← Book details Dahuwar Kaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 81

Sashe 5

Dahuwar Kaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To a gaskiya idan har haka ne sai ka tashi tsaye Hafiz, don ba na son duk wani abu da zai sa a dinga tashin hankali. Haka kuma wannan maganar ba za mu bar ta daga mu sai kai ba, dole ne ka kirawo manyanka a yi magana. Ita ma ya zama wajibi ka tsawatar mata, ka kuma kiyaye haƙoƙinta. Don za ka yi aure ba shi zai sa ka wulaƙanta matarka ba, ko ka dinga cin fuskarta kana cin zarafinta. Ka ji tsoron Allah Hafiz, wallahi idan ka cuci 'yar mutane Allah ba zai bar ka ba." Cikin girmamawa Hafiz ya russuna ya ce.

"In Shaa Allahu Baba."

Miƙewa Baba ya yi ya fita, har Amina za ta fita cikin sauri Hafiz ya ƙarasa ya riƙo ta. Rungumo ta ya yi jikinsa ya haɗa ta da bango ya ce.

"Kina tunanin akwai ranar da zan iya rabuwa da ke ne?"

A ɗan shagwaɓe Amina ta ce, "Na sani tun da tsoron matarka kake ji." Sunkuyawa ya yi ya sakarwa bakinta kiss ya ce, "Haka kike gani Meena, amma babu wani tsoro. Kin san duk macen da za a ƙara wa abokiyar zama dole a lallaɓa ta, musamman Bilkisu da take da kishi." Janye jikinta za ta yi ya sake matse ta ya ce.
"Me ya sa kike guduna ne?"

"To ni kada wani ya ganmu a haka." Ta ba shi amsa a sanyaye, zuba mata ido ya yi yana jin sonta na fisgarsa. Cikin wani irin yanayi ya ce, "Ai ba wamda zai shigo tun da kowa ya san ke matata ce, ba ki ga ma Baba ya ba mu wuri ba."
Zaro ido ta yi tana rufe baki ta ce, "To wallahi ni tafiya zan yi, wato duk kallon haka suke yi mini?"

Gyaɗa mata kai ya yi ya tallafo fuskarsa da hannu biyu ya ce, "Ina ƙaunarki Meena, na yi mamaki da har kika yarda zan iya rabuwa da ke." Tura baki gaba ya ta yi cikin jin nauyinsa, Hafiz lumshe ido ya ce.

"In Shaa Allah nan da sati biyu za a kawo kaya, sai a yi wunin biki a wuce wurin don haƙurina ya fara ƙarewa." Sunkuyar da kai ƙasa ta yi cikin jin kunya, ya sunkuya saitin kunnenta ya yi mata raɗa a kunne. Da sauri ta ɗago tana rufe ido cikin jin kunya ta ce.
"Allah Ya shirye ka, ni wallahi ba haka nake ba. Don Allah babu abin da ya dame ni."

"Ai shi ya sa na ga ba kya hana ni idan ina..."
Da sauri Amina ta saka hannu ta rufe masa baki, sai kuma ta ce.
"Ka zo ka tafi ka bar Madam tun da farar safiya." Cikin kwaikwayon muryarta ya ce.

"To duk ba ita ta ja komai ba."
Dariya Amina ta yi ta ce, "Allah Ya shirya ka Hubby."
Har ƙofar gida Amina ta raka shi tana jin soyayyar Hafiz a cikin ranta. Duk da ta ji zafin abin da Bilkisu ta yi, ta wani ɓangaren tana yi mata uzuri, saboda ba kowacce mace ce take danne zuciyarta ba idan za a yi mata kishiya.

Hafiz yana zuwa gida ya samu Bilkisu tana yi wa yara shirin makaranta, kallo É—aya ta yi masa ta É—auke kanta. Haka shi ma bai kula ta ba ya zauna har yara suka gama cin abinci, ya É—auke su ya kai su makaranta. Lokacin da ya koma tana kwance a kan gado, a gefenta ya zauna ya ce.
"Bilkisu ki tashi za mu yi magana da ke."
Ɗagowa ta yi ta kalle shi a sheƙe ta ce.

