Sashe 49
Dahuwar Kaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A wurin Maman Nana ta durƙushe tana kuka kamar ranta zai fita, sai da ta yi mai isarta sannan ta sauya kaya. Ta ɗauki Abdul da yake bacci ta goya shi ta fito daga gidan, duk wanda ya ganta kallo ɗaya zai yi mata ya fahimci ba ta cikin nutsuwarta. Gidan Maimuna ta shiga ta same ta zaune a falo, Maimuna tana jin shigarta ta saki murmushin ƙeta saboda duk abin da suka yi a kan kunnenta, tunda wayar ba mutuwa ta yi ba a lokacin da ta yi wurgi da wayar Jafar. Amma a fili tana ganin Maman Nana ta dafe ƙirji ta ce, "Lafiya kuwa Maman Nana? Me ya samu fuskarki ta kumbure haka?" Da yake har lokacin da ɗacin abin a ranta, sai Maman Nana ta rushe da kuka mai cin zuciya.
'Na rantse da Allah kuka ma yanzu kika fara, mu je zuwa wai mahaukaci ya hau kura." Maimuna ta faÉ—a a ranta, amma a fili cikin ruÉ—ewa ta ce.
"Maman Nana ki yi magana don Allah, kin É—aga mini hankali. Daga gida ne aka kira ki wani abu ya faru, ko Abban Nana ne?"
Maman Nana ta girgiza kai, Sai Maimuna ta sauke ajiyar zuciya ta ce.
"To mene ne? Don Allah ki yi mini magana, wannan kukan da gani dai ba na lafiya ba ne."
"Wai yau ni Jafar ya mara saboda wata maman Asiya, Jafar ya zama wani iri wallahi asiri aka yi masa, don Jafar É—ina ba ya cikin hayyacinsa."
Maman Nana ta yi maganar cikin kuka.
"Innalillahi wa inna'ilahir raji'un! Kada ki ce mini tun yarinyar da muka yi magana da ke kwanaki? Ai kin ga sakacinki Maman Nana, tun wancan karon na ce ki ɗauki mataki amma kika tsaya sanya. Yanzu ai ga shi kina gani ƙarfi da yaji yarinya ƙarama ta shanye shi."
Cikin ƙaguwa da neman mafita ta ce, "Yanzu mene ne abin yi Maman Asiya?"
Shiru Maimuna ta yi kamar mai yin nazari, sai ta É—ago da sauri ta ce.
"Gidanku sun san abin da ya faru?" Girgiza kai Maman Nana ta yi, sai Maimuna ta ce.
"Yanzu abin da za ki yi kai tsaye ki wuce gida, ki sanar da iyayenki a san halin da ake ciki. Saboda wallahi matuƙar ba a ɗauki mataki ba abin ƙara gaba zai yi, kin san aka ce idan namiji ya ji daɗin dukanka ya samu wuri kenan. Kar ma ki faɗa masa za ki tafi, ki bari sai dai ya dawo kawai ya ga ba kya nan. Idan aka yi muku sulhu daga baya sai ku daidaita ki dawo, amma ina mai tabbatar miki da sai kin tashi tsaye." Shawarar Maimuna ba ƙaramin kwanciya ta yi a zuciyar Maman Nana ba, haka ta dinga ba ta shawarwari daga ƙarshe suka yi sallama ta fita. Da yake makarantar su Nana a bakin titi take, sai ta da ɗebi kayansu sannan ta wuce ta makarantar ta ɗauke su suka wuce gidansu da ke unguwa uku.
Tun bayan da Maman Nana ta yi wa Maimuna sallama da ta ji fitarta daga gida, ta kira Jafar ta kwashe ƙarya da makirci ta faɗa masa. Don har cewa ta yi Maman Nana tana ta zaginsa kuma ta ce ta tafi gidansu kenan, domin ta gama zaman aure da shi. Maganar da ta fi tsaye masa a rai da Maimuna ta ce wai Maman Nana tana kuka tana cewa, ta yi dana sanin haɗa zuri'a da shi, domin shi ba miji kuma uba nagari ba ne. Da irin waɗannan miyagun huɗubar, Maimuna ta samu yin galaba a kan Jafar. Har shi ma ya hau dokin zuciya da cewar ba zai taɓa nemanta ba, kuma ba zai je biko ba tun da ba shi ya ce ta tafi ba. Ya kuma ci alwashin ko a ranar ta nemi takardar saki, a shirye yake da ya miƙa mata kayarta. A ranar tun yamma ya dawo gida saboda ya san Maman Nana ba ta nan, kuma har cikin zuciyarsa da zai samu yadda yake so kuma da babu 'yan gulma tsaf zai ce Maimuna ta zagayo su sha soyayya. Amma da yake ya san akwai matan maƙota da suke kai kawo, sai ya haƙura da buƙatarsa. Ya shiga ɗaki ya rage kayan jikinsa sannan ya jira Maimuna a waya, ya ce ta kunna data za su yi magana. Ita ma da yake ta gama girki ta kuma sheƙa wankan ƙananan kaya, sai wayar ta shi ta zo mata a daidai. Ta whatsapp ya kira ta video call, ta ɗauka a kunyace tana sunne kai ƙasa.
"Wai wai wai, wannan wankan duk ni aka yi wa? A gaskiya baby za ki hargitsa ni." Sai kuma Jafar ya shagwaɓe murya ya ce, "Don Allah idan babu damuwa ki zagayo mana Moon. Wallahi babu wanda zai gane, domin a cike nake da ƙishirwarki."Maimuna ta yi shiru tana nazari, domin ita kanta wannan lokacin ta jima tana buri da fata.
