ba ka bayar da maganin Shamsiyya ba, kada sai ka tafi ta aiko."
Uwale ta furta.
Buhun ya buɗe ya ɗebo wasu matsakaitan magunguna a cikin jarkoki guda huɗu, sannan ya ɗauko wata ƙaramar roba mai ɗauke da man shafawa na magani ya miƙa mata. Ya ɗago jarkokin guda biyu, ya nuna mata wurin da aka yi bayanin maganin a jikin takardar.
"Wannan ki ce mata sai ta ci abinci za ta sha, maganin sanyin mara ne. Kuma sau biyu ake sha safe da yamma, duk lokacin da za ta sha murfi biyu za ta sha saboda yana da ƙarfi sosai."
Ya sake É—auko ragowar roba biyun da yake ba iri É—aya da waÉ—ancan ba ne ya ce.
"Wannan kuma idan ta tashi biyu za ta raba shi, ta sha rabin roba yau gobe ta sha rabi. Shi kuma wannan man zafi ne, na ciwon bayan da ta ce tana yi ne. Za ta dinga shafa shi a bayanta safe, rana da dare. Amfaninsa iya baya ne. Kar ta ji ƙafa ko gwiwa tana yi mata ciwo ta shafa, ba zai yi mata aiki ba. Duka dai bayanan maganin suna jiki, na san kin fahimta abin da ba ta gane ba sai a bari na dawo, saboda ba na son na ba wa mutum magani ya sha ba daidai ba a samu matsala."
Duk bayanin da Baba Sale yake yi Fadil yana cikin mota yana jin sa, ba ƙaramin birge shi ya yi ba. Don haka ya fito ya ƙarasa wurinsa cike murmushi ya ce.
"Am Baba Sale na ji duk bayanin da kake yi mata, kuma AlhamduLillah ka birge ni matuƙa. Saboda yadda na ji kana bayanin magungunanka daki-daki cikin ƙa'ida, ta yanda ba zai haifar wa mutane matsala ba."
A sheƙe Baba Sale ya dubi Fadil ya ce.
"Kai yaro da me ka ɗauki masu magungunan gargajiya? Jahilai ka ɗauke mu ko yaya? Ka ɗebo tsila-tsilan ƙafafuwanka kamar ƙwailayen lawashi za ka yi mini iyayi."
Kunnuwansa Fadil ya riƙe ya ce, "Allah Ya huci zuciyarka ba haka nake nufi ba, ka yi abin da ya dace ne shi ya sa na yabe ka. Saɓanin wasu masu magungunan da suke sayar da magani babu dosage, mutum ya sha yadda ransa ya so babu ƙa'ida." Baba Sale ya taɓe baki ya ce, "Da ka ɗauka maganin asibiti ne kaɗai yake da galihu? Masu magungunan ai wasu suna suka tara, kamar yadda a cikin likitocin akwai muna likita. Kai dube ni nan. Sana'ata ba irin ta sauran masu magani ba ce. A yanzu ma idan na samun jari, babban wuri zan buɗe na huta da gararanba a titi. Sai na sake inganta su, don ina da burin har jami'an lafiya zan zuba tun da ni dai ka san summun bukumin ne, zo na kashe ka da turanci ban sani ba ballantana na san harkar gwaje-gwaje."
Fadil ya saki murmushi, ya yaba masa sosai da sabon tsarin inganta maganin da ya É—auko, har zai tafi ya waigo ya ce.
"Na ji Daddy ya ce an yi wa yaron nan shayi ya jikinsa?"
Jin tambayar Fadil ta sa hawaye ya zubo masa, ya saka hannun rigarsa ya share. Mamaki ne ya kama Fadil yana shirin magana Baba Sale ya ce.
"Ɗan Bishir dai ga shi can rai a hannun Allah, daga kaciya jikin yaro sai fitar da ruwa yake duk ya jagalgale abin ba kyan gani. Na saka masa magani a banza, haka wanzan da ya yi masa kaciyar ya aiko masa da magani amma sai ta fara kamewa sai ta koma 'yar gidan jiya." Ya ƙarasa maganar yana fashewa da kuka.
"Subhanalla, kuma ka kai shi asibiti?"
Kamar Baba Sale yana jira ya ce, "Kaciyar zan kai asibiti don lalacewa? Wai me ya sa a kullum, sai ka nemi wulaƙanta mana sana'ar wanzanci ne?"
Fadil ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Ni fa ba da wata manufa na faÉ—a ba, yanzu mu je na ga yanayin jikin na sa."
Babu musu Baba Sale ya yi gaba Uwale da Fadil suna biye da shi. Suna zuwa suka samu Ɗan Bishir a yashe a ƙasa, kudaje sun yi yamama a kan jikinsa. Da sauri Fadil ya ƙarasa ya fara karkaɗe masa, ya ɗago a ɗan zafafe ya ce.
"Garin yaya kuka bari jikin yaron nan ya yi haka? Saboda Allah dubi yadda ƙudaje suka bin sa ko su ba su isa su saka masa wata cuta a jiki ba."
Mai shirin kuka ne aka jefe shi da kashin awaki, jin kalaman Fadil ya sa Baba Sale ya saki wani wawan kuka har sa da ya tsorata Uwale da Fadil. Ya riƙo hannun Fadil jikinsa yana rawa ya ce. "Boka wallahi ban san yadda aka yi ba, don Allah yanzu mene ne abin yi?"
Jim Fadil ya yi sannan ya ce, "Mafita kawai a ɗauke shi zuwa asibiti shi ya fi fa'ida. Don haka a yanzu muke bayar da shawara idan za a yi kaciya a san wuraren da ya dace a kai yara, ba zan kushe ta wanzamai ba. Domin tun daga shekarun baya zuwa kusan ɗan shekara ashirin da yake a yanzu, kusan yawancin duka kaciyar gida aka yi musu. Amma a inda gizo yake saƙar, rashin kula da tsaftace kayan aikin yin ta zuwa kula da ita bayan an yi wa yara, sune manyan ƙalubalen."
"Wai boka da kake ta ƙafafa a kan shayin, asibiti shin tana da bambamci da ta gida ne? Duk dai ba abu ɗaya ake yi ba?"
Uwale ta tambaya, don ta fara jin haushin yadda Fadil yake fifita aikinsa a kan sana'ar mijinta.