"FaÉ—i maganarka ai kunne ne yake ji."

Ajiyar zuciya ya sauke ya ce, "Bilkisu kin san ina sonki ina ƙaunarki, kuma kin san babu macen da zan kawo na bari ta raina ki, ko ta ci mutumcinki. Kin san ba zan ɗauki haka ba, duk abin da kike wa 'yan uwana ina sane, amma duk da haka ban bari ɗaya daga cikin ƙannena sun raina ki..."

"Don Allah idan ba wata magana mai muhimmanci za ka faɗa mini ba ka ƙyale ni." Bilkisu ta faɗa rai a ɓace. Girgiza kai ya yi yana danne ɓacin ransa ya ce.

"Muhimmancinta ne ya sa na same ki da maganar. Bilkisu yanzu ba ki ji kunyar saƙon da kika turawa Amina a matsayin ni ba ne? Ko kin ɗauka aure wasan yara ne da za ki yi wannan shirmen? Don Allah ki kama girmanki Bilkisu, ina respecting ɗinki a wurin Amina. Don haka ita ma ko da wasa, ba ta taɓa kawo maganar wargi a kanki ba, ina girmamaki fiye da yadda kike tsammani. Ki girmama kanki ta yadda ba za ki bada ƙofar da yarinyar nan za ta raina ki ba, ni idan kin yi mini zan iya shanyewa. Amma kin san ba lalle ne ita idan kin yi mata wani abin ta ɗaga miki ƙafa ba..."

"To duk abin da za ka saka ta yi mana, wallahi duk shegiyar da ta kawo mini raini sai na yi mata dakan sakwara." Bilkisu ta faÉ—a tana tashi zaune. A É—an zafafe Hafiz ya ce, "Kada ki sake zagar mini mata."
Bilkisu ji ta yi kamar ya watsa mata ruwan zafi, don haka a zafefe ta ce.

"Na zaga idan ka ga dama ka rama mata, 'yan iskan 'yan mata ba za su nemi mijinsu su aura ba sai mace ta raini mijinta su zo su aure suna tunƙahon mijinsu ne." Jin ba zai iya ɗaukar maganganun da Bilkisu take faɗa ba, ya sa shi ficewa daga ɗakin ya nufi ɗakin yaran ya kwanta a can.

Kamar yadda Hafiz ya faɗa cikin ƙasa da sati biyu ya ƙarasa haɗa duk wani abu da ake buƙata na lefe, juma'a tana zuwa aka kai kaya gidansu Amina. A nan su kuma iyayenta suka tsayar da ranar juma'a mai zuwa, a matsayin ranar da za a yi wuni da kai amarya. Hafiz ya yi ƙoƙari sosai, akwati biyar ya yi mata daidai rufin asirinsa. Ya ba ta kuɗin kamu da gyaran jiki don shi ba shi da ra'ayin zuwa wurin kamu. Haka ita ma Bilkisu akwati guda ya cika mata da kaya, dangin atamfofi da lesuna da kayan shafe-shafe har da kayan bacci. Yaran kuma ya saya musu sababbin ƙananan kaya kala ɗaiɗai da shadda kala bibbiyu.
A cikin satin Hafiz ya sa aka fitar da kujerun Bilkisu aka kai wurin kafinta ya gyara mata su, aka saka sababbin sosuna da sababbin yadi suka dawo kamar sababbi. Sai labulaye da ya saya mata masu yanayi da kujerunta duk don ya faranta mata. Sannan ya ba ta dubu hamsim ya ce ta yi duk wani gyara da za ta yi dangin kitso da ƙunshi. Ana saura kwana biyu Amina za ta tare ya kira masu fenti suka yi wa gidan fenti, sai dai jere ne ya hana 'yan uwan Amina su yi a ranar saboda yana tsoron kada Bilkisu ta aikata abin da za ta kunya shi a wurinsu.