Tun da dare ya yi bayan ta kwantar da yaran ta yi shiru tana ƙare musu kallo, Na'ima da Fatima ne ta yi musu shimfiɗa daga ƙasan katifa. Hidaya da Humaira kuma ta yi musu shimfiɗa a kan katifa, tana nan zaune Kabir ya shiga ɗakin bakinsa ɗauke da sallama. Amsa masa ta yi ta mayar da kanta gefe, saboda haka kawai haushin Kabir take ji. Shi kansa shiru ya yi ganin yanayin kwanciyar da suka yi, sai kuma jikinsa ya yi sanyi tausayinsu ya kama shi. Kayan abincinsa ta ajiye a gabansa, ba tare da ta ce masa uffan ba. Shi kansa ya fahimci fushi take da shi, sai ya ɗan saki fuska ya ce.
"Haba Fauzina yanzu wannan fuskar da kika haɗe duk saboda za ki zauna da mahaifiyata ne, zaman nan fa ba na dindindin ba ne. Don Allah ki daina ɓata ranki ba na so." Fauziya da dama ciki take da shi ta ce.
"Ni ba ina fushi da zaman da zan yi tare da mahaifiyarka ba ne Abban Na'ima, domin Inna tamkar mahaifiyata haka na ɗauke ta. Kawai yanayin zaman ne bai yi mini ba, dubi a inda yaran nan suka kwanta. A gaskiya sam babu tsari wallahi, don girman Allah ka bari mu koma gidannmu idan ya so ko a hankali sai ka ƙarasa."
Kabir ya ɗan yi jim ya ce, "Ummu banat kin san dai muna da maƙiya, waɗanda suke son ganin cigabanmu, wallahi ba na son na koma a ga gidana ko fulasta babu. Kin san idan aka ce shago ba naka ba ne sai haƙuri, Oga ba wata kyakkaywar sallama yake mana ba. Kin ga Allah Ya taimaki Sani da yake shi kekensa ya kai shagon, shi yake cin gashin kansa. Sai dai ɗan kuɗin da yake bayarwa duk shekara, wanda Oga yake cikawa ya biya kuɗin shago. Ni ma kin ga da ina da keken kaina rufin asirin da zan samu sai ya fi haka."
Shiru Fauziya ta yi, ta kallo keken ɗinkinta da ke waje. Ta tuna ba wani ɗinki take samu ba, mafi yawa sai ɗan gyare-gyare da mata suke kawo mata. A yadda take jinta kamar kwance cikin ƙaya, babban burinta bai wuce ta ga sun tashi daga wannan gidan ba. Don haka ba ta yi dogon tunani da nazari ba ta ce. "Indai hakan zai sa ka yi ka ƙarasa mana, ga kekena nan ka ɗauka Abban Nana. Babban fatana Ubangiji ya rufa mana asiri." Tana gama magana Kabir ya rungumo ta jikinsa, sai ya shiga sakar mata kiss a duk ilahirin jikinta. Cikin wata irin murya ya ce, "I love you my Fauzee."
Fauziya ta saki murmushi ta ce, "I love you too Abi." Gani ta yi Kabir yana yunƙurin wuce gona da iri, don haka ta janye shi daga jikinta ta ce, "Ga abincinka fa." Kafaɗa ya maƙale mata yana bin ta da wani irin kallo ya ce. "Idan da ke abinci da komai ba ne." Tana shirin sake yin magana Kabir ya janyo ta jikinsa, ya shiga yawo da hannuwansa a cikin jikinta.
"Wallahi kunya nake ji, magana ta Allah ba zan iya wani abu a cikin É—akin nan ba. Don gani nake kamar Inna tana jin duk abin da muke yi, tun da kaga É—akinmu a jikin É—akinta yake. Kuma ka dubi kusancin kwaniya da muka yi da yaran nan."
Kabir ya zame hannun rigarta ƙasa, ya ɗora kanta a saman cinyarsa cikin wata irin murya ya ce.
"Babu abin da za ta ji, don haka kada ma ki..."
"Kabiru! Kai Kabiru ashe kana ciki?"
Maganar Inna da bakaɗa labulen ɗakin da ta yi ne ya sa maganar da Kabir yake yi ta maƙale, cikin tsananin jin kunya Fauziya ta tashi tana jan rigarta sama. Inna ta saki baki haɗe da riƙe baki ta ce.
"Dole na ji ku shiru a ɗaki mana, ku dai wallahi an yi jarababbun yara. Don masifa tun a farkon dare? Ko tara fa ba ta yi ba, shi ne za ki saka yaro a ɗaki ki ƙadandane kamar alkaki."
Shi kansa kunya Kabir ya ji, ya É—an sosa kai ya ce.
"Amma Inna ai da kin yi sallama kafin ki shigo."
"Ba zan yi ba, na ce ba zan yi shashashan banza da wofi. Ina ganin jarabar su Sadiya da duk asuba za ka ji su suna karafniya da ruwa kamar kifaye, ashe nasu shafar mai ne tun da ga ku; ku tun garin bai nausa ba. To idan ka gama shinshine-shinshinen sai ka zo ka same ni a ɗaki." Inna ta ƙarasa maganar tana sakin tsaki sannan ta wuce ɗakinta.
Bayin Allah na kusa kammala free pages, masu son littafin za su biya kuÉ—in karatu 500 ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank sai shaidar biya ta wannan lambar 07062062624
Ummou Aslam Bint Adam🌚
07062062624
[19/02, 17:43] Ameera Adam: *NAUSHIN WUTA*
©®AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
GARGAÆŠI: Ban amince a sarrafa mini littafi da kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.
SADAUKARWA
Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da mata da gidan Aljanna Amin.
SHAFI NA SHA ÆŠAYA