Ranar juma'a tun da sassafe 'yan uwan Amina suka je gidan Hafiz yin jere, kallo ɗaya suka yi wa Bilkisu suka fahimci zai yi wuya a yi zaman lafiya da ita a cikin gida. Don haka suka dinga kaffa-kaffa, gudun kada ta ce sun yi mata wani abin. Saboda sun ji sai faɗa take yi wa yara da habaici, kuma abu kaɗan yaro zai yi mata sai su ji ta rufe shi da duka. Kusan azahar suna ta aiki sai ga Fadila ƙanwar Hafiz, ta yi sallama cikin gidan hannunta ɗauke da ƙatuwar cooler. A ƙofar ɗakin Amina ta tsaya suka gaisa da masu jere, ta miƙa musu abincin ta yi musu bayanin kanta. Ta sake fita ta shigo da ruwa da manyan lemuka ta ajiye musu, sannan ta nufi ɗakin Bilkisu.

Tun da Fadila ta shigo Bilkisu ta hango ta, ta cikin labule. Ta dubi ƙanwarta Hafsa ta ce.

"Hmmm dangin miji ko baƙaƙen munafukai, dubi Fadila can ki ga. Wai ita aka aiko ta kawo musu abinci, saboda neman wurin zama. Wai yanzu duk yadda nake da su Fadila, haka za su yi mini su koma ɓangaren amarya." Bilkisu ta ƙarasa maganar cikin ƙwafa.
Ajiyar zuciya Hafsa ta sauke ta ce, "To ya za ki yi ai sai haƙuri, kin san mijinki ne fa ɗan'uwansu. Kuma duk abin da yake so shi za su so, tun da ke dai bare ce a cikinsu." Shiru Bilkisu ta yi ta cigaba da girgiza ƙafa, suna nan zaune Fadila ta shiga ɗakin da murmushi bakinta ɗauke ta sallama.

"Ina wuni Aunty Bilkisu." Fadila ta faɗa cikin girmamawa, tun daga ƙasa Bilkisu ta ɗebo Fadila da harara ta watsar a gwasale ta ce.
"Lafiya."

Shiru Fadila ta yi tana tsaye, don ba ta ga fuskar da za ta zauna ba. Bilkisu ta ce, "To ai sai ki koma can tun da wurinsu kika zo."

"A'a abinci ne kawai na kawo musu." Fadila ta faÉ—a a sanyaye. Kamar Bilkisu tana jira ta ce.
"Ai shi ne na ce ki koma can, tun da ni matar yayanki ce waccan É—inma da za ki wurin matarsa ce." Fadila ba ta tanka wa Bilkisu ba ta fice daga É—aki ta yi wa 'yan'uwan Amina sallama ta tafi.

"Haba Aunty Bilkisu, ki dinga rage wani abin mana. Wai ba ki ga yadda Aunty Murja ta yi ba ne, kowacce mace fa tana jin kishi kawai iya taku ne." Hafsa ta furta, don ta lura idon yayarta ba ƙaramin rufewa ya yi ba. Cikin masifa ta ce .
"Ita daban ni daban, malama kema idan ɓata mini rai za ki yi ki fice ki ba ni wuri." Hafsa ta yi shiru tana mamakin zafin ran 'yar uwarta.

Koda 'yan uwan Amina suka gama jere ba duka suka tafi ba, sai aka bar mutum biyu a ɗakin da yayarta da kuma ƙanwar babanta. Suna gani Bilkisu shiga ɗaya-biyu idan ta yi sai ta yi musu habaici, ko ta saki tsaki tana harararsu. Sai da aka idar da sallar Magriba, sannan Hafiz ya aika aka ɗauko Amina zuwa gidansa.

GIDAN ALHAJI UMAR
Chapter 5 · 0% Book details